IZALAH ZASU FADI MATSAYAR SU KAN MAKOMAR IYAYEN ANNABI
Kungiyar Izalah Zata Fadi Raayinta Game Da Fatawar Jalo Jalingo akan Hadisin Anas Dan Malik Na Cikin Littafin Imam Muslim Mai Lamba 203 Wanda Yake Cewa:
حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ ، حَدَّثَنَا عَفَّانُ ، حَدَّثَنَا حَمَّادُ بْنُ سَلَمَةَ ، عَنْ ثَابِتٍ ، عَنْ أَنَسٍ ، أَنَّ رَجُلًا قَالَ : يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَيْنَ أَبِي ؟ قَالَ : " فِي النَّارِ ". فَلَمَّا قَفَّى دَعَاهُ، فَقَالَ إِنَّ أَبِي وَأَبَاكَ فِي النَّارِ ".
Ga Fassarar Hadisin:
Sahabi Anas Dan Malik Ya ce Wani Mutum Ya Tambayi Annabi {S.a.w} Cewa Ina Baba Na Yake? Sai Annabi {S.a.w} Ya ce Yana Wuta. Yayin Da Wannan Mutum Ya Juya Wai Sai Annabi {S.a.w} Ya Kira shi Ya ce Masa Da Baba na Da Babanka Suna Wuta.
Kungiyar Da Yanzu Haka Tana Nan Tana Gudanar Da Zama Akan Lamarin Inda a Bayan Kammalawa Kungiyar Zata Fadi Matsayarsu akan Sheikh Jalo Jalingo Da Hadisin Na Iyayen Annabi.
Ina Da Tabbas Dole Ayi Daya Cikin Abu Biyun Nan:
Kodai a Karya ta Hadisin Kenan a Koma Kan Fatawar Sheikh Abduljabbar Kabara ta Fitar Da Duk Wani Hadisi Da Ya Taba Mutunci Da Martabar Annabi
Ko Kuma a Tabbatar Da Hadisin Kenan a Tabbatar Da Mahaifan Annabi Suna Wuta {Waiyyazubillah}
Ga jawaban akasa
Comments
Post a Comment