Zaman kotu na 3/2/2022


 Kotu ta bada umarnin a dawo da sheda na farko dan sake yi masa tambayoyi.


Nasiruddeen Abdullahi


A safiyar yau Alhamis ne aka cigaba da gabatar da Shari'ar malamin addinin musulunci Sheikh Abdujabbar Kabara wanda aka gurfanar dashi a gaban kotun shari'ar Muslunci dake zaman ta a kofar kudu, a jihar Kano.


A zaman na yau, Barista A.O Mohammed SAN ne ya jagorance lawyoyin da suke kare Malam Abdujabbar, inda Barista Sa'ida Shu'aibu SAN ya jagoranci tawagar lawyoyin masu gabatar da kara. 


A zaman na yau, Lawyoyin Malamin sun nemi a dawo musu da sheda na farko domin sake yi masa tambayoyi, sai dai ɓangaren da suke gabatar da ƙara sunyi suka akan wannan roko inda suka nuna cewa hakan ya saɓa da ka'ida, kuma ɓata lokacin kotu ne. 


''Wannan sheda na daya an sallameshi, a yanzu haka yana makarantar su a jamhuriyar Nijar, a tsari na Shari'a Allah madaukakin sarki ya hana wahalar da sheda'' inji Sa'ida Shu'aibu SAN


Ya kara da cewa "Idan muka duba dokar ACJL 2019 sashe na 258, ya nuna cewar wajibi a kawo kwararan dalilai da zasu sa a yiwa sheda kiranye, in akwai bata lokaci koda an kawo kwararan dalilai, to kotu baza ta yarda ba. Sati 4 da aka bayar ya nuna bata lokaci ne hakan daga gare su.''


A nashi martanin, Barista A. O Mohammed SAN yace rokon da yayi kankanin abu ne suka maida shi babba, kuma ba haka dokar ta ce ba.


''sashe na 258 ACJL ya bada dama a dawo da shedar a kowanne lokaci idan kotu taga dama da kanta, ko kuma duk lokacin da wani daga yan Shari'a yayi nema na a dawo da shi'' inji A.O Mohammed SAN


Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola bayan ya nazarci hujjojin dukkan ɓangarorin, ya bayyana cewa wannan roko bai saɓa da doka ba. 


''Wannan roko bai saɓa da doka ba, shi yafi kama da adalci, sashe na 258 ACJL ya karfafe su ne da cewa a kowane lokaci, alƙali ko ɗan Shari'a yayi roko a dawo da sheda, za a iya dawo dashi. Nabi ƙa'ida Kuma na kwatanta adalci'' inji mai Shari'a. 


Ya bada umarnin a dawo da shedar a zama na gaba dan sake yi masa tambayoyi a Shari'ar. 


A ƙarshe ya ɗage shari'ar zuwa 17/2/2022 dan cigaba da Shari'ar.


Jarida Radio

3/2/22

Comments