kamar haka.
"Babban abinda yake kan duk daliban Malam a faɗin duniya a yanzu shine su duƙufa wajen yi masa addu'a da rokon Allah ya cigaba da bashi kariya, lafiya da kuma sabaati. Cece kuce da rarume rarumen cewa wane kaza ko wance kaza a wannan gaɓar rashin adalci ne wa kanmu musamman a wannan lokacin da muka fi buƙatar haɗin kai da kuma magana da murya guda"
Yakuma cigaba dacewa.
"Lamarin Shari'a abu ne mai sarƙaƙiya wanda kana zaune a gida da waya a hannun ka baza ka iya hasaso aƙibar ta ba, kuma al'amari ne wanda idan baka da sani ko kwarewa akan sa, zaka yi ta zubar da kimar ka ne idan ka yi ta magantuwa akai, ka yi magana akan fannin ka, ka bar ma'abota wani fannin suyi tsokaci akan abinda suke da kwarewa akai"
Dalibin sheikh abduljabbar yacigabada cewa.
"Tsokaci kan yadda Shari'a ta wakana daga ''Leyman'' ƙara jagula abubuwa yake, abu ne da yake da bukatar a zauna collectively a duba kafin a kai ga wata matsaya. Shiyasa ban kai ga cewa komai akan Shari'ar nan ba sai da na tabbatar na nazarce ta tare da waɗanda suke da kwarewa a fannin, na kuma fadi abinda na yi nazari akai duk da cewa na sha martani har daga waɗanda ya wajaba suce sun gode.
Yanzu kawai dan kana direban mota ƙarama sai kace a baka jirgi zaka tuƙa, ko kuma ɗan kana likita sai kace a baka generator za ka gyara? kowa da muhallin da yake da kwarewa akai, ya kamata a dinga ƙaddara kowa da fikirar sa. Allah SWT cewa yayi ''Fas'alu ahlazzikiri inkuntum laa ta'alamun".
A ɗaiɗaikun ku ko a cikin taro, ya kamata ku ƙara azama sosai da ƙara ƙaimi cikin addu'o'in ku ga Malam, maganganu da yarfe, taɓa juna da kuma sukar Shaksiyyar juna ba abinda zai amfane mu dashi a halin da muke ciki yanzu, ya kamata mu dubi irin ƙarfin da magautan mu duke dashi, mu kara ƙarfafa alaƙar mu da Allah mu kuma nemi ɗaukin sa.
Shawara ce ga zuciyar da ke budaddiya da kyakkyawan hange.
©Fatimiyya Alawuyya tv
Comments
Post a Comment