Cikekken Abinda yafaru A kotu 17/2/2022


 CIKAKKEN BAYANIN YADDA TA KASANCE A KOTUN MAI SHARI'A SARKI YOLA, A YAU ALHAMIS 17/02/2022, CIKIN SHARI'AR MALAM ABDULJABBAR DA GWNATIN JAHAR KANO.


Bayan ɓangaren Gwamnati sun gabatar da lauyoyinsu, sai alƙali ya juya ga lauyan M. Abduljabbar don suma su gabatarwa da kotu kansu, inda a nan ɗaya daga cikinsu ya tashi ya nemi alfarmar kotu kan ta ƙara musu minti biyar sakamakon tashin isowar wanda yake jagorantarsu lauya mai muƙamin SAN wato A.O MUHD.


Take alƙali ya basu minti goma domin samun isasshen lokaci. Bayan da lokacin ya cika Lauya bai ƙaraso bane aka fara Shari'a kai tsaye daga inda aka tsaya.


Alƙali ya juya ga lauyan Gwamnati da cewa ko shaidarku na farko mai suna Adamu Adamu ya zo ?


Lauyan Gwamnati ya amsa da eh ya zo.


Ana cikin haka sai ga lauyan wanda yake kare wanda ake ƙara nan ya shigo tare da nuna takaicinsa na hana shi shigowa da jami'an ƴan sanda suka yi, bisa dalilin umarni da aka basu cewa bayan an fito da malam kada wanda suka bari ya shigo. Shi kuma ya bayyanawa kotu cewa shifa lauya ne mai muƙamin SAN kuma a na ƙasa Najeriya, don haka bai ga dalilin da zai sa a yi masa haka ba. A nan dai alƙali ya taushe shi tare da bayyana cewar shi ba shi ne ya sa a yi masa haka ba, kuma bai san da wannan umarni ba.


Shari'a ta ɗora da cewar alƙali ga lauyan wanda yake kare M. Abduljabbar, to ga shaida na farko nan yana tsaye sai a yi masa tambayar da ake so a yi masa musamman wacce ta dace.


M.Abduljabbar : Ranar 14/10/2021 a yayin da kake bayar da shaida ka ce a bisa taƙaitawa ka karanta litattafai 40 a cikin fannoni guda uku 20 a fannin Hadisi, 10 a fannin fiƙhu haka kuma 10 a fannin Tauhidi. To idan ba bisa taƙaitawa ba zasu kai nawa litattafan da ka karanta ?


Shaida : Ni wannan baya cikin abinda kotu ta kira Ni ta yi min tambaya a kansa, wannan tunani na ne Ni ya shafa.


Malam : idan haka ne me  yasa da lauya ya yi maka tambayar matakin karatunka a ranar ka bashi amsa ?


Shaida : na bashi ne a wannan lokacin saboda akwai buƙatar hakan


Malam : ko zan iya sanin buƙatar ?


Shaida : dalili shi ne shi lauyan yana da buƙatar sanin hakan 


Malam : ko zan iya sanin sunayen waɗancan litattafai da ka faɗa da kuma wurin malaman da ka karanta su ?


Shaida : babu buƙatar na sanar da kai don ba a kan litattafan ake magana ba, amma a cikinsu akwai Bukhari da Muslim, su kaɗai zan iya faɗa maka.


Malam : ko ka san malaman da suka yi rubututtuka kan shaida da ƙa'idojin bayar da ita sun sharɗanta kewayewa da sanin mas'alar da mai shaida zai bayar ?


Shaida : Eh na sani


Malam : Bukhari da Muslim da ka ce ka karanta ko ka sami tahƙiƙin mas'alolin da nake tattaunawa ?


Shaida : Eh na samu.


Malam : a cikin Bukhari Hadisin da aka rubuta cikin cajin da aka kawo ƙara ta mai lamba 5120 ya nau'anta wannan wannan ruwayar wannan Hadisin da lafuzza mabanbanta waɗanda suka tayar da ƙura a Duniyar kafirai a yau ?


Shaida : Eh ya nau'anta ruwayar Hadisin a wurare guda huɗu, amma babu inda ya tayar da ƙura a wajen wani, sai dai wanda bai fahimci Hadisin ba.


Malam : wurare huɗun su ne wanne da wanne ?


Shaida : a'a sai dai kai ka faɗa mu ji.


Malam : ai kai zaka faɗa


Nan alƙali ya ja hankalin malam ko zai faɗa masa a wuce wurin.


Malam : ai babu buƙatar na faɗa masa tunda shi ya fara maganar a kai.


Nan dai shaida bai faɗa ba.


Malam : to sai dai su masu Aɗraf na Bukhari wuri biyu ya zo ba huɗu ba, to yaya za'a yi kenan da kai da ka ce wuri huɗu ?


Shaida : Ni ban san haka ba sai yanzu na ji a wurinka.


Malam : ka yarda da yadda na faɗa ɗin ko kuwa ?


Shaida : ina buƙata a fara kawo min.


 Take aka bashi ya duba malam kuma ya karanto masa.


Alƙali ya ce a wuce nan malam.


Malam : me ya sa malamai masu takhriji suka rage yawan wuraren ko ka san dalili ?


Shaida : basu rage ba.


Malam : to daga, wuraren da suka rage akwai Hadisi 6072 cikin Bukhari. To shin ka yarda mata suna kama hannun Annabi (s) su tafi da shi inda suka ga dama, kamar yadda ya zo a Bukhari 6072, ka yarda yana yin haka ?


Shaida : ai don mace ta kama hannun Annabi a haƙƙinsa babu komai, domin babu mai zargin Annabi idan ba mara imani ba, domin Allah ya ce Annabi shi ya fi kusanci da muminai a kan kansu.


Malam : dama "AULA"  tana nufin kusaci ?


 Nan alƙali ya ce da malam a wuce nan akwai lokaci da za'a yi min bayani na gamsu sosai.


Malam : to shike nan, ko zai iya faɗa min inda ayar ta ce a kama hannun Annabi ? Ko kuma shima dai a wuce ya kalli alƙali cikin fara'a ?


Alƙali ya ce da dai ya fi saboda akwai lokaci na faɗa maka da zaka yi  bayanai sosai, shi yanzu wannan ya gama abinda zai ya yi tafiyar sa kawai.


Malam : to ba damuwa. Sannan malam ya ci gaba ya ce ka ce ba laifi bane a hakkin Annabi ya yi haka, to ga shi a Bukhari a Hadisi mai lamba 7214 daga Nana A'isha r.a ta ce bai taɓa taɓa hannun wata mace wacce ba mallakinsa ba, to ya zamu yi da wannan ?


Shaida : ai wannan maganar da aka yi a Hadisin ba haka ake nufi ba, sai ka kawo cikakkiyar da ka gutsuro akwai amsar.


Malam : ai ba Ni na gutsuro ba haka Bukhari ya faɗa, kuma ma ya kawo ayar cikakkiya a nan malam ya karanta masa.


Shaida : Ni abinda ayar take magana zancen matan da suka yi mubaya'a ne ba zasu yi zina ba, shi ne Nana ta faɗa cewar Annabi bai taɓa taɓa hannun wata ƴa mace ba, don ta nisanta shi da zinar.


Malam : abin mamaki gareka da baka rabe Massu da Lamsu ba, don Hadisin da na kawo maganar Massu yake yi (taɓawa), ita kuma ayar da kake magana, maganar shafawa take yi .


 A nan alƙali ya yi tsokaci kan taƙaita wannan lamari.


Malam : a cikin Hadisan nan da suke tashin ƙura Bukhari ya rawaici Hadisin ana yiwa Annabi wahayi.... nan ma alƙali tare da taimakon lauyoyi suka bawa malam hakurin a jinkirta wannan magana zuwa zaman da malam zai yi kariya. Malam ya yarda.


Malam : shin cikin al'ƙur'ni ka san akwai ayar da Allah ya ce "ku guji dandali na Gumaka, ku guji shaidar zur, ku bi hanya madaidaiciya kada ku yi shirka" ka san wannan ?


Shaida : ba shi kotu ta nemi na bayar da shaida a kai ba.


Malam : baka Annabi (s) ya alaƙanta wannan aya da abinda ka zo kake yi a nan ba ?


Shaida : Annabi ya alaƙanta ayar da shaidar zur ne, Ni kuma ba ita nake yi ba, ina bayar da shaida ne kan abinda na sani.


Malam : ko zaka iya yi min bayani me ake nufi da shaidar zur ?


Shaida : Ni ba ma'anar shaidar zur na zo faɗa ba.


Malam : baka tunanin wannan amsar taka akwai fatali da faɗin Allah na "kada ka ce uffan a kan abinda baka san haƙiƙarsa ba" ?


Shaida : bata yi fatali ba domin na san ji na da zuciya ta da gani na dukkansu Allah zai tambaye Ni ranar ƙiyama.

Malam : tambayar da lauya ya yi maka kan matakin karatunka na ƙur'ani ranar da ka bayar da shaida ka ce kai mahaddaci ne, to ina so na sani shin baƙin ka haddace ko kuwa baƙin da ma'anarsa ?


Shaida : abinda na haddace ba shi kotu take buƙata ba.


 A nan alƙali da lauyan Gwamnati suka ja hankalin shaida kan cewa duk abinda aka tambaye shi idan ya sani ya faɗa, idan kuma bai sani ba ya faɗawa kotu cewar bai sani ba, domin irin yadda yake bayar da amsar zai iya bashi matsala.


Malam : ciki abinda ka ce ba shi kotu take buƙata ba har da ayoyin da suke da alaƙa da abinda ka zo bayar da shaida kansa ? Kamar auren Nana Safiyya, suma babu ruwanka da su ?


Shaida : idan kotu ta buƙaci na kawo zan kawo.


Malam : daga ayoyin da suke da alaƙa da Hadisin da muke magana a kansa akwai ayoyin idda, kuma a Hadisin babu ita, shin akwai batun idda a alƙur'ani ko babu ?


Shaida : tabbas akwai a cikin ƙur'ani har ma da Hadisin.


Malam : ko zaka nusar da Ni inda iddar ta zo a Hadisin ?


Shaida : ina so ka karanto Hadisin sai na faɗa maka wurin.


Malam : wanne kake so na karanta maka ?


Shaida : kowanne 


Malam : take malam ya karanta Hadisi mai lamba 1375 ciki Bukhari da ya kammala ya ce ina iddar ?


Shaida : to ma ji wannan karanto min wani bayana wannan.


Malam : nan ma malam ya kuma karanto masa wata ruwayar mai lamba 371 cikin Bukhari ya ce to ina iddar ?


Shaida : bai nuna iddar ba, amma sai ya karanto wani Hadisin daban wanda kalmar "Hallat" ta fito ma'ana ta halatta.


Malam : to cikin bayanin ina baiko da ɗaurin aure tunda ta halatta ?


Shaida : a ina aka ce an yi an yi baiko da aure ?


Malam : ai shi ne matsalar dama, rashin ambaton baiko da auren.


Shaida : rashin ambatar su matsala bace domin ba ita kaɗai Annabi ya aura babu baiko da ɗaurin aure ba, misali Nana Zainab bint Jahshi a lokacin da mijinta Zaid ya sake ta, Allah take ya ce ya aurawa Annabi ita.


Malam : ayar da ka kawo ... Nan alƙali ya kuma jan hankalin malam cewa lokaci zai zo da za'a yi bayanai cikakku.


Malam : to shike nan da ka ce babu idda Auren Nana Zainab ya zo a Muslim Hadisi mai lamba 1428 Anas ya rawaito sai da ta yi idda sannan ta yi aure.


Shaida : bai bayar da amsa ba, sai dai ya ce ya yi mamaki da Malam yau kake kafa hujja bayan ka ambace shi tataccen maƙaryaci, shi ya sa ma ban kawo maka shi ba.


Malam : to tunda ka faɗi haka ka bari na tambaye ka mene ne matsayin ya ce Annabi ya tarad da shi a Banɗaki tsirara yana wanka, wai sai Annabi ya tambaye shi wankan me kake yi na janaba ne ko na Juma'a ne ?

 Anas ya ce na janaba ne, wai sai Annabi ya faɗi wasu lugogi masu tsauri cewa ya wawwanke su, sai Anas ɗin ya ce shi bai gane waɗannan lugogi ba, wai sai Annabi ya ce masa matso kusa da Ni, zauna wai sai Annabi yake fassara masa ƙarƙashin muƙamiƙinka habbaika ne, masanaika zagiɗaika, ana nufin tushen cinyoyinka da sauran bayanan Hadisin wal'iyazu billah. 

 Malam ya ce to yanzu kai wanda ya faɗi wannan mene ne matsayinsa wurinka, idan ba'a ce masa maƙaryaci ba ?

 Wannan ya zo cikin Tarikh Dimashƙa na ibn asakhir .


Shaida : to ina so ka faɗa mana Anas yana shekara nawa ya ce a lokacin da aka yi haka ?


Malam : ko ma dai shekara nawa ne, ya ce wankan janaba yake yi ka ga kuwa Shari'a ta hau kansa.


Shaida : Ni a wuri na, wannan ba aibu bane domin Annabi Ɗa ya ɗauki Anas.


Malam : dama ya halatta a yi wa Ɗa haka ?


A nan ma alƙali ya kuma jan hankali malam cewa a sassauta domin akwai lokacin da zaka yi bayanai sosai.


Malam : to mu dawo batun idda, ita idda a al'ƙur'ani iri nawa ce ?


Shaida : Ni ban sani ba.


Malam : ita kuma muddar yin idda a ƙur'ani fa iri nawa ce ?


Shaida : iri uku ce.


Malam : ko zaka kawo min su ?


Shaida : matar da take al'ada da mace mai ciki da kuma wacce bata al'ada.


Malam : akwai ayoyin da suka tabbatar da haka ?


Shaida : akwai a Baƙara da Ɗalaƙ, ya kuma karanto su.


Malam : Ajalahunna da ka faɗa rufu'a ce ko fataha domin wasali yana iya canja ma'ana kacokan.


Shaida : ya gano gyaransa cikin ayar ya kuma ce ya godewa Malam.


Malam : take ya ƙaro masa wasu muddar iddar guda uku a take a wurin cikin ayoyin ƙur'ani suka zama guda shida, a maimakon guda uku da shaida ya ce.


 Malam : ya ɗora da cewa kaf cikin ƙur'ani babu inda ta zo ƙasa tsarki uku, to ta yaya daga sanda aka zo da Nana Safiyya ya ganta kyakkyawa, ya ce mata sadakinki ƴancinki, mai ruwayar ya ce take ya danka ta a hannun babarsa a yi mata shirin amarya.

 A gefe guda ruwayar Zuhair bin Harf ta nuna a hanya aka gama shirinta aka tsayar da rundunar yaƙi ta mutum 16.000 aka kafa tanti ya shiga da ita ciki, bai fito ba sai asuba. Abu ayuba yana ganin fitowarsa sai ya yi kabbara, sai Annabi ya tambaye shi kabbarar me kake yi ?

 Sai ya ce wa Annabi (s) ka kashe mijinta da ɗan uwanta da baffaninta da dukkan danginta ban aminta da ta yi maka kisan gilla, shi ya sa da na ga ka fito na yi kabbara.


 Malam ya ɗora da cewa a ruwayar bin abi shaiba tana cewa a nan Khaibar ɗin aka shirya ta ya kuma tare da ita. To abin tamabaya a nan ina zamu fitar da watanni uku na idda a cikin waɗannan ruwayoyi ?


Shaida : shin har waɗanda aka kama ribattattu suma adadin iddarsu wata uku ne ?


Malam : ƙwarai kuwa har su domin ƙur'ani bai ware kowa ba.


Shaida : ba haka bane 


Malam : to yaya ne ?


Shaida : ƙur'ani ya yi magana ne a kan matan da suke gidajensu, amma akwai Hadisi wanda Annabi (s) dukkan wacce aka kama matsayin ribatacciya, tana yin istibra'i ne kawai kafin ya halatta a aure ta, idan tana da ciki ne kawai to sai bayan ta haihu.


Malam : kuma wannan Hadisi da ka faɗa sanannun malaman Hadisi na Duniya sun yarda da ingancinsa ?


Shaida : ko da basu yarda da ingancinsa ba yana da shawahid (shaidu) tunda aikin Annabi (s) ya tabbatar da su.


Malam : kamar wanne shawahid kenan ?


Shaida : wannan Hadisi da ake magana na auren Nana Safiyya yana ciki kuma malamai sun tabbatar da haka.


Malam : to idan ka ce haka ya zamu yi da ruwayar Abubakar bin Abu shaiba ta 1365 ita wannan ruwayar tana nuna ƙarara, wadda hammadu bin Salama ya ce ina zaton Anas ya ce da Sabitu Safiyya ta yi idda a Gidan Ummu Sulaim, idda ya faɗa ba istibra'i ba.


Shaida : to ai gama jinin shi ne iddar, shi ne abinda malamai suka tabbatar .


Malam : kamar wanne malami kenan ?


Shaida : akwai Baɗɗal, a nan ya kawo wani sharhi, sai dai babu kalmar iddar a ciki.


Malam : to ai Ni kalmar iddar nake nema, da malamin da ya ce istibra'i yana nufin idda.


 A nan kotu ta yi umarni da tafi hutu na minti 20.

Bayan an dawo daga hutu minti 20 malam ya ɗora kamar haka.


Malam : faɗin Muslim Hadisi mai lamba 1365 kalmar ƴancinta sadakinta, ma'anarsa daga baiwa zuwa matar aure kai tsaye.

 To idan haka ne yaya zamu yi da Hadisin da Muslim ya rawaice shi mai lamba 1419 a cikin BABIN WAJABCIN NEMAN IZININ BAZAWARA DA FURUCI NA CEWA TA YARDA WAJIBI NE, ITA KUMA BUDURWA IDAN TA YI SHIRU BATA NUNA RASHIN YARDA BA IZNI NE ko su Imamu malik sun magantu kan wannan.


Shaida : aikin Annabi baya buƙatar amincewar wani ko rashin amincewarsa, don haka wannan kususiyyar Annabi ce.


Malam : da me ka dogara kan wannan magana taka, domin cikin Suratu Hud aya ta 88, "Allah ya lazimtawa Annabi ya fi kowa hanuwa da aiki idan ya hana wasu" haka cikin Suratu a'araf aya ta 157.


Shaida : shin malam ka yarda Annabi yana da keɓantattun abubuwa waɗanda shi kaɗai ya halatta ya aikata ?


Malam : kafin yarda ko rashin yarda ta, a ina kalmar kususiyya ta zo a ƙur'ani ko a Hadisi ?


Shaida : malaman Musulunci su suka tabbatar ba Ni ba.


Malam : kamar wa da wa ?


Shaida : kamar shafi'i da Sa'id bin musayyib da hasanul basarai da ibrhimul naƙa'i da imamuz zuhri da sauransu.


Malam : suka ce yaya ?


Shaida : ya kawo wasu bayanai, amma babu kalmar ko ma'anar kususiyya a ciki.


Malam : a cikin ƙur'anin da ka ce ka haddace a cikin Suratu Rum aya ta 21 " Allah yana lazimta auratayya bisa tushe biyu ku zauna da su zama na soyayya da jin ƙai.

 To a nan ina soyayya da jin ƙai ga yarinya ƴar shekara 17 a ijma'insu wai a ranar ya kashe mijinta da mahaifinta da duk sauran waɗanda suka lissafo kuma a kwanta da ita a ranar.


Shaida : ai jin ƙan ne ya sa Annabi ya aure ta. 


Malam : jin ƙan ne ya sa a Muslim Hadisi mai lamba 1465 ya bayana Annabi ya aure ta ya daina ciyar da ita da shayar da ita da kuma daina kwanciya da ita (wal'iyazu billah).


Shaida : ya nemi a karanta, take kuma malam ya karanta masa.


Shaida : Annabi (s) bai ƙauracewa Nana Safiyya ba, a cikin Hadisin babu inda aka ce ya hana ta ci da sha, abinda kadai ba ya yi shi ne kwanciya da ita, kuma ita ta sarayar da haƙƙinta.

 Domin an rawaito cewa ita Safiyya da kanta ta barwa Nana A'isha kwananta, kuma Annabi bai yadda ba sai da ta tabbatar masa.


Malam : ko zaka faɗa min Hadisin ?


Shaida : ba zan iya kawo shi yanzu ba, amma na tabbata akwai.


Malam : a wurinka mene ne ta'arifin auren dole ?


Shaida : a fahimta ta a auri mace ba da son ranta ba, ta hanyar tilasta mata.


Malam : idan aka auri mace mace aka kwanta da ita ba da son ranta ba, ya sunan wannan kwanciyar.


Shaida : sunanta kwanciya.


Malam : a cikin shaidarka ka ce sharhin da na yiwa Hadisin duk Duniya babu wanda ya yi irinta, yanzu idan na fito maka da irin sharhi na cikin litattafai 23 me zaka ce ?


Shaida : Ni ai cewa na yi kalmomin da ka faɗa babu wanda ya taɓa faɗa sai kai.


Malam : kenan akwai wanda ya yi sharhin, kalmomin ne babu ?


Shaida : Ni ban yarda ba


Malam : kana buƙatar na kawo maka ?


Shaida : har da ya ce malam ya karanto masa, sai kuma ya ce ya janye shi baya buƙata.


Malam : game da maganar kususiyya ko ka san akwai malaman suka faɗa a ƙarƙashin safiyul magnani cewa Annabi ya yi aure ba waliyi ba shaida, sannan ko babu yardar yarinyar da iyayenta, kususiyya ne ?

 Sannan suka ce duk ƴar da Annabi (s) ya gani idan har ya yi sha'awarta, to ta hallata gareshi ko da kuwa matar aure ce ?


Shaida : to ai abinda ka kore shi kake tabbatarwa.


Malam : to ta yaya ?


Shaida : domin na ce Auren Annabi kususiyya ce, kai kuma baka yarda ba.


Malam : ayar da ka kawo AULA BIL MU'UMININA MIN ANFUSIHIM cikin Suratu Ahzab ko ka san Annabi ya fassara ta, kuma fassara ɗaya ya yi mata cikin Bukhari da Muslim wacce ta banbanta da fassarar ?


Shaida : ai wannan ayar bata da alaƙa da wannan abin da ake magana a kai.


Malam : to bata da alaƙa me ya sa ka kawo ta ?


Shaida ya yi shiru.


Malam : ko ka san babu wani littafi da kalmar kususiyya ta zo cikinsa da ya girmi littafin Ma'asa Maɗawi ?


Shaida : kususiyya ƙur'ani shi ya tabbatar da ita ciki Suratu Ahzab, inda ya karanto "khalisatan laka "


Malam : khalisatan daban kususiyya daban. Malam ya ɗora da ko ka san muhallin saɓani na da kususiyya ?


Shaida : a'a ban sani ba.


Malam : Annabi (s) ya haramta kyauta kuma a ƙwace, to an ce sai da aka bayar da ita aka yi hauzi da ita sannan ya ƙwace ta, kuma an rawaito a Muslim Hadisi mai lamba 1622 an rawaici wanda ya yi haka kamar kare ne ya amai ya kuma lashe abinsa, to mene ne laifi na don na korewa Annabi wannan wai da sunan kususiyya ?


Shaida : kai ne ka fahimci cewa kyauta aka yi aka ƙwace, amma malamai ba haka suka ce ba. Annabi ya karɓeta ne saboda masalaha malamai sun ambaci hakan.


Malam : ko zaka faɗa min masalahar ?


Shaida : Eh suhaili ya faɗa wanda ibn hajar ya kawo a cikin fatahul bari, yake cewa hikimar da ta sa Annabi (s) ya ce da Dihya ya dawo masa da ita, haƙiƙa da aka ce da Annabi ta kasance ƴar sarki ce daga cikin sarakunansu, sai Annabi ya ce ba irinta ake bawa mutane irin Dihya ba, saboda yawan iri-irensa daga cikin Sahabbai da waɗanda suka fishi, da kuma ƙarancin ire-iren ita Nana Safiyyan daga ribatattun da aka samo, wannan ya kasance masalaha daga cikin waɗannan sahabbai baki ɗayansu. Annabi (s) ya dawo da ita wurinsa da kuma ribatiwartuwarta gareshi domin shi ya fi cancanta da ita. Domin wannan abu ne dukkan sahabban sun yarda. Hakan ba ya nuni da an yi amai an lashe kamar yadda ka faɗa.


Malam : ga lafazin muna gani sai mu bi wani labari  labarin wani suhaili. Kuma ya zamu yi da ruwayoyin da suka ce sai da Annabi ya yanka yara ɗari uku 3,00 sannan. Da kashe kowa nata har da mijin da amarya ce a wurinsa.

 Ina maganar girmamawa a nan ?


Shaida : ya yi shiru.


Malam : a cikin bayanan da ka bayar da shaida ka ce wai na ce Annabi ya samu wannan mata a kwararo ya biya mata buƙata, kuma mu'amala irin ta Ɗa namiji da Mace. Yanzu da zan ce ka kawo karatun domin a ji na faɗi haka ko ban faɗa zaka kawo ?


Shaida : Eh


Malam : da za'a kawo a ji ya saɓa fa ?

 Nan alƙali ya ce wannan hukunci na ne.


Malam : yanzu a ce ka kawo karatu na da na karanta Hadisi na 5120 a ranar 25/10/2019 zaka iya kawo wa ?


Shaida : Eh


Malam : ka ce na ƙarasa faɗar lafazi na a Hadisi mai lamba 2324 Ni kuma na ce ba a nan na faɗa ba.


Shaida : yadda ka faɗa haka na faɗa.


Malam : yanzu idan an samu karo fa, musamman da abinda aka rubuta a caji fa ?


Shaida shiru : 


Malam : ko ka san fassarar da na yi da kuka ce na ce tana sha'awar annabi, idan ka duba Bukhari Hadisi mai lamba 5234 cewa da Annabi s ya kaɗaita da ita maganar soyayya ya yi mata ?


Shaida : eh ita ma maganar soyayyar ta yi masa cewa ta yi tana ba son sa. Abinda ƴar Anas ta ta faɗa na kaico ko munin abin da ta aikata, ta duba kasancewarta mace ne bai kamata ta ce tana son namiji ba.


A nan malam ya kammala tambayoyi, take alƙali ya juya ga lauyoyin malam ko da sauran wani suka ce babu, haka lauyoyin Gwamnati suma suka ce babu komai, a nan alƙali ya sallami shaida. Tare da faɗin zai faɗin matsayarsa a hukuncin ƙarshe.


Lauyan malam ya yi godiya tare da cewa duk da bamu gamsu wannan shaida ba, amma zamu yi bayani a ciki bayanan kariya.

 

Sannan a ƙarƙashin A C J L 2019 muna da damar shiga kariya kai tsaye ko kuma gabatar da shaida idan da buƙatar hakan.


 Haka kuma ƙarƙashin ƙaramin sashi na 3 A C J L 2019 Wanda ake ƙara zai bayar da jawabi a matsayin shaida, kuma zai iya gabatar da shaidun nuni da ya dogara da su. Don haka muna neman a saka mana wata rana a gaba.


Alƙali ya juya ga lauyan Gwamnati ya ce ka ji abinda ya ce ko zaka ce wani abu ?


Lauyan Gwamnati ya ce bamu da suka.

 

A nan alƙali ya saka ranar 03/03/2022, domin ci gaba da Shari'a.


Daga.....

Ashabulkahfi Social Media Team

           (AKSM TEAM)

        February 17th, 2022

Comments