AN KUSA RABA WASU YANDARIKU DA ANNABI SAW


 DA IMAM HUSAIN DA IMAM ALI AS, 


DA KUMA


SIDI ABDULQADEER JILANI DA SIDI AHMAD TIJJANI RA. 


SUWA SUKA FI WASU DARAJA HAR A WURIN ALLAH? 


Dalilin yin wannan tambayar shine:-

 

Ziyarar da Mawakin Manxon Allah SAWW ya kaiwa Imam Ali as da Dansa Imam Husaini as a Iraq Naga ta tayar da Kura. 


Daga cikin Abinda ake xarginsa dashi shine, 

Wai ya zama Danshi'a, Har shima ya tsaya yana kare kansa saboda Hujumi yayi masa yawa. 


Tambaya:-

Ashe yanxu a duniyar Musulmi Babu mai Kaunar Imam Ali da Dansa Imam Husaini as Sai Danshi'a? 


Haka ma babu mai ziyartarsu sai Danshi'a? 


Shin akwai wani Mai da'awar shi dan Sunne ne ko Dariqa da In Aka bashi Zabi akace ka zabi daya  Ko a Kashe shi, 

Tskanin Imam Ali da Dansa Imam Husain as


Ko ya Zabi Sidi Abdulqadir Da sidi Ahmad Tijjani RA

Har ya kasa gane wanne xai zaba yabar wani? 


Tabbas yan Dariqa Wahabiyawa Sunyi Galaba a kanku kuma sun rabaku da Manzon Allah da Shehunan da Kuke Kallo a abin koyi. 


Duk wata Falala ta Wadancan Shehunan guda biyu in ka Hadeta bata kai Matsayin Majanyin Dokin Imam Husaini as ba Balle wani Sashe na Jikinsa. 


Duk wata Falala da suke takama da Ita bata wuce kace Musu su Yayan Imam Hasan da Husaini ba, Jikokin Fatima da Ali as. 


Idan kana so kayi Musu zagin kare dangi to kace su Basu da Tsatso da Imam Husaini as. 


Da zaka goge duk wata Falala tasu amma Kamayar musu Falala daya ta kasancewarsu yayan Jikokin Ali da Fatima as To har yanzu baka ci Mutuncinsu ba. 


Haka da zaka jingina Musu ko wace Irin falala amma kace su Ba jikokin Imam Ali as bane to ka gama ci musu mutunci. 


Basu da wata daraja ko wani Haske wanda ya wuce kasancewarsu  Jikokin wadannan da kuke ki da Hafiz Abdallah ya ziyarcesu a Karbala da Najaf. 


Yandariqa Kubi a  Hankali kada wahabiyawa su rabaku da Imaninku. 


Kasar Kabarin Imam Husain as tafi dukkan Shehunan Dariqa girman daraja. 

Ku kiyaye wannan.

©Fatimiyya Alawuyya Tv

Comments