TSAKANI NA DA MAI GIDANA
Jiya da yamma wani me gida na ɗan boko kuma ɗan siyasa ya kirani da rana ina shirin tafiya zikiri yace mun in na gama abunda nake komai dare yana son gani na nace masa Tom.
Haka kuwa akai misalin 9:10 naje ƙofar gidan sa nai masa waya ya turo 'yarsa ta shiga dani ya fito muka gaisa yasa wannan yarinyar ta kawomun wainar shinkafa bayan naci na koshi yasa aka kawo shayi me dumi aradun Allah shayin nan ya bada citta😅👌
Yace: kasan me yasa na kiraka?
Nace: masa A'a
Yace: Jiya da daddare kamar koda yaushe idan zan kwanta nakan kunna karatuttukan malaman mu na Ahalussunnah a wayata ina saurara har bacci ya ɗauke ni, to Jiya sai na kunna karatun Dr. Sani wanda yayi na raddi ga malamin ku wanda yayiwa suna da warwarar shubuhohin Abduljabbar ka taɓa jin sa?
Sai nace: eh daga farko har karshe ma kuwa?
Sai yace: me yasa ka saurara?
Nace: Allah ya gani kuma shine shaida ta na saurara ne dan inji ya ɗauko shubuhohin ya warware dan In shiriya in hakura dabin malam Abduljabbar kuma wallahi da naji shubuhohin ya warware kamar yadda ya faɗa nine farkon wanda zan turawa maulana Amirul wa'izina Allah ya kara masa yarda dan inji ta bakin sa indai ya gaza bani gamsar dani in hakura da bin wannan tafarki nasa.
Yayi dariya yace mun wato Allah ya kara masa yarda kai Hafizu bana son wuce gona da iri😅
Nace: Allah ranka ya dade gaskiya na faɗa maka.
Yace: bance karya kake ba ai Allah ya kara masa yardar na cewa banso ka huce gona da iri😅
Nai dariya nace: Allah ya taimakeka ai Addu'a nai masa da fatan alkairi dan ni a yanzu shi kaɗai na yarda na danka amanar imani na a hannunsa kaf malaman nan.
Yace: naji to da ka saurari waccen karatun baka ji an warware shubuhohin ba?
Nace: daga farko har karshe banji warwarar nukuɗa ɗaya daga nukuɗoɗin Maulana Amirul ya taɓa taunawa ba.
Yace: kamar yaya fa?
Nace: misali Maulana Amirul wa'izina ya tattauna maganar hadisin Anas ta zuwa gidan Ummu haram da cin Abincin Annabi a gidan ta da kama masa Kwarkwata dayin bacci zuwa karshen hikayar to da Dr Sani warwarar shubuhohin zaiyi sai ya ɗauko wannan hadisin sai ya fito da fikihun dake ciki saɓanin wanda malamin mu ya fito dashi na cin mutuncin Annabi da hadisin ke ɗauke dashi sai ya karyata maganar malamin mu ta cewa ainihin hadisin na ibn Abbas ne Anas ya ɗauka ya juya yaci mutuncin Annabi dashi.
Sai yace: wannene na Anas wannene na ibn Abbas ɗin ai magana za muyi ta fahimta ni ban ban fahimci maganar taka ba?
Sai nace: abunda nake nufi malam ya kawo hadisin da Anas yake cewa Annabi yana zuwa gidan ummu haram matar ubadatu bin sabit ta bashi abinci yaci ya jingina a jikinta ta kama masa kwarkwata barci ya kwashe shi yayi mafarki a cikin baccin Nasa wasu daga Al'ummar sa za su haura kogi suyi yaki dan daukaka kalmar shahada.
Na cigaba da cewa sai malam ya kawo hadisin Abdullahi ibn Abbas yace wata Rana Annabi yana ɗaya daga cikin dakunan matansa sai ya kishin giɗa bacci ya kwashe shi sai can yafarka yana murmushi sai wannan ɗaya daga matan nasa da yayi baccin a ɗakin nata take cewa su Rasulullahi me yasa kake murmushi?
Sai yake bata labarin cewa a cikin baccin sa yayi mafarkin wasu daga Al'ummar sa zasu haura kogi suyi yaki dan ɗaukaka kalmar Allah ya faɗi alkairi masu yawa akansu.
Sai malam yace: mana wannan hadisin Anas ya ɗauka ya fitar da Annabi (S.A.W) daga gidan sa ya kaishi gidan ummu haram ya fitar dashi daga ɗakin matar sa ya kaishi ɗakin matar wani ubadatu bin sabit yace babban dalili na kan hakan shine kwata kwata a sanda Anas ya zantar da nasa hadisin babu ragowar matan Annabi S.A.W a duniya saɓanin ibn Abbas da sanda yake zantar da nasa hadisin akwai ba'arin matan Annabi S.A.W a duniya.
Nace: to da Dr Sani warwarar zaiyi da gaske sai ya ɗauko irin waɗannan nukudodin ya warware ya kore cin mutuncin Annabi S.A.W da Malam yace Anas yayi a wannan riwayar takan nasafta tawa Annabi kwarkwata,shiga gidan matar wani da bacci a jikin ta sai kuma ya tabbatar da cewa ba hadisin ibn Abbas ya sata ba.
Oga yayi shiru yana saurara ta can yace mun: amma na taɓa jin Malam rabi'u yana yiwa malamin ku raddin wannan hadisin yace malamin ku karya yake a gefe Annabi ya kwanta ba a jikin ta ba kamar yadda malamin naku ya faɗa ba.
Nace: na jishi shima bai iya warware hujojin malam na karyata hadisin ba sai renin hankalin da suka saba yiwa mutane nace a ranka ya dade a yaya akewa mata tsifa?
Yace: mai tsifar tana zama a sama ta bude kafafunta wacce za aiwa ta shiga tsakiyar ta ta jingina da jikin ta.
Nace:tom ranka ya dade a hadisin ma cewa akai (فَاتَّكَأَ عِنْدَهَا) ya jingina a jikinta.
Na cigaba da ce masa kuma ko ba a faɗi hakan ba ranka ya dade aka ce ta kama kansa tana duba kwarkwata ai babu bukatar ace ga a sigar da akayita tunda gashi da bakin ka yanzu ka faɗi yadda ake tsifa.
Sai yace: haka ne kuma.
Nace: Da da lokaci sai na ta faɗa maka hujjojin malam na rushe hadisin da yarda shi mai hadisin ya dinga canja karyar kowane lokaci akwai yadda zai fada ɗabakar wanda yake zantarwa da maganar tana kasa yana kara munana riwayar nace amma duk yadda zan faɗa maka baza ka gamsu ba sai kaji malam da kunnen ka.
Yace: tukunna dai kasan me yasa na kiraka?
Nace: A'a Allah ya taimakeka?
Yace: Allah ya sani ina jin zafin bin mutumin nan da kake ko status ɗin ka sai dana daina budewa dani da yayan ka..... munsha zama mu tattauna ko ranar da akai zama damu a masallacin unguwar ku akan yadda za a bullowa da malamin ku tare dashi muka taho har kofar gidan ku ya shiga na huce sai da mukai zancen ka to amma nutsuwar ka da yarda mu'amalar ka take yasa ban iya fitar dakai daga sabgogina ba.
Nayi murmushi nace: Allah ya taimakeka ai ni me biyayya ne a gareku tun a lokacin da kunyi mun magana ai zanji abu ɗaya kawai zan nema ku kaini wajen wani malami da zai bani hujjar da tafi ta Maulana Amirul Wa’izina shikenan an gama.
Yayi dariya yace: kai ko Hafiz ba wannan ba, jiya abunda yasa nayi tunanin neman ka shine furcin Dr na cewa bashi da lokacin warware shirman malamin ku taya zaiyi awa 3 yana zuba kazanta shima yayi awa 3 yana sharewa wannan bazai yuhu ba.
Ya ci gaba da cemun: sai wani tunani yazo raina shin idan barnar wannan mutumin da suke faɗa takai yadda suke faɗa ko awa dubu yayi ai ya wajaba ayi masa awa dubu 10 dan warwarewa kodan a tsare imanin mutane.
Nayi dariya nace: Allah ya taimakeka naji daɗin wannan tunanin naka kuma gashi yanzu na kara maka daga farko har karshen wannan warwar da shehi Sani yayi bai iya warware mas'ala ɗaya maimakon ya shagala da warwarar shubuhohin da yace sai ya shagala da fadar inda ake ciro shubuhohin 😅🤣
Yace: yace mun yanzu kasan me nake so karatuttukan malamin ku nake so ka saka mun waɗanda aka ciro waɗancan muryoyin a ciki.
Nace: tom ranka ya dade.
Kunsan ya muka karke dashi akan Bakari Mika'il ku biyo ni a gaba ta 2
Comments
Post a Comment