YADDA SHEIKH ABDULJABBAR (H) YAFASSARA MALAMAI MASU DAAWA A WANNAN LOKACIN


 YADDA SHEIKH DR.ABDULJABBAR (H) YA FASSARA MALAMAI ( MASU DA'AWA ) NA WANNAN ZAMANI DA MUKE CIKI   !!



Ma fi yawan malamai, ba dukkaninsu ba ne, su ka maida wazifar koyarwa , a matsayin ibada !!! Dayawansu, sun maida ita ( koyarwar ) sana'a ce,  saboda haka, kallon su kullum, ina riba take.


 Duk abin da zai ba su faɗuwa, za su yaƙe shi, komai kyawunsa . Saboda su, kasuwanci ne suke yi da wannan al'amari. To kuma, a nan ne , musibar take . Sai dai,  ita kuma gaskiya, zata juya ka, kamar waina ta kife , idan baka bi ta ba !

 Sai kuma ta tafi da wasu, kai kuma ka zama tarihi , inji Malam . A karatunsa na shimfiɗar tafsirin Alƙur'ani Maigirma ,mai suna jaufulfara zama na sittin da uku (63)



Comments