TAGWAYEN DA AKA HAIFESU A SHEKARU DABAN DABAN.


 Tagwaye da aka haife su a shekaru daban daban daya cikin 2021 daya kuma cikin 2022 A Kasar Amurka

__________


Wani abun al'ajabi ya faru a Asibitin Salinas, jihar California. Kasar Amurka 


Wata uwa ta haifi  wasu ƴan biyu a shekara daban-daban a Amurka, a shekarar 2021 da kuma 2022.


Minti 15 ne tsakanin haihuwar tagwayen wanda ya raba shekarunsu. Da kuma watannin haihuwar su. 


An fara haihuwar namiji a 2021, bayan minti 15, kuma bayan shiga sabuwar shekara aka haifi mace a 2022.


Asibitin Navidad da aka haifi jaririnan ne ya sanar da al'amarin a shafin sa na Twitter wanda ba a saba gani ba.


Hakan na nufin an samu banbamcin rana da wata da kuma shekara a takardar shedar haihuwarsu. Kamar yadda asibitin ya fitar da takardar haihuwar su. 


Ko kun taba cin karo da irin wannan labarin a yankin ku?


Comments