Karatun da sheikh Abduljabbar yabiya a Kotu 17/3/2022


 CIKAKKEN KARATUN DA AKAI A KOTU TARRDA SHEIKH ABDULJABBAR

Zaman Kotu Na 17-3-2022


Da Farko A Wancan Zaman Da Kotu Tayi Na 2/3/2022 Malam Ya Yi Kariya Akan Tuhuma Ta Daya Da Ta Biyu Wanda A Wannan Zama Ya Malam Zai Tashi Kan Tuhuma Ta Uku Da Ta Hudu.


Lawyoyi Daga Dukkannin Bangarori  Sun Gabatar Da Kansu Ga Kotu


Sannan Sharia Ta Cigaba Kamar Haka:


Lawyan Malam: Wancan Satin Da Mukazo Mun Gama Da Tuhuma Ta Daya Da Ta Biyu Yanzu Zamu Shiga Ta Uku


Lawyan Gwamnati: Za’a Tuna Masa Da Rantsuwarsa


Alkali: Lallai Kuwa Inda Kotu Ta Tunasar Da Malam Akan Rantsuwar Da Ya Dauka Da Alqur’ani Akan Duk Abinda Zai Fada Gaskiyane


Lauyan Malam: A Cikin Kunshin Tuhuma Ta Uku Sunyi Bayanin Cewa Akwai Auren Dole Da Fyade,

Ka Fadawa Kotu Mai Girma Abin Da Kake Nufi, Kila Basu Fahimce Kaba Ne.


Malam: Ga Eukkan Alamu Wanda Sukayi Wannan Kara Basu San Ma’anar Fyade Ba,

Dalilina Akan Haka Duk Shaidun Su Da Na Tambayesu Meye Fyade (Me Ake Nufi Da Kalmar Fyade Da Auren Dole) A Gaban Wannan Kotu Basu Ban Amsaba.


Dalilina Na Biyu Daya Sa Nake Kyakyawan Zaton Basu San Ma’anar Fyade Ba Nayi Musu Tambayoyi A Gaban Wannan Kotu Mai Girma Musamman Shaida Na Daya Sai Da Akayi Masa Kiranye Da Shaida Na Hudu (Kwararren Shaida) Sai Gashi A Gaban Wannan Kotu Sun Tabbatarwa Da Ma’aiki Siffar Da Nake Kira Fyade Ba Tare Da Sun San Wannan Siffar Itace Fyade Ba,

Misali Kwararren Shaida Ya Kafa Hujja Da Littafin Karshi Juzu’I Na 2 Shafi Na 64 Akan Lamarin Auren Nana Safiyya Amma Abin Mamaki Bai Gane Cewar Fadin Karshi “Yana Daga Cikin Kebance-Kebancen Ma’aiki (S.A.W) An Halarta Masa Auren Matan Al’ummarsa Wadda Yaga Damar Aurenta Da Kansa Ko Ga Waninsa” Ya Maimaita An Halarta Masa Zai Iya Yin Hakan Ba Tare Da Yaddar Ita Matar Da Za’a Aura Ba Kuma Ba Tare Da Yaddar Iyayenta Ba, Kuma Bada Sadaki Ko Waliyyi Ko Shaida Ba.


Wani Abu Na Gaba Wanda Yake Nuna Shi Kwararren Shaidarsu Da Shaida Na 1 Basu San Ma’anar Fyade Ba A Nan Kotun Na Tambayi Shaida Na Daya Ya Fitarmin…… Adaida Wanna Guri Ne Sai Lawyan Gwamnati SAN Ya Nike Yace Ai Sam Ba Haka Ake Ba, Bai Kamata Ya Dainga Yin Zancen Shaidun Da Suka Gabata Ba


Alkali: Ni Na Bashi Dama Zai Iya Yin Hakan


Malam: Ya Cigaba Da Maganar Da Ya Fara Aka Katseshi Yace:


A Ina Aka Samu Yardar Nana Safiyya Duba Da Cewa Hadisin Da Ya Karanto Ya Nuna Cewa Sanda Aka Pito Da Nana Safiyya Daga Haibar Bama Ta Da Tsarki To Ta Ina Za’a Fitar Da Yardarta Da Iddarta Da Bayan Batai Tsarki Ba Sai A Inda Suka Ce Wai Ya Kwanta Da Itaba Ya Kasa Bani Aamsa.


Sanna Ya Kara Da Cewa Ba Wannan Ne Na Farko Ba Auren Nana Zainab Duk Babu Wadannan (Shaidu Waliyyi) Kuma Na Tabbatar Masa Da a Littafin Ba Haka Bane Kuma Alkur’ani Cewa Yayi

“ZAWWAJNA KAHA) Amma Yace Babu Yardar Ta Wannan Yazo A Hadisin 1428 Muslim Wanda Ake Ta' Baba Kansa A Jere Anas Ya Jerasu Yace “ Yayin Da Iddar Zainab Ta Kare Ma’aiki Yace Da Zaidu Ya Gaya Mata Yana Sonta kuma Hakan Akayi.


Wadannan Abubuwa Guda Biyu Suka Saka A Wancan Hadisin Babu Baiko, Babu Shaidu, Babu Idda, Ya Sanya Maliku Da Abu Hanifa Da Laisu Bn Sa’ad Da Ibn Shubruma Muhammad Bn hassan Ashaibani Da Zufar Bn Huza’if Da Ibn Muraibidi Da Abu Dayyib Addabariy Da Jabir Bn Zaid Suke Cewa Wannan Aure Bai Halarta Ba Don Haka Annabi Ba Zai Ba Kuma Bai Ba.


Wannan Shine Yasa Na Gamsu Da Maganarsu Nace Nima Wannan Aure A Guna Haramtacce Ne Ma’aiki Bazai Yishiba Domin A Cikinsa Akwai Nasabta Masa Fyade Wato Yin Aure Ba Baiko Sannan Akwai Nasabta Masa Yin Aure Ba Sharrudan Auren Duka Wadanda Suka Hada Da Idda Waliyyi Sadaki Da Shaidu.

To Wannan Yake Hukunta Min Da Cewar Sun Gina Cajinsu Da Shaidunsu Ba Bisa Ilimi Ba.


Fadin Shaidarsu Na Biyu Sanda Na Tambayeshi Ya Fitar Min Da Sadaki A Cikin “YA MAIDA YANCINTA SADAKIN TA”

Bayan Da Naja Masa Ayar Da Tace Ba’a Sadaki Saida Kudi Ko Da Wani Abu Na Kudi Anan Ya Fada Cewa Ba Wanda Zai Lazimtawa Annabi (S.A.W.) Ga Yadda Zaiyi, Wanda A Zatonsu Imamu Malik Shi Ya Lazimtawa Annabi Hakan Wanda Ko Kusa Ba Haka Bane.


Muslim Yayi Babi Wanda Yake Wajabta Yin Baiko A Aure Sunan Babin

“BABIN NEMAN IZININ BAZAWARA HAR SAI TA FURTA CEWA TA YARDA ITA KUMA BUDURWA KO SHIRU TAYI AKA GANE YARDA SHIKENAN”

Shine Hadisi Na 1419 A Muslim Kuma Malik Yayi Kishin Ma’aiki Ya Musa Wancan Hadisin Nima Nace Annabi Baiba.


Mu Koma Muslim Hadisi Na 1365 Daga Zuhairu Bn Harbin Yace Isma’il Ya Zantar Dani Yana Nufin Da Ulayyata Daga Anas Har Inda SabituT Yake Tambayar Anas Menene Sadakin Safiyya Sai Yace Kanta Shine Sadakin Ta Har Saida Suka Zama Akan Hanya Sannan Aka Gama Yi Mata Kwalliya Sai Tai Masa Budar Kai A Cikin Wannan Dare Sai Annabi Ya Wayi Gari Ango. 

To A Duk Masu Sharhi Ba Wanda Ya Iya Fitar Da Baiko AnanDdon Bazai Fitaba.


Sannan Malam Ya Cigaba Yace Ga “AL MUHALLA” Na Inb Hazmin Al Andalusi Juzu’I Na Tara Shafi Na 101 Yana Magana Kan Hadisin 1365 A Muslim Yana Sharhinsa Yace Abu Hanifa Da Laisu Bn Sa’ad Sun Ce Bai Halarta Ba Yancin Kuyanga Ya Zama Sadakin Ta Ba, Sanna Yazo A Qasa Wajen Maida Martini Yace Wannan Magana Ta Limaman Nan Itace Mafi Wautar Maganar Da Kunne Ya Jita,

 Maimakon Ya Kawo Dalilinsa Kawai Sai Yace Wannan Suka Ne Ga Ma’aiki Don Haka Sun Pita Daga Musulunci, Sannan Mafiya Yawan Wadanda Sukai Wanna Maganar Zaluntarsu Akai.


Ni Kuma Da Nabi Sai Naga Zaluntarsu Kawai Yayi Don Bai Bada Wasu Hujjojiba Don Inda Sukayi Daban Inda Yayi Daban, Daga Ciki Wannan Hadisi Na Wajabcin Baiko A Aure Bai Kawoshi Ba Har Ya Gama Maganarsa.

Sannan Hadisin Nana Aisha A Muslim Wanda Yake Tabbatar Da Cewa Ma’aiki Ya Bawa Duk Matansa Sadaki Yana Nan A Muslim Hadisi 1426 Yace Abu Salama Yace Na Yambayi Aisha Yaya Sadakin Ma’aiki Yake Ga Matansa? Tace Sadakinsa Ga Matansa Shine Uqiyya 12 Da Nashshi Sai Ya Tambayeta Meye Nashshi? Tace Rabin Uqiya.


Malam Ya Cigaba Da Cewa Lafazin Da Tace Duk An Bawa Ko Wacce Wannan Adadi Ga Hujjar A Cikin “MUSANNAF” Na San’ani Malamin Bukhari Juzu’I Na 6 Shafi Na 142 Hadisi Na 10448 Ga Lafazin “ Manzon Allah (S.A.W.) Ya Yiwa Duka Matansa Sadaki Na Uqiya 12 Da Rabin Nashshi ( Dirham 500 Kenan Jimla. Hatta Zuhuri Kaga Masa Suka Yi Kamar Yadda Sheda Na Farko Ya Fada, Shima Ua Tabbatar Da Cewa Anyi Sadaki Wanda Da Shine Na Gamsu Auren Annabi (S.A.W.) Duk Yayi Sadaki.

Kai Ba Nana Aisha Kawai Ba Har Sahabbai Manya Dukkansu Sun Tabbatar Annabi (S.A.W.) Ya Yiwa Duka Matansa Sadaki Wanda A Cikinsu Akwai Wanda Sun Bawa Ma’aiki Yayansu Kamar Sayyadina Umar Dan Kaddabi Shima Yace Lallai Annabi Ya Bawa Duka Matansa Sadaki Wannan Magana Tazo A “DABAKATUL KUBRA” Na Ibn Sa’ad Albasari Mujalladi Na 8 Shafi Na 128 A Babin Bayar Da Sadaki Matan Annabi (S.A.W.) Ya Fara Da Hadisin Nana Aisha Wanda Na Kawo Yanzu Sanna Ya Karo Da Na Sayyadina Umar Da Asanidu Har Hudu, Anan Sai Malalm Ya Karanto Daya Daga Cikin Isnadan.


Sanna Malam Ya Ci Gaba Kamar Yadda Yake Abune Sananne Cewar Sayyadina Umar Yana Kin Tsadar Sadaki Da Ya Samu Cewar Ma’aiki Yayi Aure Ba Sadaki Da Ya Tabbatar Wa Da Wani Yayi Hakan.


Sannan Yayan Gidan Ma’aiki A Cikin “Dabakatul Kubra” Sun Tabbatar Ma’aiki Ya Bada Sadaki Ga Dukkan Matansa.


Malam: Ya Cigaba Da Cewa Wannan Nassi Da Kwararren Shaida Ya Kawo Yace Yana Da Kususiyyar Annabi (SA.W.) Ya Auri Mace Ba Tare Da Sadaki Ba Ya Kawo Hujja Daga Kharshi Sanna Ya Cigaba Da Cewa Wannan Maganar Cewar Ma’aiki Yayi Aure Ba Sadaki Ba Shaidu Ba Waliyyi Wannan Shine Fyade, Kuma Shi Yasa Nace An Nasbta Masa Fyade.


Malam Yace Mu Duba “KIRMANi” Yadda Ya Kawo Ta’arifin Aure A Gun Annabi Amma Shaida Ya Kauce, To Ga Shi A Cikin

“KAWAKIBUL DARARIY” Wanda Aka Fi Sani Da Kirmani Juzu’I Na 19 Shafi Na 144 Amma Sai Dai Shaida Yace Annabi (S.A.W.) Yana Bukatar Yin Auren Mace To Ta Halarta A Gareshi Ya Aurawa Kansa Ita Ba Tare Da Yardar Ta Ba Ba Tare Da Yardar Iyayen Taba, Da Zarar Yace Mata “ Ba Ni Kanki”Shi Kenan Saboda Fadin Hakan Ai Don Ya Faranta Mata Raine.


Sanna Malam Ya Cigaba Da Cewa Ga Mafi Girman Sharhin Bukhari Juzu’I Na 9 Shafi Na 313 Yace Wasu Sunyi Suka Akan Hadisin Bukhari Cewar Ta Yaya Bukhari Zai Maganar Saki Bayan Ba’a Daura Aure Ba, Kuma Da Ya Nemi Ta Bashi Kanta Taki To Ta Yaya Za’a Yi Maganar Saki?. Ina Tunatar Da Kotu Cewar Na Tambayi Kararran Shaida Wadannan Tambayoyi A Wannan Kotu Mai Hirma Kuma Ga Irin Amsar Da Ya Bani Yace “ Ai Shi a’aiki Zai Iya Aurawa Kansa Koda Matar Ba Tare Da Yardar Taba Kuma Ko Da Iyayenta Basu Yardaba” Sai Nace Masa To Meye Auren? Sai Ya Kuma Cewar Ai Turawar Da Yayi A Zo Masa Da Ita Da Kawota Gabansa Da Akayai Da Sha’awar Ta Da Yayi Wato “RAGBA” Aure Ya Dauru Ko Tana So Ko Bata So Cewarsa” Bani Kanki” Kawai Don Ya Da Dada Mata Ne.


Malam Ya Ci Gaba Da Cewa Su A Gurinsu Duk Ayoyin Alqur’ani Wadanda Suka Halarta Matsayin Aure Da Yadda Ake Yinsa Sun Rushe Kawai Suka Ce Idan Yaga Mace Yayi Sha’awarta Ta Halarta A Gareshi Ko Ta Yarda Ko Bata Yarda Ba Haka Ko Iyayenta Sun Uarda Ko Basu Yarda Ba Ko Tana Idda Ko Babu Sadaki Kuma Wannan Haka Yace A Cikin Littafin “Umdatul Qadhi” Mujalladi Na 20 Shafi Na 327 Inda Yace Kawai Ma’aiki Idan Ya Gani Yayi Sha’awa Shi Kenan. Kuma idan Muka Duba Cikin

“AL FAJARUS SADI’I ALA SAHIHIL JAMI’I” Shima Haka Ya Fada, Bugu Da Kari Wanna Ta’arifi Kazami Shine Dai Yazo A Cikin

“IRSHADUS SAARIY” Sharhin Bukhari Juzu’I Na 12. Sannan Haka Dai Ya Kuma Zuwa A Cikin

“MAFA TIHUL GAIB” Na Raziy Mujalladi Na 25 Shafi Na 194 Shi Har Ya Zarta Su Duka Domin Yana Maganar Har Matar Aure Idan Ya Ganta Yayi Sha’awar Ta To Ta Halarta Gareshi Kuma Ta Haramta Ga Mijinta, Kuma Abin Takaici Da Bakin Ciki Hujjar Itace: Ya Tabbata Ga Annabi (S.A.W.) Idan Yaga Wata Mace Yayi Sha’awarta To Ta Haramta Ga Mijinta Dole Ya Sake Ta, Sannan Shi Raziy Ya Kuma Koro Wasu Zantuttuka Muna Na Akan Ma’aiki Wai “Saboda Wahayi Yana Wa Ma’aiki Nauyi A Farkon Annabta Don Haka Aka Halatta Masa Duk Wadda Yayi Sha’awarta Ko Matar Aure Ce Ta Halarta Amma Da Yayi Sabo Da Jibrilu Sai Aka Shafe Wannan Hukunci, Kuma Anyi Masa Haka Ne Saboda Su Debe Masa Kewa Da Sha’awarsu.


Malam Ya Cigaba Da Cewa Tare Da Munin Wannan Maganar Ibn Hajar Yayi Raddin Cewar Ba’a Shafe Taba Ya Kafa Hujja Da Cewar Ai Dabdalar Da Ma’aiki Ya Keyi A Gidan Babar Anas Ya Kasance Har Karshen Rayuwar Sa. Basu Tsaya A Nan Ba Wajen Wannan Aure Na Kususiyya Da Suka Halartawa Annabi (S.A.W.) Kadan Daga Abin Da Suka Ciro A Cikin Tafsirin “KHURDABIY” Mujalladi Na 14 Shafi Na 137 Yana Lissafin Wannan Kususiyoyin Da Mukayi Ta Rigima Da Masu Shaida Gasu Kamar Haka

1. Yin Aure Da Lafazin Kyanta.

2. Yin Aure Babu Waliyyi.

3. Ba Da Shaida Ba.

4. Sarayar Da Raba Kwana Tsakanin Matansa.

5. Idan Yaga Mace Yayi Sha’awarta Ta Haramta Ga Mijinta.

6. Bai Zama Wajibi Ciyar Da Iyalinsa Ba.

7. Zai Iya Kwace Abinci Ko Ruwan Shan Mutum Ko Da Zai Halaka Saboda Wai Fadin Allah

“Annabiyu Awla Bil Muminina Min Anfusihim”


Malam Yace To Abin Dubawa Anan Shi Ne Daga Ina Suka Samu Wadannan Maganganu? Babu Shakka Sun Samo Sune Daga Cikin Littafin “ÁHKAMUL QUR’AN” Na Ibn Arabi Anan Suka Ciro Juzu’I Na 3 Shafi Na 577 Abin Tashin Hankalin Shine Daga Annabi (S.A.W.) Suka Samo? A’A Daga Sa’idu Bn Musayyib Suka Ciro Domin Wannan Ya Rushe Alqu’ani Ya Rushe Annabi Don Haka Ba Annabi (S.A.W.) Ya Fada Ba Shi Ibnl Musayyib Shi Ya Fara Fadar Ta, Shi Kuma Ibnl Musaiyyab An Haifeshi Bayan Rasuwar Annabi (S.A.W.) Da Shekara 2 Shi Sukace Ya Fara Fadarta.

Sannan Maganar Aure Ba Sadaki Ita Kuma Wannan Maganar Qatada Ne Ya Fara Fadarta Shi Kuma An Haifeshi Bayan Wafatin Ma’aiki Da Sama Da Shekara 5 In An Bi Maganar Ba Tada Asali Daga Ma’aiki (S.A.W.).

Ita Kuma Maganar Aure Ba Yardar Mace Da Iyayenta Ba Sadaki Ba Shaida Ga Wanda Ya Fara Fadarta Shine Aliyu Bn Ahmad Al Wahidiy A Cikin Littafinsa Mai Suna “ATTAFSIRUL BASIYD” Juzu’I Na 18 Shafi Na 174 Anan Ya Fara Wannan Mummunan Jawabi Na Rushe Ma’aikin Allah, Inda Yace Al’umma A Matsayin Bayin Annabi (S.A.W.) Suke Zai Iya Yin Duk Yanda Yaga Dama Dasu Ko Da A Wajen Matansu Na Aurene Sun So Ko Sunki Hujjarsa

“ Annabiyu Awla Bil Muminina”.

Abin Takaici A Duk Wadannan Munanan Ta’arifi Da Suka Yiwa Annabi Itace Maganar Wani Rawi Da Suka Hadu Akan Rauninsa Shine Ibn Zaidin (Jada’ana) A Duba “DABARI” Mujalladi Na 10 Shafi Na 258 Gata A Hadisi Na 28335 Ita Ce Dai Maganar Dalilin Kwanciya Da Mace Ba Yardarta Cewar “ Ai Mutane Kamar Bayi Suke A Wajen Sa Shi Kuma Wannan Ibn Zaid Din Bashi Da Wani Malami A Cikin Sahabbai Sai Anas Wai Hujjarsa Cewar


“Annabiyu Awla Bil Muminina”.

Abin Dubawa Anan Shine Fadin Ubangiji A Cikin Suratu Ali Imran Aya Ta 79


“Ma Kana Li Basharin” Har Zuwa Gurin Da Allah Yake Cewa “ Summa Yakula Lin Nasi Kunu Ibadan Liy Min Dunil Lah” Ma’ana Sanna Yace Da Mutane Ku Zamo Bayi A Gareni Ba Allah Ba. Wanda Alqur’ani Ya Korewa Annabi (S.A.W) Wannan Maganar Da Shi Wanna Rawin Yake Fadar Ta Wannan Yana Nuna Bazai Yiwu Annabi (S.A.W.) Ya Hana Abu Kuma Ya Aikata Bayan Ubangiji Yana Yi Masa Kirari A Cikin Suratul A’araf Da “Allazina Yattabi Unar Rasulan Nabiyal”.


A Dunkule Bayan Zuwan Wadannan Hadisai A Guri Uku A Muslim Duk Ruwayoyin Ya Zo A Cikinsu Maganar Fyaden To Amma Abinda Zai Sa Hawaye Su Zuba Suke Sun San Ba’a Yiba Ga Hujjata Hadisin Da Shaidar Kiranye Ya Fada Na Bukhari Cewa “Har Sai Da Muka Je

“SADDIL RAUHA’I” To Shi Kansa Gun Da Suka Ce Ma’aikin Allah Ya Tsaida Runduna Ta Mutum 16000 Har Tsawon Kwana Uku Yana Amarci Mai Suna


“SADDIL RAWHA’I” To A Duniyar Nan Babu Gurin Wallahi

Ba Gurin Wallahi

Ba Gurin Kir Kirar Sunan Gurin Anas Yayi

Kuma Wannan Shine Littafi Mai Suna “MU'JMA’UL BULDAAN” Na Yakutur Rumiy Wanda Shi Wannan Littafi Geograpy Ne Na Musulunci A Cikin Mujalladi Na 3 Shafi Na 76 Yazo Kan “RAUHA’U” Yace Kwata-Kwata Ma Babu Hadi Tsakanin Rauha’u Da Makka. Sanna Guri Da Ake Kira Da RAUHA’U Bashi Da Alaka Da Khaibar Kwata Kwata Kuma Sunan Gurin

“FAJJIR RAUHA’I” Kuma Yana Tsakanin Makka Da Madina Da Alhazai Suke Zango A Gurin.

Abu Ubaida Al Andalusi Yace Ita Wannan “RAUHA’U” Annabi Ya Kirata Da FAJJIR RAUHA’IY Sai Aka Juyata Zuwa SADDIL RAWHA’I Kuma Ga Hadisin Da Annabi (S.A.W.) Yake Maganar Shi Wannan Guri Wanda Imamu Ahmad Bn Hambali Ya Ruwaito A Mujalladi Na 13 Shafi Na 109 Yace Ibn Maryam Zai Mikati A FAJJUL RAWHA’I Sai Aka Juyata Zuwa SADDIL RAWHA’I Wadda Babu Ita A Gaba Daya A Wannan Nahiyar Ta Khaibar.


Malam Ya Cigaba Da Cewar Wani Abu Da Zai Tabbatar Da Ita Kanta Qissar Ta Auren Nana Safiyya Kirkirarta Akayi Duk Sun San Cewar Kafin Haibar Da Shekara Biyu Aka Aureta Wato Kamin Ayi Waki’ar Da Akace An Kamota A Cikin Bayi Ma Ta Kasance Matar Manzon Allah (S.A.W.) Kuma Hatta Bukhari Ya Kawo Cewar Da Ita Akaje Yakin Usfan Kuma Idan Muka Duba Cikin “AL AHADU WAL MASANIY” Na Ibn Abi Asim Mujalladi Na 5 Shafi Na 440 Yana Tarjamar Hadisan Matan Ma’aiki Yazo Kan Nana Safiyya Wacce Tazo A Tarjama Ta 1069 Sai Ya Kawo Tatsuniyoyi Marasa Kyau Amma Sai Gashi Ya Kawo Hakikar Auren A Mujalladi Na 6 Shafi Na 112 Tarjama Ta 1208 Karkashin Hadimar Ma’aiki Mai Suna “Amatullah” Ga Yadda Auren Ya Faru: Daga Bakin Amatullah Wacce Itace Yar Kuyangar Da Ma’aikin Allah Ya Bawa Nana Safiyya A Matasayin Sadakin Ta A Lokacin Da Ya Aureta Ga Yadda Ta Fadi Ainihin Yadda Akayi Wannan Aure Mai Albarka

Tace Annabi (S.A.W.) Ya Ribaci Safiyya A Yakin Bani Kuraiza Ya Bata Sadakin Babarta

A Duba “Musnad Abi Ya’ala” Mujalladi Na 6 Shafi Na 170 Tarjama Ta 7125 Wanda Shi Ya Kawo Cikacciyar Qissar Kuma Itace Mafi Girmamawa Ga Hakkin Ma’aikin Allah Ga Yadda Amatullah Tace


 Babarta Ta Gaya Mata Ma’aiki Ya Ribaci Safiyya A Yakin Kuraiza Da Nadir Da Taga Yawan Bayin Da Aka Kamo Sai Tayi Kalmar Shahada Sai Annabi Yazo Da Ita Yana Janta Da Hannunsa Dama Nana Aisha Tace Ma’aikain Allah Bai Taba Taba Wata Mace Ba Sai Iyalinsa Sannan Yazo Da Ita Ya Nemi Aurenta Ya Bata Sadaki.


Sannan Malam Ya Fara Kawo Litattafan Da Suka Kawo Yadda Auren Na Gaskiya Ya Kasance Kamar Haka


(1) A Duba “ATTAUDIH” Sharhin Bukhari Amma Basa Kawo Ta A Gurin Nda Ya Kamata Amma Idan Aka Duba Nujalladi Na 25 Shafi Na 227 Bayan Duk Bayanan Da Yayi Sai Yace Ibn Mandah Da Wasunsu Sun Tabbatar An Bata Sadaki Da Kuyanga Mai Suna “RAZINA” Amma Sai Ya Cire Qissar Da Take Nuna Ba A Khaibar A Kayi Ba.


Malam Yace: Daga Wadanda Suka Fadi Auren Nana Safiyya Na Gaskiya Akwai


(2) “Dabariy” Mujalladi Na 24 Shafi Na 277 A Mu’ujamul Kabir Nasa. Yace Ma’aiki Ya Bata Sadaki Da “RUZAINA” Kuma Ya Tabbatar Da Falilin Yantata Shine Kalmar Shahada Da Ta Fada.

(3) “IBN ASAKIRA” Nujalladi Na 2 Shafi Na 221 Yayi Tarjamarta Bai Fadi Yadda Akai Auren Na Gaskiya Ba Amma Sai A Mujalladi Ba 4 Shafi Na 325 Sannan Ya Kawo Cikakken Auren Wanda Ya Hada Da Sharadin Auren Na Gaskiya Wanda Ya Gabata A Baya.

(4) “UMDATUL KARIY” Juz’I Na 20 Shafi Na 15 Ya Kawo Yadda Akayi Auren Na Gaskiya.

(5) “KUBRA” Ta Baihaki Juzu’I Na Takwas Shafi Na 209 Ya Kawo Maganar Gaskiya.

(6) “BIDAYA WANNIHAYA” Ta Ibn Kasir Ya Kawo Auren Na Gaskiya Saidai Tarjamarta Daban Bayanin Auren Shima Daban A Duba Mujalladi Na 5 Shafi Na 307.

(7) “SUBLUL HUDA” Na Salihi Shima Ya Kawo Cikakken Auren A Mujalladi Na 7 Shafi Na 213.

(8) “USUDUL GABA” Ta Ibnl Asir Mujalladi Na 7 Shafi Na 21 Ya Kawo Gaskiyar Auren Cewar Anyi Sadaki Da komai.

(9) Abu Nu’aim Shima Ya Kawo


A Nan Ne Alkali Yace


“A BARSHI HAKA KADA NA KASA KARANTAWA”.


Anan Gurin Sai Malam Yayi Tanbihi Game Da Irin Munanan Ruwayoyi Da Ake Nasabtawa Ma’aikin Allah Tare Da Tabbacin Maruwaita Akan Sam-Sam Kir-Kirarrune Kuma Wannan Shine Irin Tambayar Da Yanjarida Suka Yimin


Wai Me Yasa Nake Fushi Idan Ina Karanta Irin Wadannann Zantuttuka Nace Abinne Yake Damuna Matuka Domin Ganin Mafi Yawan Maruwaita Sun San Abinda Suke Nasbtawa Annabi (S.A.W.) Tatsuniyoyine.


KARO A TSAKANI WADANNAN RUWAYOYI


Karo A Tsakanin Wadannan Munanan Ruwayoyi Misali Hadisin Ibn Abi Shaiba Da Na Cikin Muslim Wanda Shin  Ibn Abi Shaiba Wanda Yake Nuna A Nan Take Annabi (S.A.W.) Ya Kwanta Da Ita Kuma Kamar Yadda Na Fada Ta Kan Gawawwaki Aka Wuce Da Ita Kuma Gawawwakin Yanuwanta Da Mijinta Da Babanta, Da Hadisin Muslim Na Zuhairu Bn Harbin 1365 Wanda Shi Kuma Yake Cewakan Hanyar Dawowa Yayi Kwanciyar Aure Da Ita Maimakon Su Yiwa Annabi Adalci Na Cewar Amaryar Nan Guda Dayace Kuma Aka Samu Irin Wannan Karo A Ruwayoyin Amma Sai Suka Ce Duka Sun Inganta. Amma Gashi A Cikin Ibn Hisham Mujalladi Na 4S Shafi Na 415 Sunan Babin


“BABIN TARIYAR ANNABI DA SAFIYYA DA GADIN ABU AYYUBA GA KUBBAR ANNABI”


Sai Yace Annabi Yayi Angwanci Ko Dai A Khaibara Ko A Saddurrauha’I Duba San Rai Guri Daya Ta Yaya Za’ai Haka Ta Yiwu? Sun San Ba’ayiba.

Irin Yadda Yayi Haka Ibn Kasir Yayi A

“BIDAYA WAN NIHAYA” Mujalladi Na 4 Shafi Na 211 Shima Yace Duk Biyun Anyi.

Ibnl Qayyim A Cikin

“ZADUL MA’AD” Juzu’I Na 2 Shafi Na 708 Sai Ya Canja Tsarin Maganar Saboda Ya Fuskanci Hankali Bazai Karbe Taba Sai Yace Annabi (S.A.W.) Ya Ribace Ta Sai Ya Umarci Bilal Ya Tafi Da Ita Sannan Yayi Mata Tallan Musulunci.


Anan Sai Malam Ya Dawo Kan Tuhumominsu Da Suka Gabatar Wa Kotu A Cajinsu.


Malam Yace Daga Cikin Tuhuma Ta 3 Suka Ce Nayi Wa Ma’aiki Kazafi Da Kage Cewa Ya Kwace Nana Safiyya.


To Ni Ba KWACE Nace Ba Cewa Nayi KWACEWA (Ya Bayar Ya Kwace)


Wanda Shi Kwacewa Daban Kwace Daban. Wanda Lafazin Hakan Yazo Karara A Cewa Annabi (S.A.W.) Ya Bashi (Nana Safiyya) Bayan Tsegumin Kyanta Sai Yace Ya Kwato Ta Yace Yaje Ya Dauki Wata Wannan Sunansa Kwacewa Ba Kwace Ba.


Shi Kwace Abinda Baka Baiwa Mutum Ba Ka Karba, Shi Kuwa Kwacewa Ka Bawa Mutum Kyauta Sanna Kace A Dawo Maka Da Ita Shine “Kwacewa” Kuma Wai Bayan Yaganta Kyakyawa


Wal Iyazu Billah.


Yana Daga Cikin Mummunan Bayanan Da Sukayi Akan Yadda Ma’aiki Ya Mallaketa Ta Wannan Mummunar Hanyar Kuma Da Kansu Sukazo Bayanin Dalilin Da Yasa Ma’aikin Allah Ya Bayar Da Ita Ya Kwaceta Wanda Na Tabbatar Da Karyane Ba A Yiba Irin Bayanansu Zai Sa Musulmi Ya Zubar Da Hawaye Ga Misali A Littafin “AL MUFHIM” Mujalladi Na 4 Shafi Na 109 Su Kace Ga Dalilin Kwacewa Bayan Bayarwa.

Wai Saboda Tana Daga Cikin Gidan Annabta Sannan Kyanta (Wal Iyazu Billah) Wai Kyau Yana Sa Jin Dadin Jima’i Shi Kuma Yawan Jima’ai Yana Sa A Haifi Yaya Masu Kyau. Malam Yace Don Haka Ni Banga Wani Daliliba Face Karawa Kwaba Ruwa Da Cin Mutuncin Annabi Da Hadisin Karya.

Idan Muka Duba “ATTAUDIH” Sharhin Bukhari Juzu’I Na 5 Shafi Na 329 Shima Maganar Kyanta Yayi Inda Suka Yi Ta Bayanin Ni’imar Da Take Cikin Jima’I Da Masu Kyau Wannan Shine Abinda Suka Nasabtawa Annabi (S.A.W.) Ni Kuma Nace Annabi Bazai Zama Haka Ba.


Shaida Na Daya Ya Fadi Cewa Suhaili Ya Fadi Dalilin Da Yasa Annabi (S.A.W.) Ya Kwace Nana Safiyya A Lokacin In An Kula Nace Nasa Maganar Ibn Hajar Ce Amma Kuma Ya Kaucewa Ibn Hajar Din Saboda A Karatuttukana Na Bada Hujjoji Masu Karfi Da Suke Tabbatar Da Ibn Hajar Na Da Hannu Dumu Dumu A Kan Taba Mutuncin Annabi (S.A.W.) Wannan Yana Cikin Sharhinsa Na Fathul Bari Wannan Ne Yasa Nace Maganar Ibn Hajar Ce Ba Ta Suhaili Ba Ce, Mujalladi Na 7 Shafi Na 582 “FATHUL BARI” Shi Cewa Yayi Suhaili Yace….. Amma Tun Daga Sanda Yace “Kultu” Ya Zama Maganar Ibn Hajar Ce Ba Ta Suhaili Ba. Sai Askalani Ya Cigaba Da Cewa Da Aka Ce Da Ma’aiki Yar Sarkinsu Ce Sai Yaga Bai Kamata Ace An Baiwa Dihya Ba Saboda Akwai Irinsa Da Yawa A Cikin Sahabbai Amma Ita Irin Masu Kyanta Kadanne. Saboda Haka Shaida Ha’intar Kotu Yayi.


Wannan Yana Daga Cikin Abinda Zai Maidashi Fyade Daraja Ta Daya Daga Ibn Umar Juzu’I Na A Cikin Dai Fathul Bari Juzu’I Na Daya Shafi Na 461 Hadisi Na 16146 An Tambayi Ibn Umar Yaya Mutumuin Da Ya Maida Yancin Kuyanga Sadakinta Sai Yace Kamar Mutumin Da Ya Bada Taguwa Hadaya Ne Sannan Ya Dawo Yana Hawanta,

Kuma Duk Sahabbai Sun Hadu Akan Yin Hakan Haramun Ne Banda Abu Huraira Da Anas Ya Ciro Daga Gurinsa, To Da Annabi Yayi Wannan Babu Yadda Za’ayi Ibn Umar Zai Fadi Haka Bayan Dashi Akayi Yakin Khaibar, Sanna Ya Kawo Ibn Ma’ud Shima Ra’ayinsa Kenan A Hadisi Na 16147 Sannan Ibn Sirina Shima Yana Fadar Irin Ta Ibn Umar Sannan Ya Kawo Maganar Ada’u To Duk Wadannan Suna Kara Munin Wannan Abu Idan Da Anyi Zai Zama Darja Ta Daya.

Har Yau Daga Cikin Masu Nemawa Maganar Kwace Wa Mafita Akwai “FATHUL BARI” Mujalladi Na 9 Shafi Na 36 Yace Ibn Jauzi Yace Idan Aka Ce Nasa Annabi Ya Hana Sadakinta Sai Ace Ita Yar Sarkice Ya Kamata A Bata Sadaki Mai Yawa Shi Kuma Shugaba Bashi Dashi Don Haka Ya Maida Yancinta Sadakinta Sanna Abinda Yake Dada Kazanta Wanna Magana Itace Misalin Da Ibn Kasir Yake Fada A Cikin

“BIDAYA WANNIHAYA” Yace Babu Inda Ma’aiki Ya Samu Kudi Irin Wannan Yaki Domin Ta Kudi Kwai Ya Dunga Yi Mujalladi Na 4 Shafi Na 197

Cewa Annabi Yace Da Zubair Bn Awwam Cewa Ka Azabtar Dashi (Baffan Nana Safiyya) Har Sai Kayi Masa Karkaf Zubairu Ya Ringa Kyasta Nasa Wuta A Kirjinsa Har Saida Ransa Ya fita Sannan Ya Bada Kudin Sannan Kuma Ya Sa Aka Kasheshi. Haka Suke A Cikin

“ZADUL MA’AD” Juzu’I Na 2 Shafi Na 707 Suka Ce Annabi (S.A.W.) Yayi Galaba A Kan Dukkan Gonakin Da Dukiyoyinsu Babu Maganar Shiga Musulunci Ko Kiransu Izuwa Ga Allah Sai Maganar Kudi Kawai Yake Musu Wanda Suka Bashi Dukiyarsu Gaba Daya Sai Su Tafi Sai Rigar Wuyansu Wadanda Suka Ki Bada Kudi A Kashe Su.

Idan Muka Hada Wadannan Ruwayoyi Da Suka Bata Sunan Ma’aiki Da Kuma Irinn Tawilin Da Sukayi Cewa Farashin Kudine Yasa Annabi (S.A.W.) Bai Yi Sadaki Ba Karatun Zai Fito A Fili Suna Sun Nasbtawa Annabi (S.A.W.) Son Kudi Da Kuma Mammakon Kudin Domin A Cikin Littafin “MUGAZI” Na Ibn Ishaq Juzu’I Na 2 Shafi Na 673 Za’a Ga Suna Fadin Irin Dukiyarata Da Na Babanta Kuma Akace Ya Azabtar Da Dan Uwan Babanta Ya Kwace Kudinsa


Amma Duk Da Haka Aka Ce Bashi Da Kudin Sadaki Bayan Dukiyar Za’a Iya Kafa Daula Da Ita.


Baihaki A Cikin

“DALAILUN NUBUWA” Mujalladi Na 4 Shafi Na 229 Shi Ma Haka Ya Kawo An Kashe Mata Danuwanta, Mijinta, Babanta Kuma Aka Kwace Komai Nasu

(Amma Bashida Kudin Sadaki).

Wannan Shi Yasa Gwargwadon Iko Na Nake Fito Da Wadannan Munanan Abubuwa Don Kare Ma’aiki (S.A.W.). Kuma Sun San Annabi Ya Saka Ka’aidar Kula Da Mata Da Kuyangi A Hadisin Ahmad Mujalladi Na 32 Shafi Na 19.


Sai Malam Ya Dawo Kan Tuhumominsu Yace Game Da Tuhuma Ta Uku Da Suka Ce A Cikin Karatun Jauful Fara Na 93 Wanda Sukace Nayi Shi Ranar 10/08/2019 To Ba Gaskiya Bane Wannan Ya Nuna Da Ka Suka Rubuta Wannan Caji. Fadinsu Nace Auren Dole Yayi Mata Saboda Yace Yancinta Sadakinta Nayi Batanci Ga Ma’aiki Kuma Wai Ya Saba Da Sashin Shariar Musulunci Na Kano.

To Idan Akayi La’akari Da Kyau Cikin Wanna Tuhuma Tasu Cewa Sukayi Muslim Na Jinginawa, Wanda Wannan Yana Rushe Tuhumarsu Ta Daya, Da Sukace Annabi (S.A.W.) Na Jinginawa, Nan Kuma Sunce Muslim Na Jinginawa Haka Cikin Tuhumarsu Ta Biyu, Don Haka Tuhumarsu Ta Biyu Tana Rushe Tuhumarsu Ta Uku, Don Sun Fada Karara Cewa Muslim Na Jinginawa, Kaga Wannan Ya Rushe Tuhumarsu Ta Biyu.

Kamata Yayi Su Ce Wadannan Kalamai Da Ka Furta Basa Cikin Hadisin 1365 Da 1428 Sai Su Ce


”ANA TUHUMARKA DA KAGE GA MUSLIM”

Maimakon Fadinsu ” Ana Tuhumarka Da 

”KAGE GA ANNABI (S.A.W.)

” Yin Hakan Shi Ne Zai Daidaita Tuhumarsu Ta Daya Da Ta Uku.


Kuma Kamata Yai Tuhumarsu Ta 2 Da Sun Gineta Bisa Adalci Sai Su Ce “Bisa La’akari Da Cewa Wannan Kalmar Ta Kwace Babu Ita A Wannan Hadisi Na Muslim Sai Su Ce


“ANA TUHUMARKA DA YIWA MUSLIMI KAGE”.


Haka Zalika Tuhuma Ta Uku Adalchi Yana Lazimta Nusu Gyarata Sai Su Ce “Wannan Kalma (Auren Dole) (Ta Aureshi In Tana So Ta Yantu) Sai Su Ce


 “BISA LA’AKARI DA CEWA WADANNAN MUNANAN KALAMAN BABU SU A CIKIN WADANNAN HADISAN YA SANYA KAI KA KIRKIRESU DON CIWA MUSLIM ZARAFI MAIMAKON DON KA CIWA MA’AIKI ZARAFI”.


Domin A Cikin Wannnan Karatu Na Jauful Fara Na 93 Wanda Recording Dinsa Yananan A Hannuna Kuma A Shirye Nake In Kunna Duk Sanda Kotu Ta Bani Dama Za’a Ji Har Rantsuwa Nake Da Girman Allah Wadannan Abubuwa Annabi Bai Yiba Kuma Babu Inda Korewa Ta Zama Tabbatarwa Kamar Yadda Babu Inda Zaka Ce Annabi Bai Yi Abuba Kuma Ace Kaci Zarafinsa Da Wannan Abu Da Kace Bai Yiba Kuma , A Gaban Kotu Shaidarsu Na Biyu A Ranar 11/11/2021 Ya Tabbatar Da Yaji Ina Rantsuwa Annabi (S.A.W.)Bai Yiba Wanda Wannan Ya Rushe Tuhuma TA DAYA DA TA BIYU.

Sukana Dai A Shi Na Cewar Basu Ga Wadannan Kalamai Ba A Hadisi 1428 Da 1365 Don Haka Suke Tuhumata Da Rashin Ganinsu Da Kuma Cewar Na Kirkirane Don In Cima Ma’aiki Zarafi To Su Sani Rashin Ganin Wadannan Kalamai Ba Laifina Bane Wannan Yana Komawa Kan Rashin Sanin Su Ko Take Sanin Su Domin Ruwaya Ba Da Lafazi Kawai Ake Yi Ba A Wancan Zaman Na Karanta “AL-GAYA” Sharhin Manzumatul Gaya Shafi Na 52 Karkashin Sharhin Da Na Ambata A Zaman Baya Sakkawiy Yace Bayan Ibnul Jazari Ya Fadi Abu Mafi Inganci Tsakanin Halaccin Yin Ruwaya Da Ma’ana Da Ko Rashin Halarcin Sai Yace Da Banbanci Tsakanin Mai Yin “ISNADI” Da Wanda Yake Yin ”ISTISHHADI” Sai Yace Idan Har Ka Kawo Isnadi To Ka Lazamtu Da Lafazi Amma Idan Kafa Hujja Zakai Sai Ka Aje Isnadi Sai Ka Kawo Hadisi Da Ma’ana, Kuma Da Yardar Allah Zan Fada Da Baka Kuma Zan Kunna Za’aji Wannan Ka’ida Ta Fito Karara Da Zan Fadi Maganar Askalani Da Na Ce Tana Cikin Ju’I Na 7 In An Koma Za’aji Na Kawo Isnadi In An Duba Ruwayar Za’aji Da Lafazi Na Kawota, Kamar Da In An Matsa Za’aji Nace Buhari Ya Ruwaita 371 Za’aji Ban Fadi Isnadi Ba To Za’aji Da Ma’ana Na Kawo Ta Ba Da Lafazi Ba.

Haka Hadisin Da Yake Bin Wannan Nace Buhari Ya Ruwaita A 1490 Za’aji Na Kawo Isnadi A Wannan In An Duba Za’a Ga Da Lafazi Na Zantar Dashi Amma Hadisin Da Ya Biyoshi A Baya Nace Buhari A 2970 Za’a Ji Ban Kawo Isnadiba In An Duba Za’a Ga Da Ma’ana Na Zantar Dashi, Wanda Daga Nanne Za’a Fado Hadisin Dake Cikin Tuhumar Masu Kara Za’aji Nace 1365 Na Kuma Goya Masa Da 1428 To Bisa Ka’idarsu Koda Ma Maganar Isnadi Bata Tasoba To Ka’idar Malaman Hadisi Duk Sanda Hadisi Ya Haura Guda Daya Kuma Ake Zantarwa A Lokaci Daya To Ruwace Da Ma’ana Mudlaqan Wannan Ka’idar In Har Hadisai Sun Wuce 2 Kenan Amma Ni Da Isnadi Da Hadisi Nake Magana. A Duba “ULUMUL HADIS” Na Ibns Salah Lamba Ta 223 Yace Idan Hadisi Ya Wuce Daya Sai A Hade Ma’anoninsa Kawai, Don Haka Karshen Zancen Cewar Basu Gani Ba Ai Shi Maganar Kwace Yazo Karara Da Auren Dole Wanda Sai Mutum Ya San Ma’anar Yancinki Sadakin Ki To Anan Auren Dole Yake Kwanciya Da Ita Kuwa Da Auren Babu Baiko (In Da Anyi) Shine Fyade, To Wannan Magana Ba Nine Na Fara Fada Ba, Haka Yake A Cikin “ALMUFHIM” Juzu’I Na 4 Shafi Na 110 A Karkashin Fadinsa Imamu Malik Da Abu Hanifa Da Muhd Bnl Hasan Da Zufar Sun Ce Sanya Yancin Kuyanga Sadakinta Wannan Yazo A Muslim Hadisi 1365 Wanda Yin Hakan Bai Halatta Haramunne Ta Fuska Biyu


1. Idan Aure Ya Daura A Tana Kasancewarta Baiwa To Wannan Bai Halartaba Saboda Shi Bawa Ko Baiwa Duk Sanda Za’a Ce Musu Suyi Kaza To Hukuncin Wannan Abun A Gurinsu Wajibi Ne Basu Da Zabi Na Iy Ko A’a.

Wanda Anan Ina Jan Hankalin Wannan Kotu In Aka Saurari Bayani Na A Cikin Jauful Fara Na 93 Za’aji Kalmar Ijbar Da Ita Nayi Amfani Wanda Gata A Wannan Nassi Daga Bakin Wadannan Limamai Suka Ce Bawa Umarni A Gareshi A Matsayin Tilas Yake, To ,Ta Yaya Za’a Kaucewa Haka, Shi Ne A Fara Yantata, Sannan A Nemi Yardarta Tunda Bazawara Ce Sannan Sai Waliyyi Sannan Maganar Yin Siga Daga Nanan Sai Ayyana Sadaki Sai Kuma Shaidu Da Nassi Na Alqur’ani Ya Nuna.

To Anan Su Imamu Malik Sun Korewa Annabi Tawayar Da Aka Riskar Masa A Wannan Hadisi Amma Da Zarar Ba Baiko Aka Kwanta Da Ita, To Ya Zama Fyade, Kuma Ina Dogara Da Wadannan Litattafai Wadanda Suka Kore Wadannan Maganganu Irin Yadda Nake Korewa A Yanzu Kamar Haka:

1. “Ikmalul Muallim” Juzu’I Na 4 Shafi Na 592

2. “Attaudih” Juzu’I Na 5 Shafi Na 34

3. “UMDATUL QARI” Juzu’I Na 20 Shafi Na 114

4. “MUHALLA” Juzu’I Na 9 Shafi Na 101


Anan Malam Ya Daga Littafin “Muhalla” Yace Suma Su Imamau Malik Sun Samu Kansu A Cikin Irin Yadda Na Tsinci Kaina A Kan Wadannan Munanan Hadisai Kuma Akan Sun Tsarkake Ma’aiki Kawai Don Babu Yadda Za’ayi Dasu Ne.


A Karshen Karshe Cewar Su Kore Wadannan Maganganu Da Nake Wa Ma’aiki Sun Fadi Sashin Da Suka Dogara Dashi To Ina Tabbatar Musu Ka’aida Ta Musulunci Bata Yadda Da Taba Ran Musulmi Ba Sai Idan Har Ka’idoji Sun Cika Cif Don Haka Ya Zama Dole Su Ambaci Nau’in Batancin Da Ake Zubar Da Jini A Kansu Duba Da Hadisin Buhari Na 4037 Muslim 1801 Ina Nufin Shi Hadisin Da Suka Kafa Sashin Dokar Dashi, Sannan Bayan Nau’in Batancin Sai Kuma Manufar Mutum Duba Da Hadisin Muslim 2747 Ma’aiki Yace 

“Allahumma Anta Abdi Wa Ana Rabbuka”

Manzon Allah Yace

“AHDA’A MIN SHIDDATIL FARHI” Wato Yayi Kuskure Saboda Tsananin Farin Ciki. To Wajibi Ne A Cajin Cewa A Duba Babu Irin Wannan Shubhar Don Tsare Kimar Musulunci. Sannan Sai Sun Tabbata Yin Wannan Furuci Bisa Dadin Rai Yayi Ba Bisa Dole Ba Kamar Misalin Ammaru Bn Yassir Da Aka Tilas Ta Shi Ya Fadi Wannan Magana Wacce Take Sananniya A Cikin Suratun Nahli Aya Ta

106“MAN UKRIHA WA QALBUHU MUDMAINNU BIL IMANI”

Wannan Shi Ne Gini Kan Adalci Magami Ga Kowa Har Wanda Ba Musulmi Ba Saboda Fadin Allah

“WAMA KUNNA MUAZZIBINA HATTA NABASA RASULA”.

Sai Kuma Tuhuma Ta Hudu Wacce Cikin Yardar Allah Zan Zo Kanta A Cikin Zama Na Gaba


Lauyan Malam: Mun Bawa Kotu Litattafai 54 Don Ta Duba Sannan Muna Neman Wannan Kotu Mai Albarka Da Ta Bada Belin Wanda Ake Tuhuma Duba Da Irin Girmansa Da Irin Nauyin Da Yake Kansa Na Wadanda Suke Rayuwa Karkashinsa Sannan Duk Wasu Sharruda Da Zata Gindaya Zai Cikasu.


Lawyan Gwamnati: Duba Da Irin Cajin Da Ake Wa Wanda Ake Zargi Caji Ne Wanda Ba A Bada Beli


Lawyan Malam:

Duba Da Tsarin Mulkin Nigeria Kowane Mutum Ba Shida Laifi Sai Har In Kotu Ta Tabbatar Da Lefin Saboda Haka Malam Ba Mai Laifi Bane Har Sai In Kotu Ta Tabbatar Saboda Haka Muke Neman Kotu Ta Bada Belinsa.


AlkalI: Kotu Zata Duba Dukkan Maganganun Bangarorin Sannan A Zama Na Gaba  Zata Fadi Ra’ayinta Akan Belin.


Daga Nan Sai Alkali Ibrahim Sarki Yala  Saka Ranar 31/3/2022 Domin Cigaba Da Wannan Shari’a.

Comments