DAGA KOTU.30/9/2021

 

A SHIRYE NAKE NA SAKE SHI YA TAFI IN HAR HUJJAR DA ZASU GABATAR BATA DA KARFI KODA KUWA BAKU NEMA BA.


Hakikar Abunda ya gudana a kotu a yau Alhamis 30/09/2021:


Bayan gabatar da sababbin lauyoyin da suke wakiltar Maulana Amirul wa'izina wanda Barister Umar Muhammad yake jagorantar su Abubuwa kamar haka sun gudana:


1-Barister Umar Muhammad ya nemi belin Malam.


Sai lauyan gwamnati Sa'ida SAN yayi suka akan hakan


Sannan Alqali yace: 


bazan baku belinsa ba a yanzu saboda yayi huri kodan tsare rayuwarsa yadda yake da masoya masu yawa haka yake da magauta masu yawa kuma yana da saɓani dasu yayi gabas sunyi yamma.


Amma idan suka gabatar da shaidun su naga basu da wani karfi zan sake shi ya tafi ko baku nema ba.


2- Lauyan Malam ya nemi a bashi kwafin shari'ar dan yasan daga inda aka fito da kuma inda ake a yanzu.


3-lauyan malam ya fadawa Alqali cewa:


Naji labarin a zaman da ya gabata kace za ka bawa malamin cikakkiyar dama na yazo da dukkan abunda yake so da zai bashi damar kare kansa da kuma  cikakken lokaci na gabatar da bayanan sa, ya me girma me shari'a ina son sanin gaskiyar wannan labari.


Alqali:


Tabbas na faɗi hakan kuma kotu bata baki biyu hasali ba Alfarmace za muyi masa ba dole ne ma muyi masa hakan dan doka ce ta bashi damar amma yanzu ba azo wannan gaɓar ba tukunna idan lokacin yayi zaizo da duk abubuwan da zai bukata dan kare kansa, litattafan sa in sunkai cikin mota yazo dasu zamu bashi dama da isasshen lokaci.


4-Barista Umar ya bukaci lauyoyin gwamnati zama na gaba su fara gabatar da shaidun su dan shari'a ta tura kada a cigaba da É“atawa kotu lokaci.


Inda lauya Sa'ida SAN yace su dama suna zuwa da shaidun su gaban kotu rashin basu damar gabatar dasu shi yasa basu gabatar ba.


Anan Alqali ya amince da suzo su gabatarwa da kotu shaidun nasu a zama na gaba sai dai shaidu 2 kawai yake nema.


Daga nan mai shari'a ya dage Shari'ar zuwa sati biyu masu zuwa ranar 14/10/2021.


Muna Rokon Allah ya kara dora gaskiya a saman karya yayi riko da hannun me shari'ar zuwa ga gudanar da Adalci.

@fatimiyyaalawuyyatv

Comments

Post a Comment