SU AUNAWA DA HANKALI A MAKARANTAR SU GURIN KOYARWA !!!
Daga Daya Daga cikin daliban sheikh Abduljabbar.
Dr. Ahmad Abubakar Gumi (R) Yana so sai ya tabbatar da Hadisin dake cewa Annabi (saw) yana Kallon mãtã, alhãlin yana cikin sahabban sa, har ma yana yin sha'awarsu.
Dr. Abduljabbar Nasiru Kabara (R) Kuma, yana ƙaryata Hadisin . A cikin su wane ne yake tsabtace Manzon Allah (saw) ?????
Dr. Abduljabbar (H) yana cewa, du Hadisin da ya saba da hankali, ko ya ci karo da ƙur'ãni, ko yake tauye darajar Annabi saw, ko yake bãyuwa ga danganta ƙarya ga Annabi,to wannan Hadisin za mu zubar da shi a cikin kwandon shara , ba tare da kula da kowaye ya ruwaito shi ba.
Shakka babu, Hadisin da zan kawo , in bai haɗa duka daga waɗannan abubuwa huɗu ba ,to tabbas ya haɗa (3) daga cikin su . Wato :
(1) Sabawa da hankali
(2) Cin karo da Ƙur'ani
(3) Tauye darajar Annabi SAW.
(4) Bãyuwa ga danganta ƙarya ga Annabi (saw)
Wannan Hadisi ya zo a Sahih Muslim , da kuma cikin Mu'jamulkhabir Na Ɗabarani cewa :
Annabi (saw) na zaune da Sahabbansa sai ya ga wata mace, sai ya yi sha'awarta, sai ya tashi ya shiga gida, ya sami matarsa Nana Zainab Bintu Jahshin , ya biya buƙatarsa da ita. Sannan ya fito cikin Sahabbansa yana ce da su, duk wanda ya ga wata mace kuma ya yi sha'awarta to ya koma wa iyalinsa, ya biya buƙatarsa.
١٣٢- حدثنا أبو مسلم الكشي ، ثنا مسلم بن إبراهيم ، ثنا هاشم الدستوائى ، ثنا أبو الزبير ، عن جابر أن النبي (ص) رأى إمرأة فأعجبته، فدخل علي زينب بنت جحش فقضي حاجته منها، ثم خرج فقال : " إن المرأة تقبل صورة الشيطان وتدبر في صورة الشيطان، فمن وجد ذالك فليأت أهله فإنه يضمر ما في نفسه. المعجم الكبير للطبراني ٢٤٨٢٩/٢٦٦١٥.
A nagarta ta ɗabi'a, malamin unguwarku ba zai zauna da almajiransa ba, yana ƙura wa mata ido har yana yin sha'awarsu balle kuma Manzon Allah (saw).
Shi ne fa Annabin da Allah (swt) Ya saukar wa da wannan ÃYAR.
قل للمؤمنين يغضون من أبصارهم ويحفظوا فروجهم، ذالك أزكي لهم إن الله خبير بما يصنعون . سورة النور ((٣٠))
Ka ce da muminai maza, su runtse daga ganin su, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne ma fi tsarki agare su. Lalle ne Allah, Maiƙididdige wa Ne ga abin da suke sana'antawa.
Runtse ido, na daga abin da Allah (swt) Ya ce : (( ذالك أزكي لهم )) . Amma abin ban haushi, wancan Hadisi ya ce , wai Annabi (saw) buɗe idonsa yake yi yana kallon mata ,wai kuma har yana sha'awar su . (SUBHANALLAHI)
Sun ruwaici wani Hadisi a Sahihul Bukhari ( kitabunnikãh ) cewa Annabi (saw) ya ce ," WALLAHI NI NÃ FI KU JIN TSORON ALLAH "
باب الترغيب في النكاح لقوله تعالي (( فانكحوا ما طاب لكم من النساء ..))
................. والله إني لأخشاكم لله وأتقاكم له......................
To wallahi, tun da Allah (swt) ya ce , a runtse ido daga kallon mata, Annabi (saw) ba zai kalle su ba sam. Kamar dai yadda wancan Hadisi ya nuna.
TO GA HADISIN DAKE NUNA WANCAN HADISIN ƘARYA CE AKA YI WA ANNABI (SAW). SHI MA ANNABI (SAW) YA HANA KALLON MATA BISA SHARAƊIN ZAMAN HANYA.
MU DUBI SAHIHUL BUKHARI HADISI NA
2465, DA KUMA HADISI NA 6229.
باب أَفْنِيَةِ الدُّورِ وَالْجُلُوسِ فِيهَا وَالْجُلُوسِ عَلَى الصُّعُدَاتِ : كتاب المظالم.
«2465» حَدَّثَنَا مُعَاذُ بْنُ فَضَالَةَ حَدَّثَنَا أَبُو عُمَرَ حَفْصُ بْنُ مَيْسَرَةَ عَنْ زَيْدِ بْنِ أَسْلَمَ عَنْ عَطَاءِ بْنِ يَسَارٍ عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((إِيَّاكُمْ وَالْجُلُوسَ عَلَى الطُّرُقَاتِ)). فَقَالُوا مَا لَنَا بُدٌّ، إِنَّمَا هِيَ مَجَالِسُنَا نَتَحَدَّثُ فِيهَا. قَالَ: ((فَإِذَا أَبَيْتُمْ إِلاَّ الْمَجَالِسَ فَأَعْطُوا الطَّرِيقَ حَقَّهَا)) قَالُوا وَمَا حَقُّ الطَّرِيقِ قَالَ: ((غَضُّ الْبَصَرِ، وَكَفُّ الأَذَى، وَرَدُّ السَّلاَمِ، وَأَمْرٌ بِالْمَعْرُوفِ، وَنَهْيٌ عَنِ الْمُنْكَرِ)).
Annabi (saw) ya ce nã hane ku daga zama kan hanyoyi. Sai Sahabbai suka ce,ai babu makawa sai mun zauna saboda gurin firar mu ne. Sai Annabi (saw) ya ce to ku bai wa hanyar sharaɗin ta . Suka ce mene ne sharaɗin zaman hanyar ? Sai Annabi (saw) ya ce :
(1) KAUDA IDO DAGA KALLON MATA,
(2) KAUDA WANI ABU MAI CUTARWA
(3) MAIDA SALLAMA(4) UMARNI DA AIKI MAI KYAU, DA HANI DAGA MUMMUNA.
To yaushe Annabi (saw) za a ce wai yana ƙura wa mata ido, kuma wai har yana sha'awarsu. Kuma yana faɗa wa Sahabban sa yadda za su yi idan haka ta faru da su,
Kenan yana ba su damar kallon matan da kuma, nuna ma su mafita, idan har sun yi sha'wa gurin kallon matan. Bayan kuma Ƙur'ani da shi kanshi Annabin saw, ya hana Kallon matan balle har a yi sha'awarsu ? Da wannan ne muke ganin cewa
Wancan Hadisi yana zubar wa da Annabi (saw) ƙimarsa, kuma yana ƙaryata Alƙur'ani mai girma, kuma yana danganta ƙarya ga Annabi (saw) , sannan kuma ya saba da hankali. Saboda haka sam ba ma tare da shi. Ƙofar gyara na buɗe ga mai ganin fahimtarmu ba dai dai ba ce.
Ina taya Al ummar musulmin duniya murnan zagayowar watanda aka haifi annabi saw.
©Fatimiyya Alawuyya Tv
Comments
Post a Comment