NAFISA ABDULLAHI TA BAYYANA DALILIN FICEWARTA DAGA CIKIN SHIRIN LABARINA


 NAFISA ABDULLAHI (SUMAYYA) TA SANAR DA FICEWARTA A CIKIN SHIRIN LABARINA:-


Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Nafisat Abdullahi wacce aka fi sani da Sumayya a cikin shirin Labarina mai dogon zango wanda kamfanin Saira Movies ya ke shiryawa a yau ta sanar da ficewarta daga cikin shirin gabaɗaya.


Jarumar ta sanar da hakan ne a cikin shafinta na Facebook a wannan dare, inda ta bayyana dalilin ficewar tata kan ƙarancin lokaci saboda karatu da ta ke yi da kuma sabon shirin kamfaninta da ta ke shirin fara ɗauka kwanan nan.


Masu kallo dai sun daɗe su na ganin take-taken Daraktan Fim ɗin kan fitar da Jarumar cikin shirin tun ma kafin ta bayyana ficewar tata a yau la'akari da yadda ya ce an yi garkuwa da ita da kuma yadda ya nuna bom ya tashi da ita fuskarta ta samu matsala a wannan makon.


Sai dai mutane da dama masu bibiyar shirin na ganin rashin asalin jarumar da ta fito a matsayin Sumayya, wato Nafisat Abdullahi cikin shirin zai iya haifarwa da fim ɗin koma baya, duba da yadda jarumar ta goge wajen nuna akting ɗin fim kamar gaske.


-Kamila Magazine.




Comments