KIRARINDA SHEIKH ABDULJABBAR
YAKEYIWA ANNABI SAW.KAMARDA KOWA YASANSU.
"Dukkanin yabonmu da godiyarmu su taho gunsa mafi yabo
Ɗan Abdu mai babban rabo
Baban Muɗallabi
Jikan Muɗallabi
Ja gaba Manzonmu mai cetonmu
Ɗa tilo maras tamka, uban ɗakin dukkanin Annabawa
Shugaba ga Mala'iku
Na Khadijah
Jikan Nuhu
Goyon Amina 'yar Wahabu
Sarkin muminai
Ɗa mai biyayya
Ɗa abun bi
Ɗan halas mai kyan hali, mai kyan halitta
Ɗa fari, mai kyan kulawa, mai kala, wane dala
Wane dalandalami na gogaggar azurfa mai kala
Goshinsa das
Fuskarsa tas
Hancinsa ɗas
Ga kyan hakora jeraras
Gemunsa ya cika, yayi lub-lub, yayi daidai, yayi kyau, ba ya kama da na bunsurai.
Ƙyallinsa na haskakawa idan yayi murmushi
Ga kyan wushirya
Ga kalan lebensa ja zur
Ga idonsa gada-gada tamkar farin nono
Farinsu kal, bakinsu ƙirin, girarsa a lanƙwashe
Gashin Muhammadu [S] yafi izga
Ƙyalli da sheƙi
Walwalin fuskarsa yafi matsoƙaci
Harshensa ja
Farchensa ja da fari kamar dinariya
Naman jikinsa a ɗaure
Shi ko yana dire
Bai zanƙale a tsawo ba
Bai diƙis-diƙis a dirinsa ba
Maganarsa tamkar yayyafin da yake zuba
Lafazin sa yafi zuma daɗi idan ya fit da shi
Kyawun sa shine kyau
Gare shi ka fit da dukkan kyau ga shi ɗan Abdu
Baban Faɗima, na Khadijah
Babu kamar ya kai ﷺ"
~Dr Sheikh Abduljabbar Kabara (H).
©Fatimiyya Alawuyya tv
Comments
Post a Comment