WANENE IMAM ALI {A.S} ATAKAICE?

HAIYUWAR IMAM ALI (AS) A KA'ABA FALALA CE BABBA.


Zanyi wannan rubutu ne domin taya muminai murnar zagayowar watan haiyuwar Imam Ali (saw) shugaban duk wani mumini kamar yadda Annabi (saw) ya fada a hadisi ingantacce da shedar Malaman SUNNA gashi babu yawa.👇


An haifi Imam a cikin ka'aba inji wasu daga malaman AHLUSSUNNAH!! Babban malamin sunnah mai suna ALHAKIM ANNAISABURIY ya fada a littafinsa na Hadisi mai suna: ﺍﻟﻤﺴﺘﺪﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﻴﻦ : JUZU'I NA UKU SHAFI NA 483 .

YACE :

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﻓﻲ ‏[ ﺍﻟﻤﺴﺘﺪﺭﻙ ‏] : ‏« ﺗﻮﺍﺛﺮﺕ ﺍﻷﺧﺒﺎﺭ ﺃﻥّ ﻓﺎﻃﻤﺔ ﺑﻨﺖ ﺃﺳﺪ ﻭﻟﺪﺕ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻛﺮّﻡ ﺍﻟﻠّﻪ ﻭﺟﻬﻪ ﻓﻲ ﺟﻮﻑ ﺍﻟﻜﻌﺒﺔ .

HAKIMU YACE :,

MAGANGANU SUN TABBATA DA TAWATURANCI DA AMINCI CEWA SAYYIDA FATIMA YAR ASAD TA HAIFI IMAM ALI (AS) ACIKIN DAKIN ALLAH MAI ALFARMA WATO KA'ABA.


Ga kadan daga cikin malaman sunnah da suka tabbatar da haka.

ﺍﻟﻔﺼﻮﻝ ﺍﻟﻤﻬﻤﺔ Na Ibn Sabbaq Almalikiy shafi na 12

ﻛﻔﺎﻳﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺐ Na Allamah kunjiy shafi na 407

ﻣﻨﺎﻗﺐ ﻋﻠﻲ Na Ibn Mugazili Asshafiiy shafi 7

ﺍﺳﺪ ﺍﻟﻐﺎﺑﺔ Na Ibn Aseer Juzu'i na 4 shafi na 31

ﺍﻟﺴﻴﺮﺓ ﺍﻟﺤﻠﺒﻴﺔ juzu'i na 1 shafi na 139

ﻧﺰﻫﺔ ﺍﻟﻤﺠﺎﻟﺲ juzu'i 1 shafi na 204.

Da shaidar litattafan Sunnah da shaidar malaman sunnah an haifi imam Ali (saw) a cikin ka'aba saboda girmamawa da wannan haiyuwa.


Haihuwar Imam Ali (as) a Ka'aba ta alamta Imam Ali (as) ne zai tsarkake Ka'aba daga gumakan da ke cikinta kuma tarihi ya tambatar mana cewa Imam Ali (as) ne ya kawar da dukkan gumakan da ke cikin Ka'aba a ranar Fatahu Makkah.


Imam Ali (as) bawane kuma (khadimi) ne daga cikin bayin Annabi (saw) kuma shine ('Nafsur-Rasul') a ayar Mubahala kenan duk wata falala ta Imam Ali (as) Annabi Muhammad (saw) yana da fiye da ita Matsalar shine wahabiyawa basu san Annabi Muhammad (saw) ba ne shiyasa idan muna fadar falalar Ahlul-bayt (as) sai suga kamar muna fifitasu akan Annabi (saw) Haihuwar Annabi Muhammad (saw) ta zo da nata mu'ujizoji fiye da ta Imam Ali (as) misali tun a ciki Annabi (saw) yake magana Malaiku suna zuwa wajen Nana Amina (as) suna mata bishara da abinda ke cikinta tsagewar katangun Kisara, mutuwar wutar Farisa, kafewar koramar sawata....


Me ya sa duk lokacin da aka ambaci wata falala ta Imam Ali (as) wahabiyawa sai kan yi dukkan kokari sai sun rusa wannan falalar (idan hadisi ne sukan fara cewa bai inganta ba idan an tabbatar masu da inganci sai su yi tawili ko su kawo shubhar da ke nuna kaitsaye Annabi Muhammad (saw) da ya fadi maganar suke tuhuma ko kuma malaman da suka nakalto falalar)? Shin Salafawa ba sun cewa kin Imam Ali (as) alamar munafunci ba ce?

Don Allah! da a ce Khalifa Abubukar, Umar ko Usman (RTA) ne aka tambatar da an haifeshi a cikin Ka'aba zaku iya kawo irin wannan Shubhar? 

To me ya sa sai a kan Imam Ali (as) ne zaku kawo wannan shubhar? Kenan ya tabbata baku son Imam Ali (as)?


Me ya sa Allah ya umarci Annabi Muhammad (saw) da ya fuskanci Ka'aba a Sallah alhali lokacin akwai gumakan a cikin Ka'abar kenan Annabi (saw) da Sahabbai sun yi shekaru masu yawan gaske suna bautar gumaka har zuwa lokacin Fatahu Makkah (lokacin da Imam Ali (as) ya kau da gumakan)?

Tunda wasu daga manyan malaman Ahlus-Sunnah suka tambatar da haihuwar Imam Ali (as) a Ka'aba kuma suka ce riwayar mutawatira ce kenan yanzu manyan malaman Ahlus-Sunnah kuke tuhuma da cin mutuncin Imam Ali (as)? Kuna so kuce ka'aba dama don gumaka aka ginata ne? Anya kuwa kunsan tarihin Ka'aba kuwa? Shin lokacin jahiliyya, Larabawa kacokaf din su bautar gumaka suke? Ashe Malaman tari basu tabbatar mana akwai masu tauhidi a lokacin jahiliyyar ba? Misali: Qassu Al-Ayadi, Warkatu bin Naufal...

Idan ya tabbata Ka'aba ba don gumaka aka ginata ba kuma akwai masu tauhidi tun a lokacin Jahiliyya, to su masu tauhidin a wancan lokacin basa zuwa bautar Allah a Ka'aba ne? Idan suna zuwa to kenan suma gumaka suke bautawa tunda Ka'aba a lokacin ta cika da gumaka? Shin Allah ba da niyyar mutum yake aiki ba? Idan Lalura ta tilastawa mutum tsayawa a gaban gumaka alhali yana da cikakken Ikhlasi sai Allah yayi masa hukuncin mai bautar gumaka?

La'akari da addu'ar da Mahaifiyar Imam Ali (as) ta yi kafin bangon Ka'aban ya tsage ta shiga ciki ta haifi Imam Ali (as) tana tabbatar mana tana kan tauhidi tun kafin zuwan Musulunci ga abinda take cewa

"Ya Ubangiji na! Ni na kasance mai imani da kai da kuma dukkan litattafan da Ka saukar da kuma dukkan Manzannin da Ka aiko kuma na kasance mai gaskata maganarka da kuma maganar kakana (Annabi) Ibrahim al-Khalil (as) wanda ya gina wannan daki naka Ya Allah! Ina rokonKa don Annabawanka Manzanni da kuma Mala'ikunka makusanta da kuma don wannan jinjiri da ke cikin cikina da ka saukaka min haihuwata".

(Kashful Ghummah na al-Arbili, juzu'i na 1, fasali kan Imam Ali (as).


Tabbas haihuwar Imam Ali (as) a Ka'aba babbar falala ce a gareshi Imam Ja’afar Sadiq (as) yana cewa Abbas bin Abdul Mutallib da Yazid bin Ka’anab sun kasance suna zaune a kusa da dakin Ka’aban sai ga Fatima bint Asad bin Hashim ta zo gurin tana dauke da cikin Amirul Muminin (as) na wata tara a ranan kuwa ranar karshe ce na wannan ciki na ta da tazo sai ta tsaya a jikin dakin Ka’aban alhali kuwa tana fama da nakuda ta daga hannunta sama tana addu’a……(tana addu’a). Nan da nan kamar kyaftawa da bismillah wannan labari mai ban mamaki na tsagewar katangan Ka’aba ya yadu ko ina cikin garin Makka Ba da jimawa ba sai ga jama’a ciki har da Abu Talib suka taru a jikin dakin suna kokarin bude shi don mata su shiga su kai taimako ga Fatima bint Asad wajen haihuwa. To amma duk Wannan kokari nasu yaci tura kofar taki buduwa daga nan sai suka san wannan lamari daga wajen Ubangiji ne don haka sai suka saduda suka koma suna masu zuba wa wannan iko na Allah ido.


Su wadannan jama'a a tunaninsu, Fatima bint Asad tana cikin halin wahala ne don kuwa daman nakuda ya gaji hakan don haka ne yasa suka kawo mata dauki to amma ba su san cewa ita ba ta ma san me ke faruwa ba kuma ba ta ma cikin wata damuwa ko kuma jin zafin haihuwar kamar yadda suke tsammani don kuwa a daidai lokacin ma tana cikin nitsuwa da kwanciyar hankali ne ba tare da wata damuwa ba don dada fahimtar wannan lamari da kyau bari ma mu ji abin da take fada yayin wannan lokaci na haihuwa cewa take.


"Na zauna a cikin wannan gurin (Ka'aba) sai ga shi na haifi dana Ali (as) ba tare da wata damuwa ko zafi ba………"


Kuma don Allah ya tabbatar mana da matsayi da darajar imam Ali (as) sai yazama har baya haihuwarsa (as) Fatima bint Asad da wannan tsarkakakken da nata sun cigaba da zama cikin dakin har na tsawon kwanaki uku alhali kuwa mutane suna nan makil a gurin don ba wa idanuwansa abinci da kuma mamakin wannan babbar karama a rana ta uku kuwa sai ga ta ta fito tare da wannan d'a nata ta hanyar da ta shiga alhali kuwa wannan jariri yana haske fuskarsa tana walkiya kamar farin wata ba wanda ya san Girma da matsayi na Imam Ali (as) sai Allah da Annabi Muhammad (saw) da ya raineshi Allah ya Kara mana qaunar Imam Ali (as) da koyi da shi Allah ya bawa Mal Rinjaye akan maqiyansa albarkar Manzon Allah (saw) Amin.


QARAMIN QARAMIN DALIBIN SHEIKH DR ABDULJABBAR (H) DALIBI HAMZA TIJJANI ABDULLAHI ZANGO. we

Comments