DA'AWAR SHEIKH ABDULJABBAR KABARA ƘARA FAƊAƊA TAYI BAYAN KAMA SHI DA AKAYI !!!
Daga shehu yako yako.
Tun bayan wasan kwaikwayon daya gabata wanda aka kira da muƙabala mutane da dama daga sassan gurare da ƙasashen ƙetare sun nemi suji wai wanna irin karatu sheikh Abduljabbar kabara nan yake yi da har ya jawo mai wannan matsalar ta cin zarafin Annabi kamar da ake yaɗawa ,
duk wanda ya saurari karatun nasa daga kan (Rayuwa Bayan mutuwa) zuwa kan (Jauful Farah) ko majalisi 1 ne mutum ya saurara zai fahimci inda shehin malamin yasa gaba
Ɗaɗin da nake ji yanxu shine da yawa daga mutane sun fahimci da'awar sa itace (kore hadisan ƙarya) da tabbatar dana gaskia da tsarkake Annabi Muhammad SAW daga Dukkan wata kwamacalar ruwayar da zata raɓa masa rashin daraja ko kamala
Naji daɗi da mutane suke fahimtar haƙiƙanin saƙon koda kuwa zasuce yana hakan ne bisa jahilci yafi ace suna kan fahimtar cewa yayi ɓatanci ga Annabi da alamu sun fahimci da'awar,
ina masu ilimin su futo suyi nasu bisa ilimin sai jama'a su tantance Kai bakayi ba sannan kasan hadisan nan dasu amma ka kame hannun ka wanda kuma yakeyi kace bisa jahilci yake yi kai kuma kaƙi kayi in har dan Allah ake addinin nan to afuto tunda anyi imani da akwai hadisan wanda bana Annabin bane bai san su ba bai san dasu ba to afuto a cire su dan kwanciyar hankalin masoya Annabi 💖
wasu sunce hadisan ma Isra'iliyat ne to koma dai mene yanxu hadisan ba'a littafin Isra'iliyat ɗin muka gan su ba cikin namu littafan ne
in kuma bazaku iya ba to fa wajibin ku ku bar me yayi inyaso inyayi bisa jahilcin ku kuma saiku gyara masa bisa ilimi tunda ku kune maluman jarhi a wannan lokaci da ta'adili
Sheikh Abduljabbar baida masoyin daya kai Annabi cikin zuciyar sa bare ya fishi kishin sa da ƙaunar sa gare shi tasa shi fara wannan aiki kuma ko yau ya mutu wallahi wannan da'awar bazata mutu ba
su kuma ( maluman maja ) kishin su ga wannan littafan da akace cikin su akwai hadisan bogi da kishin su ga maruwaitan da suka assassa wannan hadisi hartafi kishin da sukewa Annabi saw ,
tasa suke ganin bai kamata a koda akwai hadisan bogi ciki ace an cire su hakan na nuna gazawar maluman da suka gabata ne ,
su gurin a hakura acigaba da raɓawa Annabi duk abin da yazo da sunan hadisi batare da aiki da hankali ba ko tunani
Na zaɓi inci gaba da bin Sheikh Abduljabbar Kabara dan kare Annabi Muhammad SAW da tsarkake shi Allah yasan zucciyar kowa da abin da take nufi
Allah ka ka bamu iklasi 🙏
©Fatimiyyaa
Comments
Post a Comment