TAMBAYAR DA WANI BATACCE YAGAGARA SAMUN AMSA.AGUN MA'ABOTA SHIRIYA


 Daga wani Bawan Allah


NI BATACCE NE, WA ZAI SHIRYAR DA NI ZUWA GA KYAKKYAWAR FAHIMTA.


Har yanzu na rasa wanda zai gamsar da ni akan wadannan Hadisan akan abubuwan da suke koyarwa, wanda ake so mu kwaikwayi Shugaban Halitta SAW cikinsu, ko su bayyana muna wata Falala ta shi ko Khususiya.


1- Muslim ya riwaito Iyayen Manzon Allah S.A.W Suna Wuta.


2- Bukhari ya riwaito, Annabi S..a..w yana fitsari Tsaye kan hanya cikin Shara.


3- Bukhari ya riwaito, Annabi S..a.w yana kewayar Matansa Goma Sha daya cikin awa Daya da wanka Daya, da Rana da Dare.


4- Bukhari ya riwaito, Annabi S.a.w yana shiga inda Matar wani Sahabi ya kwanta inda take ta dafama abinci ya ci, sannan ta kama cire Masa keyar dake garesa.


5- Bukhari ya riwaito, Annabi S.a.w yana fushi irin na Mutane har ya yi zage zage ba bisa qa'ida ba.


6- Bukhari ya riwaito, Annabi S A W a gidansa matasan uwayen Muminai suna Zage Zage a gabansa, har yayi Umurni da wata cikinsu ta yi da rama Zagin da akayi Mata, sannan ta yi zagi mai Muni, sai ya kama Murmushi ya na jinjina Mata akan Wannan zagin.


7- Bukhari ya riwaito Annabi S A W wani Sahabi ya hau kan rufin daki ya kama kallon Annabi Alhali Shugaba saw Yana biyan buqatarsa.


8- Bukhari ya riwaito Annabi S A W Annabi ya kan halarcin wurin da ake kade kade da Raye raye, tare da Shaidanun Mutane da Aljannu.


9- Bukhari ya riwaito, Annabi S A W, Annabi anyi masa Sihiri har ya rasa hankalinsa saboda tsananin tasirin sihirin gareshi.


10- Muslim ya riwaito, Annabi S A W in yaga mace ta wuce inda yake zaune sha'awarsa za ta motsa ya tashi ya Shiga gida a guje don motsawar sha'awa.


Wadannan, kadan ne daga cikin Hadisan da ban Fahimci saqon da suke isarma Al'umma ba, wanda ake son Mutum ya koya na Ibada ko Mu'amala cikinsu


In akwai wanda ya fahimci wani saqo mai wani amfani da saninsa zai amfanar da mu, cikin Hadisan nan gaba daya ko cikin dayansu ya ganar da ni, Ina Matuqar Buqatawa zuwa ga hakan, tare da kasnacewa ta mai Matuqar Farin ciki da godiya gareshi.


Akwai wasu Hadisan sunfi kam, sai dai Ina son a Fara Fahimtar dani wadannan, Sannan mu dauko sauran domin Abin ya Kasance cikin tsari.


Zuciya tah a bude ta ke, Saboda wa fauqa kulli ziy Ilmin Aliiymun.


©Fatimiyyaa

Comments