Alkalin Isra’ila ya tabbatar da haramtawa Yahudawa yin ibadah a harabar Masallacin Kudus
Ba karamar nasara bane Ga al'ummar musulmin duniya gaba daya.
Wannan hukuncin yabuyo bayan hukuncinda wata kotu karama tayi abaya.
Kamar yadda jaridar bbc ta rawaito, Ga cikekken labarin akasa kamar haka.
Wani alƙalin birnin Kudus ya tabbatar da dokar ƴan sanda da ta haramta wa wani Bayahude da aka gani yana ibadah a harabar Masallacin al-Aqsa, inda ya yi watsi da hukuncin wata ƙaramar kotu da ta goyi bayan Bayahuden wanda wasu ke ganin zai haifar da tashin hankali.
Jaridar The Times ta Isra’ila da ta ruwaito labarin ta ce hukuncin kotun na ranar Juma’a na zuwa ne bayan ministan Ć´an sanda Omer Bar-Lev ya É—aukaka Ć™ara a ranar Talata da ta gabata inda ya yi gargaÉ—in cewa hukuncin Ć™aramar kotun zai iya haifar da wani mummunan tashin hankali.
A hukuncin da ya yanke, alƙalin kotun Aryeh Romanov ya tabbatar da haramtawa Yahudawa yin ibadah a harabar da aka amincewa musulmi su yi ibadah.
Comments
Post a Comment