DAGA KOTU
Sheikh Abduljabbar ya fara kariya akan kunshin tuhuma ta 4 a kotu.
Labarai
Sheikh Abduljabbar ya fara kariya akan kunshin tuhuma ta 4 a kotu.
03/31/2022 12:30 in Najeriya
Dan Bala
A safiyar yau ne a ka cigaba da gabatar da Shari'ar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Abduljabbar Kabara a babbar kotun shari'ar Muslunci dake zaman ta a kofar kudu karkashin jagorancin Mai Shari'a Alƙali Ibrahim Sarki Yola.
A zaman na yau, lawyoyi 9 ne suka bayyana a gaban kotu a matsayin masu gabatar da kara wanda suka haɗa da;
Sa'ida Shu'aibu SAN
Mamman Yusufari SAN
Abdurrahman Mukhtar Abdullahi
Rabiu Shehu Ahmad
Abdulkarim Mustafa
Umar Usman Dan Baito
Hafsa Aɗɗa'u
da kuma Fatima Sagir Musa
Daga ɓangaren masu kare wanda ake tuhuma akwai A.O Muhammad SAN
Umar Faruk
Ishaq Adam
A zaman na yau Malamin ya fara bada kariya akan kunshin tuhuma ta 4. Kotu ta fara da tunawa Malamin rantsuwa da yayi da Alqur'ani cewa zai faɗi gaskiya, ya kuma sheda cewa yana sane da wannan rantsuwar.
Bayan karanta ma wanda ake ƙara kunshin tuhuma ta 4, Lawyan sa ya gabatar masa da tambayar shin ko ya fadi abinda ke cikin kunshin tuhumar ko bai fada ba.
''Wasu na fada, wasu kuma ba a fade su yadda na fada ba. Ni abinda nace (Wata baiwar Allah tazo tana sha'awar Annabi, shi kuma yace jeki nemi gu ki jira Ni zan zo in biya miki buƙatar ki, yaje ya same ta ya biya mata bukatar ta), wannan jumla lallai na karanta ta a Sahihul Bukhari da Muslim cikin karatun da nayi, kuma na kore ta, dan ban yarda Annabi SAWA zai aikata haka ba'' inji Sheikh Abduljabbar Kabara.
Ya kara da cewa ''Wanda ban fada ba shine fadin su nace (Ya bita kwararo ya biya mata bukatar ɗa namiji da mace).
Lawyan wanda ake ƙara ya tambayi Malamin ko shin yayi amfani da lambar hadisi 5120 da kuma 2326 cikin Bukhari da Muslim, kuma idan aka duba hadisan za a ga wannan magana?
Malamin ya amsa da cewa kwarai yayi amfani da su kuma za a same su kwabo da Kwabo yadda ya fada. Ya kuma kara da cewa shi bai aminta da wadannan maganganun ba, hasali ma shi kore su yake a cikin karatun sa. Ya kuma kara da kawo wasu littattafai da suka fito da ma'anar da ya ambata, ya ambaci littafin Fathul Bari Juzu'i na 11 shafi na 90, da kuma littafin Fathul Malik bi tabwidil tawhid Juzu'i na 6 shafi na 315.
Malamin ya bayyana cewa ba daidai bane ace ya ƙagi maganar da ta zo a cikin littafi, da kuma wacca bai fada ba. Ya kara da bayanin cewa;
''Tuhuma ta 4 ce kawai suka fadi makamancin abinda na fada, amma ragowar kunshin tuhumar sun datse mun maganganu na''
Malam Abduljabbar Kabara ya kuma bayyanawa kotu cewa duka karatukan sa ana nadar suna na'ura mai ƙwaƙwalwa, ya ambaci wani mai suna Najjarullahi a matsayin wanda yake nadar karatun a na'ura mai ƙwaƙwalwa, kuma ya na bibiya yaji karatun dan tabbatar da ingancin su, sannan ya bada umarnin a turawa masu bukata.
Darasin da ake tuhumar malamin da ambatar lafazin da ke cikin kunshin tuhumar na ciki darussan da Malamin yace an naɗe su, kuma ya bibiya ya saurara, kuma shine yake kula da kwafin karatun sa da ake tura masa.
Kotu ta tafi hutun Mintuna 30, inda zata dawo dan a cigaba da gabatar da Shari'ar.
Comments
Post a Comment