MEYASA BAMU BAR SHEIKH ABDULJABBAR KABARA BA ?
Dayawan mutane sun yi mamakin meyasa Almajiran Sheikh Abduljabbar kabara basu barshiba. faruwan wannan waki'ar?
bugu da kari ma sai imani da tafiyar da wasu suka kara yi du da Cewa ga zargin da akewa malamin nasu ga kuma halin da yake ciki
To abin da mutane wasu suka gaza fahimta shine Alhamdulillah ba alfahari ba maganar gaskia duk Wanda ka gani gaban mallam Abduljabbar daidai gwargwado ba jahili bane kuma yana da hankali ba mahaukaci bane , kuma shiya zo da kan shi ba jawo shi mallam Abduljabbar yayi ba ba kuma a gidan TV sunnah ko redio yaji muryar shi ba
Tsawan shekara sama da biyu ana Karatun Jauful Farah Wanda sheikh Abduljabbar kabara ya ke gabatarwa , sannan shekara biyu baya yayi Rayuwa bayan mutuwa Wanda a cikin wadan nan Karatukan ne aka datsi wasu gurare aka jona aka sakarwa duniya cewa yau ga sheikh Abduljabbar kabara ya zagi Annabi saw dan cimma wata manufa tasu ta ganin bayan Sheikh Abduljabbar din
Sunyi tsammanin taron mabiyan sa zasu watse ne su bar shi shi kadai to sai Allah yasa mabiyan nasa sun San me dukkanin abin dake faruwa Kana kuma Karatun sheikh Abduljabbar din ba Wanda basuji ba ba Wanda basu dashi , ga duk dalibin sheikh Abduljabbar kabara yasan awanna karatu ne aka Ciro wadan nan maganganun aka jona kuma tuni ya saurara ya wuce gurin yayin da aka kawo mai second 30 ko 40 aka ce ga malamin Ku fa yace da Annabi kaza shi yana ji yasan inda aka Ciro maganar kuma nayi imanin saiya kare maganar bama sheikh Abduljabbar ba dan haka hankalin sa bazai tashi ba domin yasan karya ce
Sun yi kokarin kunya ta shi gurin Mukabala ta yadda zasuyi masa daurin talala ta inda bazai iya taba kare kan shi ba a idon duniya , suka yaudare shi da yadda tsarin mukabalar zai kasance sai bayan ya isa gun suka sanar dashi an canza tsarin Wanda a lokacin suka so yace bazai zaman ba domin su kama shi suce yaji tsoro , to kuma daya amince zai zauna din sai suka zabi yan jaridun da suke so su zasu shiga gun sannan sai abin da suke so shi zasu yada a haka akai zaman jaridu sukai ta wallafa karya kuma suka dauko kasurgumin dan Izala wai shine alkalin Mukabalan
Alokacin babu dalibin sheikh Abduljabbar din da hankalin sa bai tashi ba magana daya sheikh Abduljabbar yayi bayan Mukabala ta kwantar mana da zukata
Duk Wanda kasan yana bin sheikh Abduljabbar kabara tun daga Mukadimma zuwa Jauful Farah wallahi bazai bar shi ba dan wannan waki'ar ta faru domin yasan shiri ne irin na magautan sa da dadden shiri
Dan haka mu diban sheikh Abduljabbar kabara a shirye muke mu bar shi idan aka tabbatar mana da hadisan daya Kore gaskia ne kuma ga fiqhun su a musulinci
Rida'ul kabeer
Sakaratul mautt
Shiga Gidan Ummu HARAM
Hadisin Fitsari a tsaye
Hadisin iyayen Ma'aki saw
Hadisin Annabi Nada shaidan
Wadan hadisan Da Sheikh Abduljabbar kabara ya Kore su a hakkin ma'aiki saw wallahi in su kadai ya Kore zuwan sa duniya kawo yau Wallahi har duniya ta tashi bazan daina kaunar Sheikh Abduljabbar
Ina Kaunar sheikh Abduljabbar kabara Fiye da wadda nake masa a 2020.
Comments
Post a Comment