1. Alkali: "Shin alkawari zaka dauka cewa zaka fadi gaskiya ko rantsewa zakayi da Alqur'ani?"
Amsar sheda: "Alkawari zan dauka zan fadi gaskiya".
Nan take Alkali ya umarci registrar daya alkawarantar da sheda.
- Registrar ya alkawarantar da sheda kamar yadda doka ta tanada.
2. Kotu ga masu gabatar da kara: "Kotu ta baku damar gabatar da sheda na farko.
3. Lauyan masu kara:
- Shin kasan wanda ake kara?
Amsa:" eh na sansh"
- lawyer: ya sunan sa?
Amsa: Abdujabbar Kabara
- lawyer: "Mai ka san ya nayi, ma'ana aikinsa?
Amsa: "Malami ne mai karantarwa.
- Lawyer:
" A ina yake karantarwa?
Amsa:
" A Jami'u Ashabulkahfi da Jami'ur Rasuul.
Lawyer: "wuraren da ka ambata a wanne gari suke?
Amsa: " A nan Garin Kano
Lawyer: "ya akayi kasan yana karantarwa?
- "Na sani ne saboda ina makotaka da Ashabulkahfi, kuma akwai yan uwana da abokai ba wadanda dalibansa ne.
Lawyer: Tunda kace kai makwabcinsa ne, shin kana halartar karatuttukansa ne?
Amsa: " eh ina halartar karatuttukansa.
Lawyer: "Shin zaka iya tinawa a ranar 08/10/2019 da misalin karfe hudu na yamma ko makamancin haka, ka fadawa kotu abinda ya faru?
Amsar sheda: "Wannan ranar juma'a ce bayan nayi sallar La'asar a inda nake sana'a ta a Sani Mainagge tsallaken tsallaken go dan kankara. Na tsallako domin sauraron karatu Kamar yadda na saba.
Bayan an karbi gaisuwa da addu'o i ga jarirai da aka haifa. Sannan Malam ya fara bayani akan mas'alar auren Annabi (SAW) da Nana Safiyya. Sheda ya maimaita kalmomi da aka sa a wurin mukabala (kamar su Kwace, Fyade, Auren Dole).
Da yake kokarin yin Karin haske ga kotu, sheda na farko yace:
”Wanda make kara yace: "Nana Safiyya tazo a kaso na wani Sahabi, sai Annabi (SAW) yasa aka kwato masa ita. Ya musanya masa da kuyangu guda 16. Yace kaga wannan kwace ne kenan.
Ita kuma yace mata: Daga Yau kin zama mata ta, kuma sadakin ki shine yancin ki. Ya fadi lambar hadisin a Musulim (1365) da kuma (1428) yace sukai ta maimaitawa. Ya kuma ce wannan fyade ne daraja ta daya. Kuma hadisin daya fada babu wannan kalma ta kwace da fyade a cikin hadisin.
Wannan yasa na fahinci shine ya kaga musu.
ZAMU CIGABA....
AKAFSAN REPORTERS
14/19/2021
Comments
Post a Comment