ABINDA YAFARU A KOTU YAU 14/10/2021


 ABINDA YAFARU YAU A KOTU 14/10/2021. KAMAR HAKA.




A safiyar yau Alhamis 14/10/2021 babbar kotun shari'ar Muslunci dake kofar kudu ta cigaba da sauraren Shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara da Gwamnatin Jihar Kano. A zaman da ya gabata, alƙali ya dage shari'ar ne dan fara saurarar shedun masu gabatar da ƙara a kotun.


Sai dai kafin gabatar da shedun, lawyan wanda ake ƙara Barr Umar Ibrahim ya bijirarwa kotu sukar da suka gabatar a baya kan batun bayyanar manyan lawyoyi masu muƙamin SAN a karamar kotu, da kuma batun karanto sabbin tuhumomin da ake wa malamin, lawyan masu gabatar da ƙara Farfesa Mamman Lawan Yusufari SAN ya bayyanawa kotu cewa a shirye suke suyi martani ga wannan sukar, yace babu gaggawar sai sun maida martani a yau, za a iya cigaba da shari'ar, suna rokon a fara gabatar da abinda kotu ta tsara za a gabatar yau na shedu, a zama na gaba zasu yi martani akan sukar.


Mai Shari'a Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya bayyana cewa wajibi ne a gabatar da martani a zama na gaba, sannan kuma ya bada izinin a cigaba da sauraren shedu. Masu gabatar da ƙara sun zo da shedu guda biyu gaban kotu, alƙali yayi umarnin a kai ɗaya shedar ofishin rejistra kafin a kammala da na farko. 


Sheda na farko Mai suna Adamu Adamu makocin masallacin juma'a na Ashabul Kahfi dake Gwale filin mushe ya bayyana wa kotu cewa, a ranar juma'a 10 ga watan Agusta, 2019 ya je masallacin Ashabul Kahfi don sauraren karatu sai yaji Malam Abdujabbar ya furta wadansu munanan kalmomi akan Annabi SAWA, yana mai cewa Malam Abdujabbar yace Muslim ne ya ruwaito a hadisi na 1365 da hadisi na 1428.


Mai gabatar da shedar ya kara da cewa a ranar 20/12/2019 da kuma 25/10/2019 yaji wanda ake ƙara ya kawo hadisin Anas yana mai jingina mummunar magana ga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam, ya ce an ruwaito a littafin Bukhari da Muslim a hadisai masu lamba 5120 da kuma 2324. Shedar yace basu ga wadannan kalmomi na Malamin a cikin littafan ba, ya kudurce cewa kawai Malamin ne ya ƙirƙire su. 


Lawyan wanda ake ƙara ya gabatar da tambayoyin sa ga shedar kan ra'ayinsa akan karatun Malam Abdujabbar, saidai Lawyan masu gabatar da ƙara ya ce basu da hurumin yin tambaya akan ra'ayin wanda yake bada sheda dogaro da sashe na 67 na dokar sheda ta kasa wato "Evidence Act 2011".


Malam Abdujabbar Kabara ya gaya wa kotu cewa tunda batu ake akan karatu a bashi dama ya bijirar da mas'alolin ga shedar ya gani daga littafan magabata har guda 9, ya kuma bayyana cewa Lawyan sa ya kasa fito da su ya bayyana a kotu, yana rokon a bashi damar ya gabatar dasu. Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya ja hankalin Malamin da cewa, dama 2 yake da ita a kotu, shine ya amsa zai tsayawa kan sa ko kuma lawyoyi su tsaya masa, amma doka bata bada dama gareshi yayi magana ba a lokacin da lawyan sa yake magana, saidai ko shi yayi lawyoyi su janye daga Shari'ar, ko kuma Lawyoyi suyi shi kuma yayi shiru. 


Daga ƙarshe kotu ta Sallami shedar bayan ya amsa tambayoyi da dama daga lawyoyin masu gabatar da kara, Lawyan wanda ake ƙara da kuma Alƙali,sannan K

alƙalin kotun yace kotun zata bayyana hukuncin ta akan wannan sheda a hukuncin ta karshe da zaiyi akan shari'ar.


Alƙali ya dage shari'ar zuwa 28/10/2021 dan saurarar sheda na biyu a gaban kotu. 


©Fatimiyya Alawuyya Tv

14/10/2021

Comments

Post a Comment