SAHIHUL BUKHARI AGURIN YAN KOGO


 SAHIHUL BUKHARI A GURIN 'YAN KOGO

ALMAJIRAN DR. ABDULJABBAR KABARA


✍️ Saifullahi Murtala Jibia


WAI ME YA HAƊA ('YAN AS'HABULKAHFI) DA IMAMUL MUHADDISINA BUKHARI ??


AMSA :

________


HANNUN-RIGA BUHARI YA YI DA ANNABI (SAW) BISA SHARAƊIN KARBAR HADISI ! 


Ma fi yawa daga wasu 'yan uwa musulmai nã kallon Almãjiran Dr. Abduljabbar Nasiru Kabara Kano (H) matsayin waɗanda suka zare kansakalin ruguje/rosa wannan littafi da Imamul Bukhari (R) ya rubuta domin su cimma wata manufa, alhali ba haka ba ne. 


WALLAHI   !!!  TALLAHI   !!!   BILLAHI  !!! 


Ba wasa 'Yan as'habulkahfi suke ba, cewar su " KOWAYE ANNABI (SAW) YA FI SHI " ! 


Bã zã mu gani a rubuce ba, Annabi (saww) ya ce a yi Gabas, Imamul Bukhari kuma ya ce a yi Yamma , saboda tsoron tunzurin ku mu rabu da Ma'aiki (saw) mu bi Buhari don mu zauna da ku lafiya. Muna ce da ku, idan mafarki kuke, wallahi ku farka ! Idan kuma ba kusan gurin ba, yau insha'allah za mu kawo maku, idan mu ne muka jahilci karatun sai ku ganar da mu, in kuma ku ne ba ku sani ba, to yau za mu sanar da ku, ruwanku ku dauka. Mu dai mun iyar kuma mun fita har a gurin Allah (swt).


Allah (swt) bai aiko Imamul Muhaddisina Bukhari ba, kuma bai aiko Ameerilwa'izina Abduljabbar ba, dukkaninsu Malammai ne da za su iya yin daidai, kuma za su iya yin kuskure.Idan har Buhari ya saba da Annabi (saw) to wajibi ne a rabu da shi, a wurgas da abin da yazo da shi. Idan Abduljabbar ne ya saba da Ma'aiki, shi ma wajibi ne a rabu da shi, a bi Manzon Allah (saw) don kuwa, shi ne wanda Allah (swt) ya aiko shi zuwa gare mu matsayin JakadanSa .


Bã tun yau ba, muke karanta wannan littafi na Buhari, kuma muna aiki da shi, kuma har yau har gobe, muna nan kan hakan, sai dai , bincike ya tabbatar mana da cewa, akwai wasu hadisai da aka lullube su da irin rigar nan ta inganci, bisa sharaɗin da shi Buharin ya ƙirƙiri abin sa mai tsananin gaske, da ya siya wa littafin daraja/ƙimar kasancewa matsayin littafi na ɗaya  ( 1 )   ((  Asahhulkutubi  )) bayan Alƙur'ani littafin da Allah (swt) Ya saukar, inda ire-iren waɗannan Hadisai, idan ka ɗauko su, ka ɗora su, bisa sharaɗin da Annabi (saw) ya bayar na auna zancensa, sai ka taras da su sun yi hannun-riga da sharaɗin Annabin (saw). Wanda iren-iren waɗannan Hadisai dai, su ne ke cin karo da Alkur'ani, kuma su ne, ke cin karo da junansu, kuma su ne ke tawaye darajar Annabin mu (saww)


Irin waɗannan Hadisan dai ne, kafiran nan na FARANSA, ko DANMAK, ke daukowa suna yin kãtīm, don practicing ɗin abin da ya shafi matanin hadisin, wanda hakan ke matuƙar sosa wa musulmai muminai rai, inda binciken Jagoran mu, ya gano masa cewa, tabbas Hadisan Ƙarya ne, ya wajaba a fidda su daga litattafan mu na Muslinci. Uwa-uba, irin Hadisan da 'yan ta'adda suke karantawa, suna karkashe mutane wai da sunan Jihadin Muslinci 😭 Subhanallah !!! Wanda hakan ya sa, waɗanda ba musulmi ba , ke kallon Addinin Muslinci matsayin Addinin 'YAN TA'ADDA wanda babu komai cikin sa sai koyar da zubar da jinane 😭 !


Wannan 👆shimfiɗa ce, yanzu za mu shiga cikin gundarin karatun in Allah (swt) Ya so.


INDA BUHARI YA SÃ'BÃ DA MA'AIKI SAW

_______________


ME AKE BUƘATA A CIKIN HADISI GURIN MANZON ALLAH ( SAWW ) ???


ME AKE BUƘATA A CIKIN HADISI  GURIN IMAMUL MUHADDISINA BUKHARI ????


TIRƘASHI  !!!


To, a nan ne fa, aka sami sabani tsakanin Manzon Allah (saw) da Imamul Bukhari !!! Inda Annabi (saw) ya yi Gabas , shi kuma Buharin ya yi Yamma. Shi kuma Shugaban 'Yan Kogon As'habulkahfi Warraƙeemi da ya fahimci haka , sai ya yi wa almajiran sa hannunka-mai-sanda cewa Imamul Buhari fa, ya saba da Manzon Allah (saw) saboda haka, zamu saba da shi a nan . Inda wasu ke kallon mu a yau , wai rosa littafin muke so mu yi kawai don su bata mana suna a idon mutane, waɗanda ba su san wannan jawabin ba da za mu kawo maku a yanzu.


GA AMSAR TAMBAYA TA FARKO DAGA BAKIN MANZON ALLAH (SAWW).


Me ake buƙata cikin Hadisi a gurin Annabi (saw) ?? Mu ɗan leƙa waɗanan litattafan :


رواه أحمد في  "المسند" رقم : ١٥٤٧٨- ١٦٤٨٣- ١٦٠٥٨ - ٢٢٥٠١ - ٢٣٦٠٦ .


رواه ابن حبان رقم : ٦٣، والطحاوي رقم : ه٢٩٦، 


وابن رجب في" الجامع " رقم ج ١ ، ص ٢٥٥، والخطيب في "الكفاية" ١٣٠١،  


والمناوي في " فيض القدير " ج ٤ ص ١٧٧، والسيوطي في " مفتاح الجنة " ج١ ص ٢٥.


ZA MU JI, ABIN DA AKE BUƘATA A CIKIN HADISI GURIN MANZON ALLAH (SAWW) SHI NE :


👉 HADISI : Ya zama mai kyau ga mutane 

👉 HADISI : Ya yi daidai da hankulan su.

👉 HADISI : Ya yi daidai da mutuntakarsu.

👉 HADISI : Ya yi daidai da yadda zukatan mutanen za su sami nutsuwa da jin sa, ba wai akasin hakan ba. 


MU TAFI CIKIN MUSNADU NA IMAMUNA AHMAD IBN HAMBAL HADISI NA 16058


الجزء رقم  :  25 ، الصفحة رقم : 456


16058 حَدَّثَنَا أَبُو عَامِرٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا سُلَيْمَانُ بْنُ بِلَالٍ ، عَنْ رَبِيعَةَ بْنِ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ ، عَنْ عَبْدِ الْمَلِكِ بْنِ سَعِيدِ بْنِ سُوَيْدٍ ، عَنْ أَبِي حُمَيْدٍ ، وَأَبِي أُسَيْدٍ ، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " إِذَا سَمِعْتُمُ الْحَدِيثَ عَنِّي تَعْرِفُهُ قُلُوبُكُمْ، وَتَلِينُ لَهُ أَشْعَارُكُمْ، وَأَبْشَارُكُمْ ، وَتَرَوْنَ أَنَّهُ مِنْكُمْ قَرِيبٌ، فَأَنَا أَوْلَاكُمْ بِهِ، وَإِذَا سَمِعْتُمُ الْحَدِيثَ عَنِّي تُنْكِرُهُ قُلُوبُكُمْ، وَتَنْفِرُ أَشْعَارُكُمْ، وَأَبْشَارُكُمْ، وَتَرَوْنَ أَنَّهُ مِنْكُمْ بَعِيدٌ، فَأَنَا أَبْعَدُكُمْ مِنْهُ ".


حكم الحديث: إسناده صحيح على شرط مسلم


Daga Abī Humaidīn da Abī Usaidīn : Lallai Annabi (saww) ya ce "Idan ku ka ji Hadisi aka ce daga gurina yake, sannane a gurin zukatan ku, wato ( wanda ya yi daidai da hankalin ku, kuma zukatan ku suka nutsu da shi ) wanda kuma ya yi daidai da mutuntakar ku, kuna ganin kusancin sa da ku, ( wato kowanen ku zai iya aikata abin) to ni ne ma fi dacewar ku da shi ;  idan kuma kuka ji Hadisi aka ce daga gare ni yake , amma zukatanku na ƙin abin , bai yi daidai da hankali da kuma mutuntakar ku ba, kuna ganin nisantarku da abin ( wato ba zaku iya aikata shi ba )  to ni ne ma fi nisantar ku da shi.


ISNADIN HADISIN INGANTACCE NE BISA SHARAƊIN MUSLIM 🤷‍♂️🤷‍♂️🤷‍♂️🤷‍♂️🤷‍♂️ !!!


👂 MASOYA ANNABI (SAW) MU KULA !!!


Umarni ne Manzon Allah (saw) ya yi mana ba wai shawartar mu yake yi ba ! Mu kam, sami'inã wa aɗa'anã. Kū mã , mu nai maku tuni da faɗin Allah (swt) a Suratunnūr (63)


فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَن تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ.


Waɗanda suke sã'bãwã daga Umarnin sa, to, su yi saunar wata fitina ta sãmē su, kõ kuma, wata azãba mai raɗaɗi ta same su.


Da kuma faɗin Allah a Suratunnisã'i (115 )


وَمَن يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءتْ مَصِيراً


Kuma wanda ya sã'bã wa Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar muminai,zã Mu jibintar masa da abin da ya jibinta, kuma Mu ƙõne shi da wutar Jahannama, kuma tã mūnana ta zama makoma .


Ƙofar Birnin Ilimin Manzon Allah (saw) ya na tare da wannan umarni na Annabi saw wato MAULANA IMAMUNA ALIYU (AS) 


MU ƊAN DUBI WAƊANNAN LITATTAFAN


رواه البخاري رقم ١٢٧، وابن حجر في " مقدمة الفتح " ج١ ص٤٤٤،  وابن بطال في " الشرح " ج١ ص٢١٨، والسيوطي في " تدريب الراوي" ج٢ ص ١٣٨.


Ba ri mu yi amfani da Lafazin Imam Buhari Hadisi na ( 127 ).


الجزء رقم :1، الصفحة رقم:37


127 وَقَالَ عَلِيٌّ : حَدِّثُوا النَّاسَ بِمَا يَعْرِفُونَ أَتُحِبُّونَ أَنْ يُكَذَّبَ اللَّهُ وَرَسُولُهُ حَدَّثَنَا عُبَيْدُ اللَّهِ بْنُ مُوسَى ، عَنْ مَعْرُوفِ بْنِ خَرَّبُوذٍ ، عَنْ أَبِي الطُّفَيْلِ ، عَنْ عَلِيٍّ بِذَلِكَ.


Maulana Imamuna Aliyu (as) ya ce : ku zantar da mutane da abinda yake sananne a gurin su wato (abin da zai yi daidai da hankulan su ) kuna so mutane su ƙaryata Allah da Manzon Sa ne ? Wato ( idan ana zantar da su Hadisan da suka saba da hankulan su ).


SHI MA IBN ABBAS (RTA) YANA TARE DA WANNAN UMARNI NA ANNABI (SAW) MU ƊAN LEƘA WAƊANNAN LITATTAFAN : 


رواه الدارمي رقم :  ٦١٤، والبيهقي في " دلائل " رقم ٢٨٤٢، و أبو الفضل في " المسند الجامع " ج ١٧ ص ٢٦٢.


BARI MU YI AMFANI DA LAFAZIN SUNAN DÃRIMĪ HADISI NA (( 614 ))


614 فَكَانَ ابْنُ عَبَّاسٍ إِذَا حَدَّثَ قَالَ : إِذَا سَمِعْتُمُونِي أُحَدِّثُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَلَمْ تَجِدُوهُ فِي كِتَابِ اللَّهِ أَوْ حَسَنًا عِنْدَ النَّاسِ، فَاعْلَمُوا أَنِّي قَدْ كَذَبْتُ عَلَيْهِ.


Abdullahi Bn Abbas ya kasance idan zai zantar da Hadisi yakan ce (( idan ku ka ji ina zantar da ku Hadisi kuma na ce daga Annabi (saw) yake ,amma ba ku sami abin da yake ƙarfafar Hadisin ba cikin Alƙur'ani,  ko kuma a gurin mutane suka ji Hadisin ba mai kyau ba  , to ku sani lallai nã yi wa Annabi (saww) ƙarya.


SHIN SHEHU ABDULƘADIR JILANI UBAN ƘADIRAWA ( R ) WAI SHI MA YANA TARE DA WANNAN UMARNI NA ANNABI SAW ?


Amsa : Ƙwarai da gaske ! Zo mu leƙa cikin Algunya ( littafin Shehu Abduƙadir Jilani )


وقد صرح الشيخ عبد القادر جيلاني بهذه الحقيقة في كتابه " الغنية " ج ١ ص ١١٥، " باب الأمر بالمعروف " 

"فصل" والذي يأمر به وينكر على ضربين :- 


فكل ما وافق الكتاب و السنة ((والعقل)) فهو معروف ، وكل ما خالف ذالك فهو منكر . ثم ذالك ينقسم إلي قسمين... إلخ


Shehu Abdulƙadir Jilani ya ce : Duk abinda ya yi daidai da Alƙur'ani da Sunnah da ( HANKALI ) to wannan sananne ne, kuma dukkan abin da ya saba da wannan , to  abin ƙī ne ..............


TO ABIN DA ZAI BA KA MAMAKI SHI NE, IMAMUL BUKHARI (R) YA SA'BA DA DUK WAƊANNAN MA'AUNAI. KAFIN IN KAWO MAKA SHARAƊIN BUHARIN WANDA ZAI ZO A RUBUTU NA GABA. 


Ga wani Hadisi, don girman Allah , ka ɗora shi bisa waɗannan ma'aunai mu gani ko zai hau,  wato  ya yi daidai da hankali da mutuntaka ,da nutsuwar zuciya da kyawo a gurin mutane ??????


👉 MU LEƘA SAHIHUL BUKHARIN ((224))


«224» حَدَّثَنَا آدَمُ قَالَ: حَدَّثَنَا شُعْبَةُ عَنِ الأَعْمَشِ عَنْ أَبِي وَائِلٍ عَنْ حُذَيْفَةَ قَالَ أَتَى النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سُبَاطَةَ قَوْمٍ فَبَالَ قَائِمًا، ثُمَّ دَعَا بِمَاءٍ، فَجِئْتُهُ بِمَاءٍ فَتَوَضَّأَ.

 

[أطرافه 225، 226، 2471، تحفة 3335]. 


Daga Huzaifata ya ce : Annabi (saw) ya zo jujin wasu mutane sai ya yi fitsarinsa tsaye sannan ya yi kira da a kawo masa ruwa sai na zo masa da shi, sai ya yi alwala .  Wato (( bayan kammala fitsarin a tsaye 😭😭 )).


Shi fa wannan Hadisin, ba a rubuta shi ba sai don Musulmi su yi aiki da shi domin su sami ladar koyi da Annabin su (saww).


A HANKALCE :


👉 Tayaya, Zuciya za ta nutsu da cewa wai shugaban halitta, ya fito daga gidan sa, ya tsaya waje cikin jujin mutane ya yi fitsari a tsaye, mutane na kallon sa ????


👉 Tayaya zai yi daidai da hankulan mu , a ce wai Annabi (saww) yana  fitsari a tsaye, aikin da ɗaya daga Shehunan mu, sam ba mu taba ganin suna aikatawa ba, sabo da yin hakan ya saba da mutuntaka, da kuma kyakkyawar ɗabi'a. Shi kuwa Annabi (saw) an aiko shi ne don ya cikasa ɗabi'un girma kamar yadda ya zo cikin muwaɗɗã Hadisi na ( 2633 ) da Musnadu Na Ahmad Hadisi na ( 8952 ), Mu dubi lafazin Imam Ahmad


الجزء رقم : 14، الصفحة رقم : 512


8952 حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ مَنْصُورٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا عَبْدُ الْعَزِيزِ بْنُ مُحَمَّدٍ ، عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَجْلَانَ ، عَنِ الْقَعْقَاعِ بْنِ حَكِيمٍ ، عَنْ أَبِي صَالِحٍ ، عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " إِنَّمَا بُعِثْتُ لِأُتَمِّمَ صَالِحَ الْأَخْلَاقِ ".


حكم الحديث: صحيح، وهذا إسناد قوي.


Yaushe, yin fitsari a tsaye zai zama ɗabi'ar girma ga wanda Allah (swt) Ya ce da shi :


وَ إِنَّكَ لَعَلَى خُلُقٍ عَظِيمٍ .


▶Domin mu ƙara fahimtar munin wannan Hadisi, ga wani ɗan taƙaitaccen misali :


( 1 ) Shehu Abdulƙadir Jilani (R) da Shehu Usmanu Ɗan Fodio, sun fito daga gidajen su, suka tsaya cikin jujin wasu mutane, su ka kwance wandunansu, suka saki fitsarin su a tsaye jama'a na kallonsu . Baƙadire shin kã yarda shehunnan ka wai zã su iya aikata hakan ?? Abin fa bã zai yi kyan gani ba, sarkin waliyyai a tsaye yana fitsari🤦‍♂️!


( 2 ) Shehu Tijjani (R) da Shehu Ibrahim Inyass, sun fito daga gidajensu, suka tsaya cikin jujin wasu mutane, suka saki fitsarin su a tsaye jama'a na kallon su. Batijjane shin kã yarda shehunnan ka wai zã su iya aikata hakan ?? Abin fa bã zai yi kyan gani ba, Shehu Ibrahim Inyass Sahibul faidah a tsaye yana sakin fitsari , murīdinsa kuma yana kallon sa 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️ !!!


( 3 ) Shehul Islam Ibn Taimiyya (R) tare da  Malam Abubakar Gumi sun fito daga cikin   gidajen su, sai suka tsaya cikin jujin wasu mutane suka kwance wandunan su suka saki fitsarin su a tsaye , jama'a na kallon su. A hankalce ba za mu taba yarda ba, a ce shehunanmu sun yi hakan kamar an cī masu mutunci ne. To don me za mu yarda Annabi Muhammad (saw) wai ya yi hakan kawai saboda Buhari ne ya ruwaito ????


A ƘARSHE WAƊANCAN SU NE MA'AUNAI DA MUKE AUNA HADISI DA SU, HADISIN DA YA YI DAIDAI DA SU, MUNA TARE DA SHI , WANDA YA SABA DA SU, TO BÃ MÃ TARE DA SHI, KÕWÃYĒ YA RUWAICE SHI


Mu haɗu rubutu na gaba, idan Allah (swt) Ya so, wassalamu alaikum warahmatullah


🇳🇬AS'HABULKAHFI JIBIA SOCIAL MEDIA TEAM, 21/09/2021,🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬.

Comments