MALAMAI SUCIRE TSORO SUYI ABINDA YADACE!

 Daga wani bawan Allah Dan Kahfi


MALAMAI KU CIRE TSORO DA MUNAFUNCI KUYI ABUNDA YA DACE.


Malamai masu zagi da la'antar Jalo jalingo saboda ya karanta Abunda ke cikin littattafan su ku cire tsoro da munafunci kuyi abunda ya dace, domin a zahirin gaskiya jalo jalingo bashi da wani lefi ya ruɗu ne da abunda kuka dora duniya na duk wanda akace sahabi ne to adali ne bazai iya karya ba bazai iya fadar son zuciyar sa ba.


shine kiran da malam Abduljabbar kabara (H) yake tayi gareku daku canja wannan tunani ku fahimci cewa akwai da yawa waɗanda aka ce sahabbai ne Amma suna cikin sahabban da Annabi yace iyakar sa dasu duniya a lahira bashi basu saboda cutar dashi kawai sukai sune dai waɗanda suka karkashe ya'yansa suka kuma kirkiri riwayoyi suka ɓata shi suka kuma kafirta Iyayen sa amma kukai kunan uwar shegu.


Daga cikin waɗannan sahabban da Amirul wa'izina yake ta cewa kubi a hankali magauta ne na Annabi ba masoyansa ba har da wanda ya rawaici mahaifin Annabi na wuta(wa'iyazibillahi)


Idan a yanzu kun yarda makaryacine to ga irin riwayoyin sa da malam Abduljabbar yake yaki dasu waɗanda suka taɓa Annabi (S.A.W) kuma shi kaɗai ya kaɗaita dasu misali:


1-Dr.Abduljabbar kabara Amirul wa'izina ya kawo hadisi na 2205 cikin musnad na Ahamad bn hambali 


عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " قَالَ لِي جِبْرِيلُ عَلَيْهِ السَّلَامُ إِنَّهُ قَدْ حُبِّبَ إِلَيْكَ الصَّلَاةُ، فَخُذْ مِنْهَا مَا شِئْتَ)


Daga kanin manzan Allah (S.A.W) Abdullahi ibn Abbas (R.A) yace manzan Allah (S.A.W) yace: Mala'ika jibrilu yace masa: (hakika An soyar da sallah a ranka ka dage da yinta)


Sai marawaicin wancen hadisin na baban Annabi na wuta ya juya shi yace Annabi yace wai: Abunda yafi so A duniya mata da turare an sanya sanyin idaniyar sa a cikin sallah.


Duba musnad ɗin hadisi mai lamba 14037 

عَنْ أَنَسٍ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " حُبِّبَ إِلَيَّ مِنَ الدُّنْيَا النِّسَاءُ وَالطِّيبُ، وَجُعِلَتْ قُرَّةُ عَيْنِي فِي الصَّلَاةِ ".


2-Amirul wa'izina ya kawo hadisi na mafarkin mu'ujiza da Ma'aikin Allah (A.S) yayi wanda a cikin mafarkin Allah ya nuna masa wasu daga Al'ummar sa da za su haura kogi suyi yaƙi dan ɗaukaka kalmar Allah ya fadi alkairi masu yawa akan su.


Wannan hadisin an rawaice shine shima takan kanin manzan Allah S.A.W Abdullahi ibn Abbas (R.A) ya kuma ce baccin nan da Annabi S.A.W yayi har yayi wannan mafarkin a cikinsa a ɗakin ɗaya daga iyayen muminai ne matan sa (S.A.W) in ka duba lamba ta 2722 cikin musnad za ka gani.

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ ، قَالَ : بَيْنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي بَيْتِ بَعْضِ نِسَائِهِ، إِذْ وَضَعَ رَأْسَهُ فَنَامَ، فَضَحِكَ فِي مَنَامِهِ، فَلَمَّا اسْتَيْقَظَ قَالَتْ لَهُ امْرَأَةٌ مِنْ نِسَائِهِ : لَقَدْ ضَحِكْتَ فِي مَنَامِكَ، فَمَا أَضْحَكَكَ ؟ قَالَ : " أَعْجَبُ مِنْ نَاسٍ مِنْ أُمَّتِي يَرْكَبُونَ هَذَا الْبَحْرَ هَوْلَ الْعَدُوِّ، يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ ". فَذَكَرَ لَهُمْ خَيْرًا كَثِيرًا.


Sai wancen dai marawaicin na hadisin mahaifin Annabi na wuta(wa'iyazibillahi) ya ɗauki shima wannan hadisin sai yace ai baccin a gidan matar wani sahabi wai ita ummu haram ma'aikin Allah yayi kuma a jikinta Annabi (S.A.W) ma yayi baccin bayan ta bashi abinci yaci tana kama masa Kwarkwata (wa'iyazibillahi) shine baccin ya ɗauke shi har yayi wannan mafarkin.


Idan ka duba bukhari 7001,7002 da ragowar litattafan hadisi za kaga riwayar:


عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي طَلْحَةَ ، أَنَّهُ سَمِعَ أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ يَقُولُ : كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْخُلُ عَلَى أُمِّ حَرَامٍ بِنْتِ مِلْحَانَ، وَكَانَتْ تَحْتَ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ، فَدَخَلَ عَلَيْهَا يَوْمًا فَأَطْعَمَتْهُ، وَجَعَلَتْ تَفْلِي رَأْسَهُ، فَنَامَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، ثُمَّ اسْتَيْقَظَ وَهُوَ يَضْحَكُ.

7002 قَالَتْ : فَقُلْتُ : مَا يُضْحِكُكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ ؟ قَالَ : " نَاسٌ مِنْ أُمَّتِي عُرِضُوا عَلَيَّ غُزَاةً فِي سَبِيلِ اللَّهِ، يَرْكَبُونَ ثَبَجَ هَذَا الْبَحْرِ مُلُوكًا عَلَى الْأَسِرَّةِ ". أَوْ : " مِثْلَ الْمُلُوكِ عَلَى الْأَسِرَّةِ ". شَكَّ إِسْحَاقُ. قَالَتْ : فَقُلْتُ : يَا رَسُولَ اللَّهِ، ادْعُ اللَّهَ أَنْ يَجْعَلَنِي مِنْهُمْ. فَدَعَا لَهَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، ثُمَّ وَضَعَ رَأْسَهُ، ثُمَّ اسْتَيْقَظَ وَهُوَ يَضْحَكُ، فَقُلْتُ : مَا يُضْحِكُكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ ؟ قَالَ : " نَاسٌ مِنْ أُمَّتِي عُرِضُوا عَلَيَّ غُزَاةً فِي سَبِيلِ اللَّهِ ". كَمَا قَالَ فِي الْأُولَى، قَالَتْ : فَقُلْتُ : يَا رَسُولَ اللَّهِ، ادْعُ اللَّهَ أَنْ يَجْعَلَنِي مِنْهُمْ. قَالَ : " أَنْتِ مِنَ الْأَوَّلِينَ ". فَرَكِبَتِ الْبَحْرَ فِي زَمَانِ مُعَاوِيَةَ بْنِ أَبِي سُفْيَانَ، فَصُرِعَتْ عَنْ دَابَّتِهَا حِينَ خَرَجَتْ مِنَ الْبَحْرِ، فَهَلَكَتْ.


Kuma abun takaici a wajen malaman hadisi na wannan marawaicin da yace mahaifin Annabi na wuta(wa'iyazibillahi) sune ingantattu na ibn Abbas kanin Annabi (S.A.W) basu inganta ba.


To amma yanzu tunda hankalin duniya da malamai ya karkato kamar suna son gyaran daga jin yarda kowane ɓangare yake ta kururuwar tsinuwa da la'antar Jalo jalingo dan a shekarun baya idan aka samu wani fajiri yayi irin wannan maganar da jalo jalingo yayi Malam Abduljabbar shi kaɗai ake jin muryar sa yana fada da wanda yayi ɗin.


Kuma abun farin-cikin yadda kowane ɓangaren daga izalar zuwa sufayen da suke tayiwa jalo raddi basu tsallake bahasin da malam Abduljabbar yayi akan hadisin ba a shekarun bayan dan shima da tuhumar sa iya kan Hamadu ta tsaya hakana hujjar sa ta tsayane iya kan karon da hadisin yayi da ayoyin Qur'ani amma yanzu sakamakon faɗaɗa bincike ya koma yana tuhumar ainihin wanda akace ya faɗi maganar wato Anasu bin malik saboda kaɗaitarsa da irin waɗannan riwayoyi dake taɓa alfarmar Annabi (S.A.W).


kuma Yanzu bincike ya tabbatarwa da shehin Malamin kwata-kwata ma Annabi (S.A.W) bai ma san shi Anas ɗin ba maganar hidimar da aka ce yayiwa Annabi ta shekara 10 tatsuniya ce ba gaskiya ba kuma har yau bamu ji malamai sun tabbatar da Annabin yasan shin ba bare kuma hidimar da aka ce yayi masa.


Yanzu abunda ya rage shine malamai kuji tsoran Allah ku koma bincike idan gaskiya malam Abduljabbar yake ku fito ku fadawa duniya ku kuma taimaka masa ya cigaba da wannan bincike dan raba musulunci da hadisan da suka zame masa matsala irin waɗanda suka koyar da ta'addanci kamar irin hadisan shi dai wannan marawaicin wanda yake cewa idan Annabi yaje wani gari kasa kune yake yaji idan baiji kiran sallah ba afka musu kawai yake da yaki wanda bukhari ya rawaita a lamba ta 610.


Kunga irin su yanzu suna koyar da ta'addanci da halarta kawai in kaje gari baka ji kiran sallah ba zaka iya yakar su.


Allah ka kara nuna mana gaskiya gaskiya ce ka bamu ikon karɓarta ka nuna mana karya karyace ka bamu ikon guje mata.


Prince Hafiz Yusuf Abdulhamid 

01/01/2022


©Fatimiyyaa

Comments