SHARIF RABIU USMAN BABA YACIKA KWANAKI DUBU DAYA DA RASUWA


 Allah Sarki Rayuwa:Cikar Sharif Rabi'u usman Baba kwana dubu da Rasuwa" Tarihin Rayuwar sa dakuma wakokin shi

February 07, 2022

Allah Sarki Rayuwa:Cikar Sharif Rabi'u usman Baba kwana dubu da Rasuwa" Tarihin Rayuwar sa dakuma wakokin shi



 Kwanan watan yazo da kamanceceniyar lambobi kuma yayi daidai da cika kwanaki 1,000 cif da rasuwar Sharif Rabi'u Usman Baba "Mutuwa bata bar talakawa ba ta yanke talaucin su, Ta kan bi sarakai ma mutuwa ta raba su da mulkin su, Um uhum wayyo kai na, Mutuwa Riga ce ba ta fita.”


 

Baitin waƙar mutuwa kenan ta shahararren mawaƙin yabon Manzon Allah  (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam), Sharif Rabi'u Usman Baba, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Alhamis 9 ga Mayu, 2019 bayan wata gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu a gidan sa da ke unguwar Janbulo a cikin garin Kano.

 

Marigayin, mai shekaru 52  a duniya a wani ƙaulin kuma 54, ya rasu ya bar mata uku a wani ƙaulin kuma Mata 4, da Ƴaƴa 13 ko kuma 18.

 

Kafin rasuwar sa dai shi ne shugaban ƙungiyar sha’irai da ake kira Jama'atu Shu’ara’il Islam Muddahi Sayyidul Anam (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam).

 

Rasuwar sa ta jijjiga duniyar Musulmi baki ɗaya, domin kuwa Sharif Rabi’u Usman Baba ya zama fitaccen Mawaƙin Janabin ANNABI (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam) sakamakon irin salon da ya zo da shi da kuma tafiya da zamani. Irin salo da jigon da ya ke amfani da shi wajen faɗakarwa, ilimantarwa ta hanyar waƙoƙin sa, ya sa ya zamo abin karɓuwa a wajen jama’a. Don haka babu wani kokwanto shi wani jigo ne a cikin waɗanda su ka kawo wa ɓangaren waƙoƙin Musulunci juyin-juya-hali.

 


Tauraruwar Sharif Rabi’u Usman Baba ta fara haskawa ne tun cikin shekarar 1985, a shekarar 1998 ya yi shaharar da babu wani Sha’iri da za a haɗa shi da shi a fagen waƙa.

 

Ya yi waƙoƙi masu adadi da yawa, kamar irin su:- Tauhidi Babu tantama, Mutuwa, Tsumagiya, Sha yabo, Majalisi, Wakar Sadiya, Zumunci, Tambaya, Sharifai, Fadima, Garkuwa, Batijaniya, Bakadiriya, Fiyayya, Sayyadil Wara, Zuma, da sauran su, amma dai waƙar da ta ƙara haska tauraruwar sa itace "Dukkan Mai Matsayi Wajen Ilahu Ba Zai Kai Ka Ba, Dan Amina" 


 

 

Fitowar wannan waƙa ta sauya alƙiblar matasa da yara ƙanana, domin kuwa a lokacin waƙoƙin da su ke tashe kuma su ka fi karɓuwa ga matasa da yara su ne waƙoƙin Indiya da na Sudan, waɗanda ana sauraren su ne ba don ana fahimtar abin da su ke faɗa ba sai dai son nishaɗi kawai. Amma fitowar wannan waƙar ta Sharif Rabi'u Usman Baba da sauran waƙoƙin sa da su ka biyo bayan ta ya kawar da waƙoƙin Indiya da na Sudan daga bakin matasa da ƙananan yara, don haka duk lokacin da za ka ji yara su na waƙa don nishaɗi sai ta yabon Manzon Allah (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam). Kuma hakan ya sa matasa da dama su ka rungumi ɗabi’ar tsara waƙoƙin yabon Janabin Manzon Allah (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam).

 

Kafin wani lokaci sai ga shi a birnin Kano da sauran jihohi an samu masu yabon Manzon Allah (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam) ba su da adadi. 

 

Tafiya da zamani ta sa Sharif Rabi’u Usman Baba ya daɗe ya na jan zaren sa, domin kuwa a farkon waƙar sa ya fara ne babu Kiɗan Bandiri, amma ganin Ƙadirawa da su ke yin waƙa da bandiri su na karɓuwa sai shi ma ya juya ya shigar da Bandiri cikin waƙar sa, duk kuwa da cewa a lokacin ya sha suka a wajen Tijjanawa da su ke ganin Ƙadirawa ne su ke kaɗa Bandiri, a tafiyar Tijjaniyya babu Kiɗan Bandiri. Amma dai ya tafi a hakan tare da ba su amsar da ya ke ganin ita ce hujja a gare shi.


A lokacin da kiɗan fiyano ya fara tashe, nan ma Sharif Rabi’u Usman Baba bai yi ƙasa a gwiwa ba, sai ya ɗauki salo don ganin kada waƙoƙin finafinan Hausa da su ke tashe a lokacin su rufe irin nasa. Don haka shi ma sai ya fara waƙa da kiɗan fiyano inda a nan ma ya yi ta samun suka, sai dai ya kare kan sa da waƙoƙin Larabawa na yabon Manzo da su ke yi da kiɗa. Ya nuna cewar waƙar sa da fiyano a duniyar Musulunci abu ne karɓaɓɓe, in dai za a bi tsarin da ya dace. (A lokacin har yayi Ƙasida ɗauke da muryar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi) inda yake bada fatawa akan halascin hakan.

 

Marigayin Mutum ne da ya san Ƴancin sa, don haka bai yarda zama cikin rashin Ƴanci ba, domin kuwa an yi wani lokaci da duk shaharar da Mawaƙi ya yi to Ƴan kasuwar da su ke buga Kaset a Kasuwar Ƙofar Wambai su ke kallon su ne kawai su ka ɗaga shi. Amma shi da su ka kawo masa wasu dokoki ya ga ba zai amince da su ba sai su ka raba hanya. Sai ya buɗe Tsumagiya Studio a Unguwar Gwammaja, wanda duk mutumin da ke son waƙoƙin sa ya je can ya saya saboda Ƴan kasuwa sun daina buga waƙoƙin sa, hakan bai sa Sha'irin ya koma baya ba, sai ma shaharar sa ta yi gaba. 

 

Haƙiƙa Sharif Rabi’u mutum ne da ya yi rayuwar sa cikin shahara kuma har ya koma ga Allah tauraron sa bai dusashe ba. Domin kuwa da aka bayyana rasuwar sa a soshiyal midiya, sai masu hulɗa da shafuka su ka yi ta saka hotunan sa da kuma rubuce-rubuce na alhini da miƙa ta’aziyya ga al’ummar Musulmi a game da rashin sa. 


 

 

Lallai duniyar Musulmi ta yi rashin babban Mawaƙin Janabin Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam). Kuma za a daɗe tarihi bai manta da Sharif Rabi’u Usman Baba ba, musamman waƙar sa ta Tsumagiya, Isra’i, Imamul Mursalina da sauran ɗimbin waƙoƙin sa. 

 

Mu na fatan Allah ya sanya shi cikin Dhiyafar Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu AlaiHi Wa AaliHi Wa Sallam) Ya sabunta rahma a gareshi, Ya jiƙan sa, Ya kai rahama kabarin sa. Allah Ya albarkaci zuriyar sa, Ya bai wa dukkan Musulmi haƙurin jure wannan babban rashin da aka yi.


Daga:

Khalifah Zubairu M Sani

Labari


©Fatimiyyaa

Comments