Yanzu nake ganin videos na daliban Malam Abduljabbar da suka yi zagayen Takutaha.
Daga wani bawan Allah.
"Ganin yadda suke fita nuna murnar takutaha da hotunan malam Abduljabbar ya tabbatar min da abunda na dade ina fadawa mutane daidaiku a cikin hira.
"Na sha fada cewa sunan Abduljabbar kara daukaka yayi ba kaskanta ba. Sannan dukkan masu rigima da shi daga na gida da na waje kaskanta suka yi sannan sunansa zai dawwama kamar yadda nasu zai gushe nan da ba da jimawa ba.
"Abunda ya sa na sha fadawa mutane wannan maganar shi ne yadda tarihi ya mu'amalanci irin wannan waki'oin. Ba wannan ne farau ba shi yasa ko sanda abubuwan suka rika faruwa ban ga wani sabon abu ba.
In muka kalli abun ta kowane bangare zai tabbatar da maganata. In dai ka karanta tarihi da yadda aka rika amfani da gwamnati don samun cin nasara a wata manufa ta siyasar addini, zaku yadda dani. Zan dan bamu misali kadan.
"Alhallaj sanannen Sufi ne a wajen mu gaba daya. Sufaye suna kafa hujja da maganganunsa da yadda yayi fana'i a kaunar Ubangiji.
" Tun kafin zuwan Hallaj akwai sufaye amma basa bayyana sirrin su a fili. Duk wani Sufi ya san "Fana'i" da "Baqa'i". Shi Hallaj a "baqa'i" ya zarce. Baqa'i shi ne matakin da Sufi yake kaiwa ya daina ganin da jin komai sai ubangiji. Alhallaj ya kai wannan mataki. Lokacin da Hallaj ya fito ya bayyana sirrin sufanci a zahiri, don a lokacin boyewa ake ba'a bayyanawa, kama shi aka yi.
Hallaj sai da yayi shekara sha daya a kulle a prison. A karshe kuma aka kashe shi. Mutane iri biyu suka rabu akan Hallaj. Akwai masu yi masa kallon mushriki don shi ne dalilin da yasa aka kashe shi da kuma masu yi masa kallon wanda ya kure a sanin Allah da jin dadin kusanci ga Allah. Haka ma Malam Abduljabbar, yana da masu masa tsananin kauna da kuma masu yi masa tsananin kiyayya. Amma a yau wa muke ambata? Hallaj ko wadanda suka kashe shi? Har yau Hallaj aka sani baa san sauran ba. Hallaj ya dauki 'risk' ne na bayyanawa duniya mene sufanci da ma'anar "Baqa'i". Shi yasa duk Wanda zai kafa abu sai ya sha wahala a karshe kuma shi zai nasara.
Kamar yadda na fada, ta kowane bangare haka lamarin yake. Imam Malik haka ya sha wahala a hannun Harun Rashid, sarki a daular Banul Abbas. Saboda kawai yayi fatawa da ta sabawa Sarkin ya sa aka kama shi aka yi masa dukan tsiya.
Imam Hambali ma haka ya sha wahala a hannun sarakunan Banul Abbas. Sai da ya shekara biyu a kulle a prison. Wasu sun ce an fito dashi an masa duka shi ma.
A tarihin duk wani malami sananne da yau ake ambatar sunansa ana neman albarkarsa ban san mutum daya wanda bai sha wahala da gwamnati ba. Kuma abunda suke kasa gamewa shi ne, a karshe sunan wanda suka tararwa din suke dagawa kamar yadda aka yiwa Hallaj da Imam Malik. Har wahabiyawan ma, Ibn Taimiyya ya shiga kurkuku. Wasu ma sun ce a kurkuku ya mutu. Idan da kulle Ibn Taimiyya ya magance matsalar da ya haifar da yau ko sunansa muna ji?
Hanya daya ce ta warware irin wannan matsalolin. A samar da dialogue mai cikakken yanci sannan a bawa kowanne damar magana su kuma mutane su rika alkalanci tsakaninsu. Da kadan da kadan har a warware duk wata matsala. Hana magana, amfani da gwamnati da karfin hukuma baya kashe da'awa.
Ina yiwa daliban Malam Abduljabbar ban gajiya. Sannan sun tabbatar min da maganata kamar yadda na fada a baya, na cewa Malam Abduljabbar ya riga ya dora tafiya sauran aikin na masu isarwa ne.
Ku ne masu isarwar kuwa. Ya gama aikin ya nuna hanyar, ku rika kokarin haskawa duniya hasken da kadan kadan kowa zai gane InshaAllah. Allah karawa malam Abduljabbar juriya alfarmar sayyidah Zahrah Alaihassalatu wassalam.
©Fatimiyya Alawuyya Tv
Comments
Post a Comment