SHIN DA GASKE SHEIKH ABDULJABBAR YA ZAGI ANNABI SAW 01
Marubuci:
Abubakar bin Alhassan (Lalau mai Alburda) kaura Tudun bojuwa.
Yafara da sunan Allah Mai rahma mai jinkai,
Da salati da sallama ga Annabi Muhammad saw.
Bayan Haka:
Godiya ta tabbata ga Allah makagin sammai da kassai,Wanda yasanya tafiyar Allah da annabinsa,ta Ahlul baiti anabata matukar wahala,
Saidai duk rintsi da wahalar watarana saita zama sai labari,gaskiya tayi halinta,Wanda ya lazinta duk Wanda zai dafa musu zaita haduwa da kalu bale da jarrabawa iri iri,daga wannan sai wancan sai kuma wata, bazai taba rabuwa dasuba sai bayan mutuwarsa.
Ya ubangiji ina rokon ka dawwama salati ga Annabin da bakai irinsaba,Annabin da yayi ta haduwa da jarrabawa nau'i nau'i,Wanda bai taba fadar son zuciya ba, Wanda duk abinda yafada haka yake, Wanda yayi alkawari har duniya takare zuriyar ahlul baiti baza ta ba karewaba, Annabi muhammadu (Sllalahu Alaihi wasallama.
Bayan haka uban giji yana cewa
الذين إذا أصابتهم مصيبة قالوا إنالله وإنا إليه راجعون"
Yakuma cewa:
واتقوا فتنة لا تصيبن الذين ظلموا منكم خاصة"
Anyi Ashara rai,masharranta, makirai, mahassada, bakaken makiya Allah a garin kano,Wanda ake kiransu da yan majah ko yan clob, Wanda suka hadu, suka dunkula, suka hada karfinsu waje daya -izala, salafiyya, kadiriyya, tijjaniyya, faira, domin suga bayan sheikh Abduljabbar nasiru kabara,badon komaiba sai don tatacciyar bakar hassada da sukeyi masa, musamman saboda yayi raddidduka ga shehunnan su, sukayi tamasa yarfen zagin shugaban halitta yakeyi, Amma Ga hakikanin
LAIFUFFUKAN SHEIKH ABDULJABBAR.
shizamu kawo muku A post nagaba.
21/12/2021
©Fatimiyyaa
Allah yasaka da alkahiri
ReplyDelete