RAHOTON ZAMAN KOTU NA YAU 23/12/2021. NA SHEIKH ABDULJABBAR KABARA

 Acigabada sau raron shariar sheikh Abduljabbar. A yau 23/12/2021.



Yadda Ta Kasance A Zaman Shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara Da Gwamnatin Kano


A yau 23 ga watan disamba ne aka cigaba da gabatar da shari’ar nan ta Sheikh Abdujabbar kabara da gwamnatin kano a babbar kotun shar’ar musulunci dake Kofar kudu.


Kamar yadda rahoton zaman baya ya nuna, a yau lawyoyin gwamnati za su cigaba da gabatar da shedu a gaban sharia, inda aka gabatar da Farfesa Ahmad Murtala na Jami’ar bayero dake kano a matsayin sheda na 4.


Farfesa Ahmad Murtala ya bayyana wa kotu cewa tsawon shekara takwas shine yake gabatar da bawa dalibai bincike akan hadisan Annabi SAW da suke fassarawa zuwa hausa, yayi karatu a matakin digiri na farko a fannin addinin musulunci musamman hadisan manzon Allah SAW a jami’ar Bayero dake kano, sannan yayi digiri na biyu akan hadisan Manzon Allah SAW a jami’ar bayero, sai digirin san a uku akan HAdisan Manzon Allah da suka shafi ka’idojin fikihu a jami’ar Bayero.


Ya kuma bayyana cewa yayi karatu a wajen malaman azure da dama kamar su; Malam Adamu na mangwarori, Malam Salihu Gusau, da Malam Yusuf Uba Mandawari. Ya kuma bayyana cewa ya samu shedar kamala karatu ta ijaza akan koyar da hadisan Manzon Allah SAW daga Wajen Malam Karshi a sakkwato, da gidan Malam gyal-gyal wanda sanadin say a dangane ga shehu usmanu hark an Annabi SAW. Ya kara da cewa yana da ijaza daga gidan Malam Boyi sokoto, Malam Gado da Masu dake sabon sara, Malam Kona da Malam Juma daga Zaria, Sheikh Taqiyyuddeen Annadawi Alhindi na kasar Indiya, Sheikh Abdulaziz bn Allal Aljaza’iri, da Sheikh Dahir Aljad na Algeria.


Ya sake bayyana cewa ya samu shedar zama dalibi mafi kwazo sanda y agama digirin san a farko a jami’ar Bayero a shekara ta 1997, kuma yanzu yana matakin Farfesa, Kuma shugaban Sashen koyar da addinin musulunci da sharia a jami’ar Bayero.


Saidai Lawyoyi masu gabatar da kara sun ce shedar bai zo da takardar wannan ijazozi ba, amma sunyi rokon a basu dama a zaman a gaba su kawo su kafin wanda ake kara ya fara gabatar da tambaya ga sheda.


Lawyan mai gabatar da kara ya tambayi shedar cewa ko yasan wani hadisi da yake Magana akan auren Nana Safiyya a sahihu Muslim?


Ya amsa da cewa; “Na san hadisin da yake cikin muslim har ma da na cikin bukhari”.


Anan ne aka nemi kotu da ta bada littafin bukhari da muslim dan a gabatar wa da shedar ya karanta hadisan. Shedar ya karanta hadisi mai lamba ra 1365 da 1428 cikin littafin Muslim a yaren larabci ya fassara cikin yaren Hausa.


Lawya mai gabatar da kara ya tambaye shedar bayan ya kamala karanta hadisin cewa “Wanda ake kara yace a akwai fyade daraja ta daya da Annabi SAW yayi wa Nana Safiyya, sanna yace akwai kwace da Annabi yayi wa Sahabin sa Dihya da aka bashi labarin Safiyya tana cikin kason san a ganima, me zaka ce akan wadannan kalamai?”


Sheda ya fara da cewa “Ina neman tsarin Allah daga wadannan munanan kalmomi, da farko maganar fyade bata taso ba kwata kwata a wadannan hadisai, babu ita babu alamarta. Saboda abinda ya faru a cikin hadisin Magana ce ta yaki da Annabi SAW yaje da sahabban sa Khaibara, Kuma Allah ya bashi nasara a yakin. Dan haka duk abinda aka samu sunan sa ganima, Amma ana bashi suna na musamman da “FAY’U” shi kuma ganima ko FAY’U, Annabi yana da iko a matsayin na Shugaba SAW ya dauki ko ya zabi abinda yake so a ciki, dan haka kasancewar ya bawa Dihiya damar ya dauki wata baiwa a cikin bayin, daga baya ta canza masa da wasu, wannan abu ne da sharia’ar musulunci ta tabbata da ga Annabi SAW domin duk malami suna cewa; yana daga kebence kebencen Manzon Allah SAW shine zabar wani abu a cikin ganima ko Fay’u kafin a raba da bayan an raba. Shine Malaman fikihu musamman Malikiyya suke cewa (Safiyyul Magnami) ma’ana Zababbun abubuwa daga cikin ganima. Har Imamul Kharshi a cikin Sharhin san a Mukhtasar ya bada misalin Safiyya a matsayin Safiyyul Magnami.”


“sannan har ila yau, hadisin ya nuna cewar Dihya a mazamin sa na Sahabin Annabi SAW da yasan darajar sa da kimar sa, ya gamsu da abinda Annabi SAW yayi, shine a inda ruwayar take cewa (FA A’A DAAHU BIHA MA ARAADA), sai ya bashi abinda yake so, shine daya ruwayar ta fassara da bayi bakwai ko kai bakwai. Dan haka maganar zancen Fyade babu ita kwata kwata, bai kamata musulmi ya kawo wannan tunani ba saboda ka’idar da ta shafi Annabi SAW, Allah yace (ANNABIYU AWLA BIL MUMININA MIN AMFUSIHIM), Annabi shine wanda yafi cancanta musulmi (su kiyaye darajarsa) akan kawukan su.” Inji Shedar


Ya kara da cewa; “Babu abinda yake nuna kwace a cikin dukkan hadisan ta kowacce fuska, domin bayanin da akayi a cikin hasisin ya nuna cewa Dihiya ya gamsu da abinda Annabi SAW yayi, shine akai ishara gareshi da wani lafazin cewa; (FASHTARAAHA BI SABA’ATI AR’USIN), sai annabi SAW ya siye ta da kai bakwai, wanda ma’anar shi ya bashi da gamsuwar sa”


“Babu inda ya nuna a cikin hadisin cewa Annabi ya aure ta auren dole, domin ita a mazaunin baiwa take, hadisan abinda suka nuna Kenan. Shi kuma bawa bisa ka’idojin yaki da aka sani, yana karkashin mallakin ubangidan sa ne”


Lawyoyin suka sake tambayar sheda da ya fassara ma’anar jumlar (JA’ALA ITQIHA SADAAQAHA), sai ya masa da cewa; “Ya sanya yanta ta shine sadakin ta”.


Ya cigaba da cewa: “A wannan aure Annabi SAW bai bada sadaki na kudi ba, sai dai ya sanya yanta ta shine sadakin ta. Dan haka hadisan gaba daya abinda suke nuna wa Annabi SAW ya aureta ta wannan fuska, kuma hadisan sun dada nuna cewa ita safiyya ta gamsu da hakan. Dan haka ba wani dalili na maganar babu sadaki, ga sadaki nan a cikin hadisin an fada.”


 


Ku dakace mu dan samun cigaban wannan rahoton.

©Fatimiyyaa

Comments

Post a Comment