SHARHI AKAN ZAMAN KOTU NA 06/01/2022


 POST:NO:1083


SHARHI AKAN ZAMAN KOTU NA 06-01-2022


Kamar Da Nai Bayani A Zaman Baya Na Cewa Da Bazan Yi Sharhi Ba A Zaman Da Ya Gabata Ɗin, Saboda Zaman Ya Taƙaita ne Ga Bayanan Sheda, Ma'ana Iya Sheda Ne Yayi Magana Lokaci Bai Bawa Malam Damar Yayi Masa Tambayoyi Da Suka Ba, Wannan Zama Kuma Malam Ya Samu Damar Yin Tambayoyi Masu Tarin Yawa Ga Sheda Farfesa Ahmad (Kususiya) Wannan Sunan Na Bashi Ne Kyauta Duba Da Yanda Ya Bayyana Mana Ma'anar Kususiya A Zaman Satin Nan, ( Bawai Sunansa Bane Da Maluman Hadisai Suka Bashi Ba) Wannan Kenan. 


Wato Ya Zama Wajibi Mu Godewa Allah Bisa Ni'imar Da Ya Bamu, Ta Hangen Abun Nesa A Kusa, Duk Da Dama Mu A Kusa Damu Yake Tuni, Wasu Ne Suke Ganinsa A Nesa, Ina Nufin Batu Kan Tabbaci Da Muke Dashi Kuma Muka Faɗa A Baya,  Kan Kwasar Kashin Da Sheda Zaiyi Da Hannunsa A Gaban Maulana Amerul Waizina Shekh Abduljabbar (H) Yan Kusa Da Ƴan Nesa Duka Sun Gani, Wanda Na Tabbata Wasu Sun Ɗauka Cika Baki Ne Kawai, To Amma Sai Allah Cikin Ikonsa Ya Tabbatarwa Duniya Yanda Karatu Ya Sha Bambam Da Shedar Karatu. ( Wacce Farfesa Kususiya Ya Zo Wa Kotu Dasu) 


Idan Muka Koma Kan Batun Karɓar Sheda Ko Korasa, Wanda Da ma Shine Muke Sharhi Akai Ta Hanyar Tambayoyin Da Malam Yayiwa Sheda Da Kuma Amsar Da Ya Bayar, Zamu Ga Babu Shakka Wannan Shedar Korarre Ne, Ba Ta Yanda Alƙali Zai Karɓi Shedarsa, Domin Ya Tabbatar Wa Kotu Maulana Amerul Waizina Kare Mutuncin Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Yake Akasin Abunda Aka Turo Shi Yayi, Zamu Ƙara Gane Hakan Idan Mukai Nazari Kan Nuƙuɗoɗi Biyu Da Aka Tattauna A Zaman Kamar Haka


1- Yanda Sheda Yake Ƙoƙarin Murɗe Fassarar Kalmar Da Sahabi Anas Ɗan Malik Yai Amfani Da Ita Lokacin Da Zai Nuna Kusancinsa Da Annabi S.a.w Lokacin Da Suke Kan Dabba, Kalmar فخذ Sai Sheda Ya Tubure A Lalle Ba Cinya Za A Ce Ba, Saboda Idan Akace Gwiwar Anas Tana Shafar Cinyar Annabi S.a.w Akwai Taɓa Mutuncin Shugaba S.a.w A Gurin, To Anan Sheda Ya Nuna Kwarai Akwai Kalaman Nan Na Taɓa Mutuncin Annabi S.a.w, Amma Ana Canza Fassara Ko A Murguɗeta Domin A Kare Wannan Mutuncin Na Annabin Rahama. To Kunga Ashe Anan Idan Alƙali Yayi Duba Na Tsanake Zai Gane Lalle Kalaman Nan Akwai Su Sai Dai Kawai An Samu Banbancin Kore Su Tsakanin Malam (H) Da Kuma Maluman Hadisi.


Banbancin Shine Su Malaman Hadisi Suna Murguɗe Fassarar ne Domin Kar Mutuncin Wasu Manya Ya Taɓu Idan Aka Tabbatar Da Fassarar, Sannan Kuma Kar Mutuncin Annabin S.a.w Shima Ya Taɓu, Shi Kuma Maulana Amerul Waizina Yana Kore Gaba Ɗaya Hadisin Ne Domin Kare Martabar Annabi S.a.w, Kenan An Haɗu A Manufa Ɗaya An Babbanta A Hanya, To Anan Muddin Alƙalin Zaiyi Duba Na Tsanake Irin Na Alƙalai Dole Ya Kuri Shedar Farfesa Kususiya  


2- Raɓuwa Da Kususiya Wajen Kare Annabi S.a.w, Wanda Shima Za Muga Kamar Dai Na Farko ne, Nan Ma Sheda Ya Nuna Tabbas Akwai Abubuwan Taɓa Mutuncin Annabin Rahama A Hadisan Nan Da Malam (H) Yake Ta Magana Akwai, Sai dai Kamar Yanda Na Faɗa Ne, Su Maluman Hadisi Suna Ganin Idan Aka Fito Aka Ƙaryata Hadisan To An Taɓa Magabata Domin Za'a Danganta Musu Ƙarya Da Ƙage, Dan Haka Sai Suke Amfani Da Kalmar Kususiya, Sai Suce Wannan Abun Da Annabi S.a.w Yayi Kususiyarsa Ce, 


Dan Haka Sai Sheda Farfesa Kususiya, Yai Amfani da Wannan Domin Kare Kansa Kan Maganar Annabi S.a.w Yayi Aure Ba Sadaki Ba Wali Ba Kuma Yardar Amarya, Da Aka Nemi Ya Kawo Sheda Inda Allah Ya Halartawa Annabi Haka Sai Yace Ai Kususiyarsa Ce, Wato Ya Fuskanta Lalle Wannan Saɓawa Shari'a Ne Dan Haka Sai Ya Raɓe Da Abunda Su Maluman Hadisan Suke Raɓewa (Kususiya) To Anan Ma Idan Mukai Duba Na Tsanake Wanda Nake Fatan Shima Alƙali Zai Yi Shi, Za Muga Batun Shedar Farfesa Kususiya Ba Zata Tabbata Ba Domin Ya Kasa Tabbatarwa Maulana Amerul Waizina Taɓa Mutuncin Annabi S.a.w Yake, Sai Dai Ya Nuna Kamar Da Na Farko ne Hanyar Kare martabar Annabin Ce Ta Banbanta, (Su Zasu Kare Annabi Da Cewa Kususiyarsa Ce Shi Kuma Zai Kare Annabi Da Gaba Ɗaya Hadisin Karya ne)


A Dunƙule Zamu Faskanci Ko Nace Alƙali Zai Fuskanci:

Hadisan Nan Kawai Taɓa Mutuncin Annabi Sai Dai Maluma Suna Bin Hanya Biyu Ne Wajen Kore Taɓa Mutuncin,

 1- Canza/Murguɗe Fassarar Su 

2- Raɓa Su Ga Kususiya 

Shi Kuma Malam (H) Yana Kare Mutuncin Annabi Ta Hanyar Kore Hadisan Gaɓa Daya, 

Dan Haka Anan Ala Dole Alƙali Ya Kori Shedar Farfesa Kususiya Domin Ya Gaza Tabbatar Da Abinda Yake Sheda Akai. 


Idan Kuma Muka Waiga Ga Abun Da Ke Iya Faruwa A Zaman Gaba Zamu Ga Tabbas Muddin Za'a Nufi Allah Ayi Adalci, Za'a Saki Malam Ne Domin An Gaza Tabbatar Da Abunda Ake Zarginsa Akai, Ko Da Kuwa Bai Kare Kansa Ba, Domin Shedu Sun Kasa Tabbatarwa, A Ka'idar Shari'a Kuwa Duk Sanda Ake Zargin Ka Da Aikata Aka Kawo Shedu Suka Kasa Tabbatarwa To Sakinka Za'ayi Kuma A Biyaka Bata Maka Suna Da Akai, Sai Dai Batun Kare Kai Ɗin Shima Wata Dama ce Da Zata Ƙara Tabbatar wa Da Duniya Waye Maulana Amerul Waizina (H) Za'a Gane Tabbas Jagoran Kare Martabar Sayyidina Rasulillahi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Ne, Kuma Idan Nace Ranar Za'a Karanta Jauful Fara Na 146 Banyi Ƙarya Ba, Allah Dai Ya Nuna Mana Kawai


A Kiyaye: 

Bawai Nace Zama Na Gaba Za'a Saki Malam Bane, A'a Ita Shari'a Ba Ƴar Gaggawa Bace, Bi Ake A Sannu A Sannu Har Gaskiya Tai Halinta, Bari Ma Ina Jin Na Taɓa Fade Ni Kallon Ibada Nakewa Malam Yake Yi A Kurkuku Bawai Tsare Yake Ba, Kallon Ɗaukaka Nake Wa Malam A Kurkuku Bawai Kaskanci Ba, Kallon Daraja Nake Wa Malam A Kurkuku Bawai Tozarci Ba, Malam Ibada Yake Bari Na Sa Babban Baƙi Na Faɗa MALAM IBADA YAKE A Kurkuku IBADAR Allah Ta'ala 


Allah Ya Kare Malam Daga Sharrin Masu Sharri Ya Bashi Nasara Akan Makiyansa, Ya Gaggauta Bashi Yanci Albarkar Sayyidina Rasulillahi Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam

Allahumma Amen 🌹 


©️ Jawad Salisu Umar

Attaqiy Alganawiy

8-1-2022

Comments