YANDA TAWAKANA A KOTU 11/11/2021

 SHEIK ABDULJABBAR YA GAJIYAR DA LAWOYIN GWANATI SUNKASA SUKARSHI AKAN TAMBAYOYI GOMA SHA UKU DA YAYIWA SHEDAR DA GWANATI TAKAWO 

Bayan Tattaunawa Tsakanin Lauyoyin Gwamnati da na Sheik Abduljabbar akan Tuhumar tsayawar Layoyi Masu Matsyin Senior Advocate of Nigeria (SAN)

Alqali Sarki yola ya tambayi Lauyoyin Malam Abduljabbar ko kuna da qorafi Akan haka Lauyoyin Malam Abduljabbar Sukace Sunbarwa Alqali ya Fadi Ra'ayinsa 

Alqali ya bari Sai Ahukuncin Qarshe Zai Fadi Ra'ayinsa 

Domin haka kotu ta koma kan lauyoyin Malam Abduljabbar ta tambayesu cewa a sharia da ta gabata kun roki cewar wanda ake kara kuna so abashi dama da kanshi yayi wa shaida tambaya da suka kuma har shima sheikh Abduljabbar ya nemi abashi damar hakan. 

Lauyoyin gwamnati sukace eah a, shine muka tsaya akan kowa yaje yayi nazari akan hakan zuwa yau. 

To gamu mundawo, shin ko kuna nan akan abawa Sheikh Abduljabbar dama yayi bayani da kansa ko kune zakuce wani abu? 

Lauyan Sheik Abduljabbar umar FAROUK yace har yanzu muna rokon kotu ta bada dama Malam Abduljabbar yayi tambaya da suka da kanshi dogaro da section 223ACGL sub section 3 da kuma sub section 4.

Cikin Barkwanci Lauya Umar Farouk yace Ina so kotu ta GARGADI Malam Abduljabbar akan wannan matsayi da ya dauka akan cewar shine zai yi wa shaida tambayoyi idan har ya yarda to mu bazamuyi suka ba ko tambaya ga shaida 

Sakamakon shi Malam Abduljabbar yace akan hadisai ne zaiyi tambaya kuma zaiyi suka. Amma akan sauran maganar sharia mu lauyoyin Malam Abduljabbar zamuyi cigaba da yin shariar Amma bazamuyi suka ko tambaya ba ga shaida sai dai shi Malam Abduljabbar zai yi da kanshi.

Alqali Sarki yola ya cewa lauyoyin Sheikh Abduljabbar, ko ina takardar da kukayi yarjejeniyar da Malam Abduljabbar cewa shine zai kare kanshi kuma shine zaiyi suka da tambaya ga shaida? 

Cikin Fara'a da da Sakin Fuska Lauya FAROUK yace wannan takarda mu kadai ta shafa tsakaninmu da shi amma shi wanda ake kara yanada takardar kotu tana iya nema a hannun shi. 

Nan take Sarki yola ya cewa Malam shin ko kaine zaka kare kanka kuma kayi suka da tambaya da kanka? 

Malam Abduljabbar "eh nine na rubuta da hannuna nace zan kare kaina da kaina. Kuma zanyi suka ko tambaya da kaina. 

Ga ma takardar da muka rubuta a tsakaninmu. 

Na gamsu na yarda ta da san raina nine zan kare kaina a gaban kotu. 

Anan Malam Abduljabbar ya mika takardar a hannun Alqali kuma Alqali yace ayi kwafi a bashi kwafi a mayarwa da Malam Abduljabbar takardar shi.Alakali ya karanta takardar yarjejeniyar agaban kowa, takardar ta kunshi Alkawari- da kariya da suka da Malam Abduljabbar zaiyi, abinda kuma yashafi harkar law su lauyoyinsa ne za suyi magana akan shi.

Kotu ga lauyoyin Malam Abduljabbar- idan na fahimci yarjejeniyar taku duk shaidar da masu gabatar da kara zasu kawo, wato wanda ake kara shine zai yi musu tambayoyi kenan, ba wai shaidar mai kara guda daya ba koh? 

Misali a duk lokacin da aka kawo shaida shi Malam Abduljabbar shine zai yi tambaya da suka koh ba haka bane? 

Lauya FAROUK yayi murmushi yace ina rokon kotu ta tambayi Malam Abduljabbar yayi bayani da kansa. 

Kotu ta tambayi Malam Abduljabbar shin ko kaine zakayi tambayoyi tare da suka ga duk shaidar da aka kawo? 

Amsa daga bakin Sheik Abduljabbar "Eh duk wani shaida da za a kawo nine zanyi masa tambaya kuma nine zanyi masa suka, kuma nine zan kare kaina." 

ALQALI yacewa lauya FAROUK ko kun yarda da abinda Malam Abduljabbar ya fada tunda kun saka hannu akan takardar? 

Lauya FAROUK yace eh mun yarda 

Amma Lauyan Malam Abduljabbar yanemi Alqali Sarki yola ya Gargadi Malam Abduljabbar Akan wai Hadarin Malam Abduljabbar din ya yi Cross Examination da kansa 

Alqli yayi Har Sau uku Amma Malam Abduljabbar yaqi Yarda Lauyoyin su Yu cross Examination Questions din Sai dai Shi yayi da kansa 

Alqali Sarki yola ya cewa lauyoyin Malam Abduljabbar, to kunji fa na gargadeshi amma ya kafe akan abinda shi yafada cewa shine zai kare kanshi. 

Ko me zakuce? 

Lauya FAROUK yace har yanzu fa ni inaso kotu ta sake nusasheda da Malam Abduljabbar kuma ta kara fahimtar dashi akwai hadari fa a wannan matakin da ya dauka amma idan yace a a, to shikenan.Kotu ga Malam Abduljabbar.

Wannan matsayi da ka dauka a matsayinka na wanda ba lauya ba zai iya yuwa akwai hadari a tare dakai na daukar wannan matsayi, domin haka me zai hana ka yarda lauyoyin suci gaba da yiwa shaidun duk tambayoyin tare da sukar domin gudun kada ka cutu? 

Sashin da aka ambata a baya yace nayi maka nasiha dan kada ka fada cikin hadari.

Cukin Fara'a Sheikh Abduljabbar yace ni ban yarda nabarsu suyi bayani ba. 

Dan haka ni a shirye nake kuma haka na zabarwa kaina.

Alqali ya sake komawa kan Malam Abduljabbar - malam Abduljabbar yin haka akwai hadari a tare dakai tunda kai fa din ba lauya bane, me zai hana ka yarda lauyoyin Naka suci gaba da yiwa shaidun tambayoyin Dan gudun samun matsala?

Shehin Malamin Malam Abduljabbar yace ni banyarda ba, ya za ayi ace nace akan ma'aiki kuma bayan ban yiba. Ni ban yarda ba 

Alqali Sarki yola lauyoyin Abduljabbar, kunji abinda ya fada, nantake lauyan Shehin Malamin FAROUK yanuna goyon baya ga Malam Abduljabbar yace mun amince a cigaba da sharia kawai.

Akramukallahu Alqali Sarki yola ya dubi lauyoyin gwamnati ko me zakuce game da wannan abubuwa duk da cewar dama Kuna goyon bayan hakan? Lauyan gwamnati yace mu muna jaddada goyon bayan mu abashi dama yayi tambaya da suka da kanshi domin constitution section 36 su section 6 (d) yabashi dama, haka ACGL 2019 yabashi dama, sai dai muna rokon kotu ta jingine komai kuma ta bashi dama yayi wa shaida tambayoyi Amma batare da lauyoyin sa sun fita ba a Cikin sharia. Domin shi jingine lauya ga wanda ake kara ya bada dama, a Cikin sashi na 36(c) ya bada dama, haka nan kuma wannan sharia sharia a ce ta babban laifi domin idan fa wanda ake kara aka sameahi da wannan laifin to hukuncin kisa ne akan shi. Dan a tsarin mulki ya bada dama duk wanda ake tuhuma da wannan laifi wajibine ya samu lauya me kareshi, kuma duk lauyan da zai iya kare irin wannan sharia to lallai sai yazama lauya ne wanda yayi gwagwarmaya ba karamin lauya ba wanda yanzu yake koyan aikiba, kuma dadin da dawa wannan kotun tana da damar da zata warware kwarkrwayar hukuncin ta da tayi idan akwai DALILIN yin hakan. Dan haka muna ganin a Cikin wannan sharia akwai kwakwakwaran DALILIN warware hukuncin da tayi, domin bashi dama yayi kariya da kanshi yana iya jawo hana lauya yayi aikin shi. Kuma manyan kotuna sunyi shariu kuma sunyi tanadi, dalili da nake cewa wannan kotu tana damar warware hukuncin da tayi muna dogaro da sharia mai suna DAMNA SDESHEN ABEROYEBE SHAFI na 1330 yabada yanayi na warware shari o i da dama. Lauya ya karanto wannan sharia a gaban kotu. Wadannan manyan alkalaine wadan da sukace kotu tanada damar warware hukuncin da tayi idan a ka taradda hukuncin da akayi bazai bayarda sahihancin hukuncin da akayi a baya ba, Dan haka idan ansamu hukuncin da akayi mara sahihanci to a koma baya da warware wa, Dan haka nake rokon wannan kotu mai adalci ta warware hukuncin da tayi a baya, DA tabawa Abduljabbar dama yayi tambayoyi da kanshi kuma tabawa lauyoyin Abduljabbar dama su cigaba da kareshi, kuma munga kokarin da kotu tayi wajen nunawa Abduljabbar hadarin dake Cikin yin tambayoyi da kanshi kuma ya fahimta, Amma yaki gamsuwa, Dan haka muna rokon kotu da ta mai mai ta bawa Abduljabbar shawara akan hadarin da ke Cikin yin tambaya ko suka da kanshi duk da yake cewar shi kariya yake bawa ma aiki ba sharri ba, Amma fa akwai hadari a tare dashi. Kuma inason kotu ta kara sanar dashi maganar CROSS EXAMINATION abinda akeyi a ciki ba lallai ne a yishi a wajen kariya ba kuma hakanan wajen kariya ba lallai bane a yisu a wajen tambayaba, shi abinda Abduljabbar yake so fa ba lallai bane abinda zai yi tambaya ba yayi shi a daidai domin shi a halin yanzu yanaso ne yayi kariya, kuma fa gene na tambaya, ba kamar yanda yake ganiba a wajen da sukayi MUKABALA DA MALAMAI YACE BA A BASHI LOKACIBA to yanzu fa ba haka bane, yabari a zo kariya sai yayi duk sukuwar da zaiyi, Amma mu muna so kotu ta bashi shawara yabari lauyoyi suyi tambaya kuma suyi suka, shi kuma idan anzo kare kai sai yayi kariya da kansa lauyoyi su taimaka masa. Nan zan tsaya Allah ya taimaki sharia ya bata kariya daga lauyan gwamnatiA halin yanzu dai lauyoyin Abduljabbar sufita waje Dan tattaunawa duba da hadarin dake Cikin wannan shari'ar. Kotu ta dawo bayan hutun dan lokaci da ta tafi. Har yanzu dai kotu tana Cikin duba da nazari kan irin halin da malam Abduljabbar zai iya shiga duba da yanayin bakinshi da furutanshi komai na iya faruwa. 

Domin haka kotu itama tayi nazari kuma zata fadi matsayar ta. 

A halin yanzu dai lauyoyin Abduljabbar sufita waje Dan tattaunawa duba da hadarin dake Cikin wannan shari'ar. Abduljabbar yake nema ya dauka ba daidai bane. 

Nima a matsayina na Alkali nayi dukkannin nazari shi Abduljabbar yanada dama ya kare kansa kuma DOKA tayi bayani akan cewar idan laifi babbane to wanda ake kara ko bashi da lauya to dolene a daukar masa lauya. 

Sannan kuma a shariar musulunci dolene idan akaga mutum zai jefa kanshi Cikin hadari to dolene a taimakeshi. 

Domin haka kotu a da ta amince shi abduljabbar zai kare kanshi to yanzu kotu ta sauka daga kan wannan hukuncin, Dan haka ta dawo akan hukuncin shi Abduljabbar zaiyi tambaya da kanshi kuma zai yi suka da kanshi, to amma wani bine lauyoyinsa suna ciki. 

Alqali Sarki yola ya tambayi lauyoyin Malam Abduljabbar Kun sanar da shi ne yanda akeyin tambaya a gaban kotu? Idan Baku sanar dashiba to inbaku lokaci ku fahimtar dashi yanda akeyin tambayoyin? Nan take Lauyan Malam Abduljabbar cikin Barkwanci da raha yace ai tunda ya yarda ai yasan yanda akeyi da alamu da Akwai fahimta sosai tsakaninsu 

Alqali Sarki yola ya tambayi lauyoyin gwamnati ko ina shaidar naku na biyu wanda yazo yabada shaida?

Lauyoyin gwamnati sun kawo shaidarsu na biyu. 

Gashi a gaban kotu, mai suna MURTALA KABIRU MOHD UNGUWAR K/NA'ISA 

Tofah yanzu fagen Daga Malam Abduljabbar sai Shedar Zur 

Murtadha kabir 

Take Mai Girma Sheikh Abduljabbar fara da bisimillah 

Tambaya - 1. Da yayiwa MURTALA

shin ko kasan matsayin shaidar da ya Sheidr abinda aka fada na sharri? Mene hukuncin sa. 

haramun ne Inji Shaidar Zur Murtadha Kabir 

Tambaya ta 2-Sheikh Abduljabbar yace Shin ya sunan wannan shaidar idan mutum yayi kazafi ga wani? Murtala Ya Amsa yace ni na bayarda amsa cewar haramun ne.

Tambaya 3- Sheikh Idan na bayarda hujjoji wanda suka tabbatar da cewar shaidar zur kabayar ko kasan matsayinka a sharia?

Murtadha ya Amsa yace ni ban canza masa magana ba ballantana a ce na canza masa magana.

Tambaya ta 4- Sheikh Abduljabbar yace abinda ka fadawa kotu akan Auren NANA SAFIYYA da kace wannan fassara kirkirarta nayi idan na nunamaka inda na ciro wannan fassarar me zakace tunda kace nine na kirkirota? 

Murtada ya Amsa yace ni abinda zance nabada shedata ne na abinda naji da kunnena a matsayina na dalibi.

Tambaya ta 5- Sheikh Abduljabbar yace Kace ka duba baka gani ba? Murtala ya Amsa yace ai lokacin da kai malam Abduljabbar kake karatun ka fadi lambobin hadisai kuma na duba ban ganiba. 

Acikin tambaya ta 6 fa Malam Abduljabbar yakecewa Murtadha mene banbanicin istish hadi da isnadi a ruwaya?

Charaf Alqali Sarki Yola yiyi Aiki da Lowyoyin Gwamnati ne ya kamata suyi ya Soki SHEIKH Abduljabbar Alqali yace wannan shaida fa abinda yabada shaida a gabanka ya bada shaida nan kuma yace yaji kace kaza da kaza a kan shugaban hallitta S. A. W. Kuma yace ga lambobin hadisin da kafada. To ya za kayiwa shaida tambayoyin abinda shi bai fada ba. Kuma inaso kasani cewar Ana yiwa shaida tambaya ne akan abinda ya fada. Dan haka idan kanaso ka yi tambaya to ka tambayi abinda shaida ya fada kawai Amma kar kafita daga Cikin Abinda Shaida ya fata 

Ya mayar da Matartani Akan Sukar Alqali Sheikh Abduljabbar yace nazo da recorder Dan na danna yanda nayi karatun.

SHEIK Abduljabbar yacigaba da sambadawa shaida tambaya harzuwa tambaya ta 7- Malam Abduljabbar yace kaji nace Muslim yazo da ruwaya ba lafazi? Shedar Zur ya Amsa yace A karatunka ka ambaci lambar hadisan kuma na duba wannan lambobin babu wannan labarin.

Tamvaya ta 8 SHEIKH Abduljabbar yaci gaba da cewa kafin in karanta na hadisi mai lamba ta 1365 kafin wannan ban karanta hadisi mai lamba ta 371 a bukhari ba kuma nace bukhari ya fadi mummunar kalma ga ma aikiba. ? Murtala Amsa ni acikin karatun malam, ko da kafadi wannan lamba ta 371 to ni ban kiyaye ba. Lafazan da kafada su kawai na kiyaye. 

Tambaya ta 9- idan na kunnan kaji a ciki me zakace? Inji Sheikh Abduljabbar

murtala yabada Amsa kamar haka To gaskiya ko da ka kunna ban kiyaye ba.

Tambaya 10-Malam yace bakaji a karatunaba na rantse da Allah ina cewar wannan abinda akace a wannan hadisin abinda aka fada Annabi na bata sunan Annbi baiyiba? Na game da Auren NANA SAFIYYA? Kaji ko bakaji ba? Murtadha ya Amsa yace Ni a matsayina na dalibi naji kayi rantsuwa Amma da nakoma a lambobin banga lafazinba. Bare ma ka kore

Tambaya ta 11-Sheikh Abduljabbar yace shin ko zaka iya fadamin littafi guda daya da idan akace wane ya rawaito hadisi lallai lafazi ake nufi? 

Shedar Zur ya Amsa yace ni dai dalibine kuma da naji malam ya ambaci hadisi kuma da na duba ban ga lafazanba

Tambaya12 Sheikh Abduljabbar yace a matsayinka na dalibina me yasa da na fada ka duba babu bakazo ka tambayeni ba Kafin kazo kotu kabada sheda, domin 'Allah yace ku tambayi wadanda suka sani idan bakusan Abu ba?' SHEDAR ZUR Ya Amsa yace na farko bansami cikakken lokacin zuwa wajenkaba domin kai ne kace kana Cikin wani bahsi a daina zuwa wajenka. Ni kuma na shagaltu da zuwa wajen karatu. 

Tambaya ta 13 Sheikh Abduljabbar yace a yanzu da zan nunamaka Gaza warka ce ta sa baka gani ba to me zakace? Amsa yace indai a karkashin wannan lambobin ne idan ka nunamin zan yarda.

Tambaya ta 14 Shehu Abduljabbar da ka duba kaga kalmar JA ALA ITKAHA SADAQAHA? Shedar zur ya Amsa yace eh nagani. Malam Abduljabbar yace to mene ma anar ta? 

Anan ne lauyan gwamnati ya Mike ya tambaya cewar shin mu munga malam Abduljabbar ya bude wani littafi ya karanta wata kalma wadda bamu santaba. Wane littafi ne? Idan ba a Muslim bane to banyar daba. Ya fada mana wane littafi ne? 

Abduljabbar yace sunan wannan littafin Sahih MUSLIM ne tare da SHARHI. 

Alqali Sarki yola ya koma kan Sheikh Abduljabbar yace duk tambayar da za ayi wa shaida to ka tsaya akan gundarin hadisin da aka am bata. Da abinda shaida ya fada. Idan kanaso zakayi sharhi to kabari sai nan gaba

SHEIKH Abduljabbar yacewa shaida. MENENE ma anar wannan kalmar? Shedar Zur ya Amsa yace ma anar ta shine ANNABI S. A. W. YANTA TA NE A MATSAYIN SADAKINTA. KUMA KUMA ANA SANAR DA BAWA NE KO A YANTASHI KUMA ANA IYA SAKA YANTAWA AKAN AMATSAYIN SADAKI. Dan haka wannani shine ma anar. Ba kamar yanda kai Abduljabbar ka fada ba kace fyade. YANTAWA daban da fyade.

Alqali ya tafi hutu ,

Bayan Alqali ya dawo daga hutun rabin awa, kuma ya waiwayi Sheikh Abduljabbar ko yanada sauran tambayoyi, ?

Nanan take ne lauyan gwamnati ya tashi yayi rokon kotu da ta sanya Sheikh Abduljabbar yazo da littafi mara sharhi Dan yin bayani akan wadannan hadisan.

Alqali Sarki yola ya tambayi Sheik Abduljabbar ko yanada littatafai marasa sharhi?

Malam Abduljabbar yace ni bani da marasa sharhi saidai ina rokon a samomin aro a ko ina ne kuma a kawomin a duk inda nake dan yin nazari akansu.

Alqali Sarki yola ya bawa Sheikh Abduljabbar dama da idan yanada kudi ya siyo nashi da kanshi, Malam Abduljabbar yace ni bani da kudin sayan littafin .

A nan ne Alqali ya waiwayi lauyan gwamnati ko me zakuce, ?

lauyan gwamnati yace insha Allah Gwamnatin jihar kano zata bashi kudi ya sayi littafin shi kuma Alkali yaje ya samo irin littafin.

Nan take Sheik Abduljabbar to na gode akan kudin da gwamnatin zata bani na sayi littafin bukhari da Muslim mara sharhi.

Dan haka dan Haka Alqali ya daga sharia zuwa lokacin da za a zo da sahihul bukhari da Muslim marasa sharhi,

yace ita kuma kotu zata Nemo wadannan litattafan a ma a jiya ta litattafa da ke BUK Alqali yaba da Umarni a rubuta takardar katin neman izini zuwa jamiaar bayero labirary Dan kawo bukhari da Muslim masu matani babu sharhi. Kuma kotu tayi umarni da lallai Government din kano da ta aikawa Sheikh Abduljabbar kudin da zai sayi littafin bukhari da Muslim daga yau zuwa ranar litinin mai zuwa.Kotu tayi umarni da shaida shima zai dawo a wannan Rana da za'a sake zama. 

Kotu ta dage cigaba da zaman shari'ar har sai nan da sati biyu masu zuwa wato ranar Alhamis 25-11-2021

Comrade Diso Zaria 

Ahlul Kisa'i Radio and tv Zazzau 

SHEIK ABDULJABBAR YA GAJIYAR DA LAWOYIN GWANATI SUNKASA SUKARSHI AKAN TAMBAYOYI GOMA SHA UKU DA YAYIWA SHEDAR DA GWAMBATI TAKAWO 

©Fatimiyya Alawuyya Tv 

Comments