Shin maulidin Annabi saw bid'ah ne?
MAULIDI IBADAH NE DA NASSIN AYOYIN QUR'ANI DA INGANTATTU HADISAI:
BIDI'ANTAR DA MAULIDI SABODA SAHABBAI BASU YI BA; TSINTSAR JAHILTAR HUKUNCE-HUKUNCEN SHARIA NE, DON BABU WATA AYAR QUR'ANI KO INGANTACCEN HADISI DA YA CE; SAI SAHABBAI SUN AIKATA WANI AIKI; SANNAN AIKIN YA SAMU GURBI A MUSULUNCI. HASALIMA AIKIN SAHABBAI BAI CIKIN MASDARORIN SHARIA (SOURCES OF SHARI'A). QUR'ANI DA INGANTATTUN HADISAI NE MASDARORIN SHARIA:
Ibn Taimiyya ya na cewa:
"Ibadah ta kunshi dukkan wani abu da Allah ya ke so a aikata ko a fada" (Duk wani abu da mutum zai aikata; Ibadah ce, mutukar babu nassin akan haramcin sa ko karhancin sa. Haka zalika nisantar haramci da karhanci Ibadah ne. Kadan daga cikin misalan Ibadah shine) son Allah da Annabi(saw)...:
يقول ابن تيمية في رسالته "العبودية": "العبادة هي اسم جامع لكل ما يحبه الله ويرضاه من الأقوال والأعمال... حب الله ورسوله... (رسالة العبودية لابن تيمية، ص 38).
Ibadah ita ce dukkan wani aiki mai kyau da Allah ya ke so, kuma babu inda Allah ya haramta shi. Ibadah ta kunshi raya alamomin (sha'a'ir na) Addini:
العبادة: تشمل كل الأعمال الصالحة التي يحبها الله وترضيه. العِبَادَةُ: الشعائر الدينيَّةُ. (معجم الوسيط). العِبَادَةُ: إقامة الشعائر الدينية. (معجم الرائد).
Atakaice, idan an ce Ibadah ba kawai ana nufin Wajibi ba. Hukunce-hukuncen Ibadah sun kunshi: Wajibi, Mustahabbi, Halal, Haram da Makaruhi.
Allah(swt) ya na cewa:
قُلۡ بِفَضۡلِ ٱللَّهِ وَبِرَحۡمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلۡيَفۡرَحُواْ هُوَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ. (ﻳﻮﻧﺲ : 58).
"Ka ce, saboda falalar Allah(swt) da rahamarsa; su yi farin-ciki (murna), irin wannan (taron na murna akan falalar Allah da rahamasa) ya fi ko wane taro alkhairi".
A wannan ayar, Allah(swt) ya na umartar mu da yin farin-ciki da murna akan falalarsa da rahamarsa.
Akwai wata rahamar Allah da takai Annabi Muhammad(saw)???
Allah(swt) ya tabbatar mana da cewa; Annabi Muhammad(saw) rahama ne ga dukkan Talikai (duk wani abinda ba Allah(swt):
ﻭﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﻨﺎﻙ ﺇﻻ ﺭﺣﻤﺔ ﻟﻠﻌﺎﻟﻤﻴﻦ. (ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ : 107)
©Fatimiyy Alawuyya TV
Comments
Post a Comment