Yau ne zaman kotu 6/1/2022
MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A KOTU YAU.
1-Shaida na 4 ya koma kotu kuma sheikh Abduljabbar yayi masa tambayoyi.
Sheikh Abduljabbar yayi tambayoyi har sama da (40) ga farfesa Ahamad murtala na jami'ar bayero bayan ya gabatarwa da kotu shaidun karatun sa.
Sheikh Abduljabbar masa tambayoyi masu tarin yawa sai dai abun mamakin yadda farfesa ya fassara فخذ da kafa ya kuma kafe akan wannan fassarar duk da ankarar dashi da Dr Abduljabbar kabara yayi.
Ya fassara فخذ da kafa ne a kokarin sa na fassara maganar anas da yace a hanyarsu ta zuwa kaibar da ma'aikin Allah (A.S) gwiwarsa tana taɓa cinyar shugaba (S.A.W) inda yace sai dai a fassara(وَإِنَّ رُكْبَتِي لَتَمَسُّ فَخِذَ نَبِيِّ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ) da gwiwar Anas tana taɓa kafar Annabi baza ace cinya ba sai dai ya gaza bada hujja akan wannan fassara tasa
A kokarin farfesa na halartawa shugaba S.A.W karɓar da Anas yace yayiwa safiya daga Dihiya ya kawo ayar da tai magana akan fai'u maimakon ganima.
Sai dai malam ya tambayeshi mai yasa yayi hakan sai yace yana so isar da malam zuwa ga ma'anar da yake son zuwa gareta sai dai malam yace ai yadda Allah yayi bayani akan fai'u haka yayi akan ganima mai ya hanashi kawo ayar da tai magana akan ganimar sai farfesa yace idan ya kawota bayaninta nada faɗi.
malam ya kawo masa hadisai da ayoyin kur'ani da suka haramta kayi kyauta kace a dawo maka da ita kamar yadda Anas yace Annabi yayiwa Dihiya ya bashi safiya bayan an bashi labarin kyanta yace ya dawo masa da ita.
Sai dai farfesa yace hakan kususiya ce ta Annabi yayi duk yadda yake so a cikin ganima.
Sannan maganar sanya Yancin nana Safiya a matsayin sadakinta shima yace kusisiyace inda ya kafa hujja da wani littafi sharhin muktasar inda malami yace yayi dingushe a littafin akwai gabar da bai karanta ba kafin wannan bayani nasa shin a cikin littafin a wannnan gabar babu batun cewa yana daga kususiyar Annabi yayi aure babu sadaki babu shaida da waliyi kuma ko da yardar macen ko babu yardar ta?
Sai farfesa ya kada baki yace ai ba littafin kaga na bude ba misali nake bayar wa, take malamin yace akwai gabar ko babu? Anan farfesa ya tabbatar akwai amma batun auren nana Safiya kususiyar Annabi ce.
Take malam yayi masa tambayar ya kawo masa Aya ɗaya tak ko wani hadisi da yace an halattawa Annabi haram da sunan kususiya anan ma dai farfesa ya gaza kawo wa inda yace malamai ne suke sanya duk wani abu daya saɓa da shari'ar da Annabi Ya dora jama'a akai da aka jingina masa a matsayin kususiyar sa kamar auren mace sama da 4.
Malam ya tambayeshi baka ganin akwai karo tsakanin wannan riwaya ta Anas da ta Nana Aisha da muslim ya rawaita da tace Annabi (S.A.W) ya bawa duk matansa sadaki, farfesa yace shi baiga karo ba malam ya shiga gabatar da masa bayanin karon Alqali ya dakatar dashi yace ya bari sai yazo kare kai yayiwa alqali bayanin karon dake ciki.
Da dai sauran tattaunawa masu kyau da suka gudana tsakanin malam da shaida farfesa.
2- daya daga wakilan yan maja masu sa ido ta fashe da kuka ana tsaka da tattaunawa tsakanin shaida da malam:
Bayan shaida ya tabbatar da cewa malamai suna kan fahimtar Annabi zai iya aure ba tare da sadaki,shaidu,waliyi da yardar mace da yardar iyayen ta ba amatsayin kususiyar sa.
Malam Abduljabbar ya tambayeshi in na fahimceka kana so kacemun suma malaman abunda na fahimta shi suka fahimta banbanci na dasu su suna kallon hakan a matsayin kususiya ni ina korewa ina Annabi ma bazai aikata hakan ba?
Anan farfesa dai ya gaza amsa wannan tambaya take malam yace Allah gafarta malam ko kasan malaman sira ciki harda ibn kayyum dalibin ibn taimiyya sun kawo sigar kwanciyar da akace ma'aikin Allah yayi da Nana Safiya.
Anan malam ya kawo masa riwayar ɗabari da aka rawaito wai Abu dalha cikin dare yana ta kewaya tantin da wai Annabi yake amarci da Nana Safiyya sai Annabi ya fito yace mai yasa baije ya kwanta ba sai yace ya rasulullahi ka kashe mata uba ka kashe mata ɗan uwan mahaifinta ka kashe mata ɗan uwan ta ka kashe mata miji tana amarci yanzu gashi kana amarci da ita ina tsoran abunda bayawudiyar zatai maka...
Anan baiwar allah nan ta saka kuka...
3-lauyoyin gwamnati sun tsaya da kawo shaidu:
Idan baku manta ba a kwanakin baya lauyoyin gwamnati sun ce zasu gabatar da shaidu goma ko sama da haka amma a zaman na yau sunce bazasu cigaba da gabatar da wadannan shaidu ba sun tsaya a haka a bawa malam damar kare kansa.
4- an dage zaman zuwa sati 4 maimakon 2:
A maimakon sati 2 alqali sarki yola ya dage zaman zuwa sati 4 dan malam ya samu cikakken lokacin bitar abubuwan da suka gudana a kotu dan ya shiga kare kansa.
Wadannan da wasu muhimman Abubuwan da suka faru yau a kotu.
Muna rokon Allah ya kara bawa malam kariya ya kuma kara taimakon gaskiya ya karya ƙarya
AKNM
6/01/2022
Ga wani rahoton Daga Shafin JARIDA RADIO👇
Comments
Post a Comment