FASSARAR DAYA DAGA KASIDUN MAULANA SHEIKH ABDULJABBAR
بسم الله الرحمن الرحيم وصلى الله على النبي الكريم وآله ومن ولاهم من الصحب والتابعين وسائر الأمة اجمعين.
أمابعد:-
1. ولائي لآل المصطفى ان يكن عيب*
فيا حبذا والله يا حبذالعيب
Jibintata ga ahalin gidan annabi s.a.w. idan tawayane to madallah da wannan tawaya wallahi madallah da,ita.
2. وإن كان ذنبا فيا ذكري خديجة *
وتفضيلها في البيت ياحبذاالذنب
Idan anbaton nana Khadija da fifikonta acikin matan ma,aiki zunubine to madallah da wannan zunubi.
3. وشوقي للزهراء إن كان بدعة*
فيا نعمها من بدعة مالها توب
Idan nuna begena ga nana fadima bidi, ane agurinku to madallah da wannan bidi,a wadda bazan tubaba har abada.
4. وذكري للكرار إن كان مغضبا*
لسامعه مني فيا حبذا الغضب
Idan ambaton Mai farmakin dabaya juyawa ma,ana ambaton (sayyedina Ali) Yana jawomin fushi daga maijinsa daga gareni to madallah da wannan fushi bansan kanayiba.
5. ومن يك للحسنين حربا فإنني*
أمامهما كبش إذا التظت الحرب
Dukwanda yake ganin zaiyaqi sayyedina Hasan ko sayyedina Hussaini to yasani nine ragon karo agabansu .
6. فما العيب فيهم غير أن عدوهم*
حقير وأنى فيه للرفعة الرحب
Babu Wani aibu atare dasu Kai bari maqiyansu ma sune wulaqantattu agurin Allah Kuma inbanda rashin tunani wace daukaka ce acikin qinsu???
7. فساوم بالزهراء هندا وبالذي*
علا إقتنا جروا عويا به حرب
Tawaya ta tabbata ga Wanda yasaida Zahara,u yasayi Hindu haka zalika tawaya ta tabbata ga Wanda yasaida Ali yasiyi kuykuyon da dukjikinsa yake dauke da qazuwa daga manzan Allah (s.a.w) ma,ana muawuya .
8. فداكم مصون الروح قلبي وقالبي*
وذا جلل فيكم إذا صدق الحب
Raina da zuciyata da gangar jikina fansa gareku yaku biyar ma,ana ahlul kisa,I wannan bakomaibane gurin Baku kariya indai soyayyar ta gaskece.
9. فداكم أبي والأم والأهل كلهم*
فسلمكمو سلمي وحربكموا حرب
Hakazlika babana da babata da dangina duka fansa ne gareku ahlul kisa,I zamanku lafiya shine zamana lafiya yakinku Kuma yakinane sai inda qarfina yaqare.
10.فداكم أحبائي فداكم أعزتي*
فداكم فداكم كل من شأنه القرب
Hakazlika masoyana da duk Wani magirma agurina da duk Wani makusancina fansa ne fansane gareku yamutu kurayu.
11.أيا أهل بيت المصطفى طاب ذكركم*
وسيف لساني في الدفاع لكم عضيم
Yaku ahlin gidan manzon Allah (s.a.w) ambaton ku yada dada aharshe kaifin harshene gayawajini na wucene wajen Baku kariya.
12.ولذة سمعي في سماع حديثكم *
ومحكم لفظي في مدائحكم رطب
Zancenku shine abinda kunnena yafi jindadin saurara hakazlika harshe yafi Bada qawa da kalmomi nacika wajen begenku.
13.فلو أن ما بي من غزيز ودادكم*
تفجر نحو الصم أذهبها الصيف
Da soyayyar danakemuku zatai ambaliya tabi takan kuraman duwarwatsu da qarfin ambaliyar yatafi da wadannan manyan duwarwatsun.
14.ومجنون ليلى لو يقاس جنونه*
بمجنونكم لم يبق في برئه ريب
Daza,a auna haukan majnunu Laila akan son Laila da kwatankwacin haukan son da nake muku da daga ranar za,a tabbatar majnunu Laila yawarke.
15.وما كان في لبنى غرام لوانجلى*
غرامي إذا ما ميط عن غيبه الحجب
Ina lubna da akece yahaukace akan soyayya to daza,a cire hijabi a auna haukan sonsa da haukan son da nake muku yaku ahlin gidan manzon Allah (s.a.w) to da daga ranar za, a tabbatar wasa yake.
16.فهل لك بالثقلين عدل وإن علا*
عدا الأنبياء فيما روته لنا الكتب
Yakai mejada wadannan ahali shin Kanada kwatankwacin wadanda ma,aiki yagwada da al-qur,Ani komai buwayar mutum idan kacire annabawa ? Kamar yadda yazo acikin litattafan musulunci?.
17.ودونك في الغبرا ودونك في السما*
يمينا شمالا دونك الشرق والغرب
Kakalli fadin sararin sama da qasa gabas da yamma kudu da arewa dama da hagu.
18.فهل لعلا أهل الكساء مشابه؟؟؟*
وهل لهمو في رحب مقدارهم درب؟
Shin kaga Wanda za,a iya
Gwadawa da ahalil kisa, I ? Shin kaga Wanda yakaisu qarfin Iko?.
19.وهل أسرة ترقى إلى نحو عرشهم؟*
متى؟والى من ينتمي ذلك السرب؟
Shin akwai Wani family da uban dakinsu yakai matsayin da uban dakin ahlul kisa,I yake Kai? Yaushe Akai haka wane irin garkene yake da irin wannan uban gidan?
20.فمن كأبيهم؟من له مثل أمهم؟*
وهم فيهمو القرآن أنزله الرب
Kadada Duba ko Ina afadin duniyar Nan kagani shin akwai uba irin ubansu? kokuma akwai Mai uwa irin tasu? To kasani akan wannan Yayan dakine Allah yasaukar da al-qur,Ani .
21.وطهرهم في "إنما" كل رجسهم*
فطاب لهم أكل وطاب لهم شرب
Kuma yatsarkakesu acikin suratul ahzab ayata 33 asabo da hakane ma cinsu da shansu ya tsarkaka ma,ana ci da Sha na qutu ruhin.
22.وليس يماري فيهمو غير جاحد*
جهول لأخبار أتانا بها الغيب
Bame ja dasu saimai taurin Kai jahili Wanda be karatuba dakuma Wanda baisan irin labaran da gaibu yazo dasu kansuba.
23.سلامي على أهل الكساء متى غدا*
يؤنبني من أجل حبي لهم هب
Gaisuwata ta tabbata ga wadanda ma,aiki ya lullube da bargo aduk sanda akawayi gari Wani mayaudari Yana ganin laifina adalilin son danake musu.
24.سلامي على أهل العباء متى غدا*
يريد مماتي ناصبي به نصب
Gaisuwata tabbata ga wadanda ma, aiki yalullube da bargo aduk sanda akawayi gari Wani naasibi Yana fatan yaga na mutu to a muqabilin wannan Allah yajuya wannan fatannasa yazama salati ga ahlul kisa, I.
25.صلاتي وتسليمي عليكم متى غدا*
يدللني من أجل وجدي لكم صب
Salatina da taslimi yatabbata gareku aduk sanda akawayi gari Wani Wani masoyina yayi farin ciki da ganina adalilin soyayyar danake muku.
26.وما فاز من خدامكم كل مخلص*
رعى ذمة المختار لا سيما الصحب
Allah kayi salati ga ahlul kisa, I kwatankwacin yadda hadimansu suka rabauta Kuma suka kula da haqqinsu Dana kakansu musamman ma sahabbai na kwarai.
27.وما أرغم الرحمن أنف عدوكم*
لدى الحوض مهما ذيد عن حوضكم صحب
Salatina da taslimi na ya dauwama kanaku muddun Allah yatirmije hancin magautan ku Abakin tafkin al-kausara yayinda za,a Kore wasu mutane da akecewa sahabbai Amma basahabbai bane na kwarai maqiya annabi da ahlin gidansane ma,ana( Fi,atul bagiya )
Safiyullahi hamza Muhamma makwarari
بقلم صفي الله حمزة محمود مكوراري
©fatimiyyaa
Comments
Post a Comment