TAMBA YOYIN DA LAUYAN MALAM ABDULJABBAR WA SHAIDAR FARKO


TAMBAYO YIN GASU KAMAR HAKA!



KAMAR YANDA SHAFIN MUJAMMA'U ASHABUL KAHFI SUKA WALLAFA A SHAFINSU NA FACEBOOK.

TAMBAYOYIN LAUYOYIN SHEIKH DR SHEIKH ABDULJABBAR KABARA GA SHAIDAR YAN MAJA NA FARKO.

Bayan lauyan gwamnati ya gabatar da shaidarsu na farko kuma yayi masa tambayoyi a gaban Alkali, sannan ya amsa amatsayin shaida.

Kamar yanda shafin mujamma'u ashabulkahfi suka wallafa.
Sukacigaba da cewa.

Alkali ya ja hankalin sheda na farko kan kada ya kosa da tambayoyin da Lauyan Sheik Abduljabbar (H) zai yi masa.

Sannan, Alkali ya juya bangaran lauyoyin malam da tambaya kamar haka: "shin kun yarda da shaidar mai gabatar da kara?

Amsa: "Ah ah.

Alkali: "tunda baku yarda da shaidar ba, shin Kuna da tambayoyi ne da zaku yiwa shaidar masu gabatar da kara?

Amsar lauyan malam: "muna dasu.

Ya fara da tambaya kamar haka:

1. Lauyan malam: "shekararka nawa?

Shaida: "shekarata 32.

2. Lauyan malam: "Kace kana zaune kusa da masallacin malam?

Shaida: "Eh haka ne.

3. Lauyan Malam: "idan nayi daidai gidanka yana kusa da wajan da malam yake karatu? 

Shaida: "Eh, amma shekarar data gabata na koma Kuntau, amma gidan iyaye na a nan yake.

4. Lauyan malam: "Shin shekararka nawa kana karatun addini?

Shaida: "tun daga tasowata har izuwa yanzu.

5. Lauyan malam: "Shin nisan karatunka na addini zuwa inane?

Shaida: "Na haddace Al-qur'ani, na karanta litattafan hadisi a kalla 20, fiqhu 10 da tauhidi a kalla 10.

6. Lauyan malam: "Hadisin daka fada mai lamba 1360 da 1428, shin ka sauraresu a bakin Malam daga farko har karshe, ko kuwa iya inda ya fadi kalmomin nan ka saurara?

Shaida: "Naji daga farko har karshe.

7. Lauyan Malam: "Shin ko kasan mai malamin yake nufi da kalmomin daya fada?

8. Shaida: "Nufinsa a cikin zuciyarsa saishi sai Allah, kuma idan ba haka yake nufi ba mai yasa ya fadi kalmar.

8. Lauyan Malam: "Su wadannan bayanai daya ke fada ko kasan yana cewa wasune suka rawaito?

Shaida: "Eh, amma an duba babu.

9. Lauyan Malam: "kana nufin yayiwa Bukhari da Muslim kage kenan?

Shaida: "Eh, Bukhari da Muslim da Manzon Allah SAW.

10. Lauyan Malma: "Ko kasan Allah SWT. da Manzon Allah SAW.  kawai ne ba'a mayar musu da martani?

Shaida: "Eh, nasan haka.

11. Lauyan Malam: "Su wadannan hadisai da kake fada, wasune suke fada ba malam ba, shi kawai yana karantawa ne?

Shaida: "An duba babu.

12. Lauyan Malam: "Shin a wadanda suke kara da har kake bada shaida, akwai wakilin Bukhari ko Muslim?

Shaida: "Babu, amma wakilan musulinci ne.

13. Lawan Malam: "Shin a saninka hadisai ana musu sharhi da fassara?

Shaida: "Eh, ana musu amma ba wanda yake irin ta malam, a cewar shaida farko.

14. Lauyan Malam: "Shin ana samu a malamai yadda wani zai fassara da ban da yadda wani zaiyi?

Shaida: "Eh, ana samun haka.

15. Lauyan Malam: "Shin kai malami ne?

Shaida: "Ah, ah, ni ba malami bane.

16. Lauyan Malam: "Tunda kace malamai kowanne yana iya yin nasa fassarar, shin fassarar da malam yayi baiyi daidai ba kenan a tunaninka?

Shaida: "Ba fassara yayi ba, kuma ba sharhi yayi ba.

17. Lauyan Malam: "Shin fassarar malamai ba tana sabawa da juna ba, kuma kowa yakan tsaya ne a kan fahimtarsa ba?

Shaida: "Zamanin magabata haka ne, amma banda yanzu.

18. Lauyan Malam: "Shin ba ana samun sabani a tsakanin malamai ba, kuma kowa ya tsaya a kan fahimtarsa ba?

Shaida: "Eh, amma a da kenan, banda yanzu.

19. Lauyan Malma: "Idan na fahimce ka yanzu ba a bincike kenan?

Shaida: "Ana bincike amma ta hanyar bin Sharhin magabata.

20. Lauyan Malam: "Misali, shin idan kayi bincike ka fahimci wani abu daban wasu mutanan kuma sukaki yarda, shin wannan binciken da kayi zai zama laifi?

Shaida: "Ah, ah, bazai zama laifi ba.

21. Lauyan Malam: "Misali, shin idan malam yayi bincike ya gano wani abu daya saba da ra'ayin wani, wannan binciken zai zama laifi kenan?

Shaida: "Bani da amsar wannan tambayar tunda ba dani kayi misali ba.

Lauyan wanda ake kara: "Kace baka da amsar wannan tambayar akan malam, amma da akayi misalin akanka, ka bada amsa.

Abinka da mara gaskiya jikin sa sai karkarwa yake gaba daya ya futa hayyacin sa, a nan ne lauyoyin gwamnati sukayi suka a kan yadda lauyan malam wanda  yake tambayar shaidar da suka gabatar....

ZAMU CIGABA INSHA ALLAH.......

A KASANCE DAMU.

            #MAKWN
   14/10/2021
Iya abinda suka wallafa kenan.taredacewar zasucigaba.Fatanmu Allah yabayyana gaskiya.gaskiya kuma tayi halinta.amin
©Fatimiyya Alawuyya tv

Comments

Post a Comment