Shari'ar Sheikh Abduljabbar ,malamin yazoda littattafai 27 da suka halatta fassarar hadisi da ma'ana


 Shari'ar Sheikh Abdujabbar: Malamin ya zo da littafai 27 da suka halatta fassarar Hadisi da ma'ana.


Fatima Abdullahi Bintulhuda


A Safiyar yau ne aka cigaba da zaman shari'ar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Abdujabbar Kabara wanda aka gabatar a babbar kotun shari'ar Muslunci dake zaman ta a kofar kudu. 


A zaman na yau, Malamin ya bayyana a kotu tare da littafai da dama domin shiga kariya bisa tuhumar da ake masa ta furta kalaman ɓatanci da kuma tunzuri. 


Kafin fara gabatar da kariya, Malamin yayi rantsuwa da Alqur'ani mai girma cewa zai fadi gaskiya, wannan shine karo na farko da wani daga shedu a shari'ar yayi rantsuwa da Alqur'ani cewa zai fadi gaskiya. 


Malam Abdujabbar ya fito da littafai guda 27 da ya bayyana su a matsayin shedu ababen nunawa a cikin shari'ar, littafan duka sunyi bayanin halaccin fassara hadisi da ma'ana ba da lafazi ba. 


Daga ciki akwai littafin Almuhaddisul Fasil Bainar Rawiy Wal Waqiy na Ramahurzi shafi na 551, ya kawo cewa:


''An tambayi Hasanul Basari cewa, Muna jin kana faɗar hadisi da ma'ana bada lafazi ba, sai yace da su babu laifi a cikin yin hakan matukar ba a halatta halal bane ko a haramta haram''


Malamin ya kara da kawo fadin Ibn Sirina da yace ''Mukan ji hadisi daga mutum 10 amma kowanne da lafazin sa daban'', ya kuma bayyana cewa babu laifi a hakan. Ya kara da ra'ayin Sufyan Athauriy da na ibn Abbas da ya ce ya zo a shafi na 657 cikin littafin na Ramahurzi cewa: 


''Sha'abi ya tambaye shi; Kana gaya mana hadisi yau, gobe kuma muji ka canza lafazi, dai yace ba laifi indai ba a wajen halatta halal bane ko haramta haram''. 


Mai Shari'a ya bukaci Malamin ta tsagaita a littafai 11, har ya bada misalin cewa ko a jarabawa ce mutum yaci 11 cikin 27 ya wuce. 


Malamin a cikin kariyar da yake yi ya bayyana kuskuren da ke cikin tuhuma ta farko da aka shigar kansa, inda ya bayyana cewa ranar da suka rubuta cewa yayi wannan karatun ba gaskiya bane. Sannan kuma ya bayyana wa kotu cewa da yiwuwar rashin sani ko take sani a wajen masu shigar da karar, domin basu bi matakin da addini ya shimfida wajen tabbatar da Tuhumar da ake hukuncin kisa akan mutum ba. 


Sannan malamin ya yi bayani akan auren Nana Safiyya da yake cikin tuhumar da batun sanya yancin ta a sadakin inda, ya kawo maganganun Imam Shafi'i da na alqadiy Iyadh da suke kore wa Annabi SAWA aikata hakan kaman yadda Shima malamin ya ke ikirari.


Kotu ta tafi hutum minti 30 kafin a dawo a dora daga inda aka tsaya. 


Jarida Radio

3/3/22

Comments