ANFAKEDA GUZUMA..

 ANFAKE DA GUZUMA!!

AN FAKE DA GUZUMA...


TSOKACI AKAN RIWAYAR DA YARON DAMO YA FAKE DA ITA YA ZAGI IMAM ALIY (AS)


____

Wata magana ce na gani cikin abinda na bibiya bayan na dan leqa sahar Facebook. Post ne wanda daya daga cikin yaran Damo yayi da yake nuna cin mutuncin Imam Aliy (as) da kuma dansa Sayyiduna Alhasan (as). 


To Amma a gurguje zan dan yi tsokaci akan wannan rubutu na Alnafahat Annasibiy kuma zan qalubalance shi da ya fito mu tattauna dashi cikin mutuntawa. Ga abinda Alnafahat Annasibiy yace:


____

Annabi S A W Ya Yi Busharar Cewa Jikan Na Sa Al-hasan Shi Zai Yi Sulhu Tsakanin Wasu Runduna Biyu Ta Musulmi Da Fadin Sa Cewa:

ﺇﻥ ﺍﺑﻨﻲ ﻫﺬﺍ ﺳﻴﺪ ﻟﻌﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺼﻠﻪ ﺑﻪ ﺑﻴﻦ ﻓﺌﺘﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ.

Kuma Abinda Ya Faru Kenan Saboda Duk Wanda Ya Karanta Wani Abu Koda Kadan Ne A Cikin Sirar Sa Mai Cike Da Haske Da Albarka Zai Fahimci Sam Babu Fitina Ko Kadan A Cikin Halittar Ima'm Al-hasan.

____


Amsa:


(1) Ita wannan riwaya da take fadin sulhu tsakannin tawaga biyu na musulmai ta sanadin Imam Alhasan (as) da malaman hadisi suka riwaito ance a kan mimbari Annabi (saw) ya hau ya fadeta kamar yadda Abu Bakrah yace: 


ﺳﻤﻌﺖ اﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ اﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، (ﻋﻠﻰ اﻟﻤﻨﺒﺮ ﻭاﻟﺤﺴﻦ ﺇﻟﻰ ﺟﻨﺒﻪ، ﻳﻨﻈﺮ ﺇﻟﻰ اﻟﻨﺎﺱ ﻣﺮﺓ ﻭﺇﻟﻴﻪ ﻣﺮﺓ، ﻭﻳﻘﻮﻝ:)


 "اﺑﻨﻲ ﻫﺬا ﺳﻴﺪ، ﻭﻟﻌﻞ اﻟﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﺼﻠﺢ ﺑﻪ ﺑﻴﻦ ﻓﺌﺘﻴﻦ ﻣﻦ اﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ"


To sai dai duk da haka, hatta shi Imam Alhasan din da sauran sahabban Annabi (saw) da akace anyi a gabansu da mabiyan Sayyiduna Alhasan (as) basu san da ita ba kafin wannan waqi'ar.


(2) Riwayace da take cikin Bukhari da tazo a guri-guri, amma dai duk da haka ta gun mutum daya kacal, ga isnadin hadisin kamar haka:


ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺻﺪﻗﺔ، ﺣﺪﺛﻨﺎ اﺑﻦ ﻋﻴﻴﻨﺔ، ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﻣﻮﺳﻰ، (ﻋﻦ اﻟﺤﺴﻦ، ﺳﻤﻊ ﺃﺑﺎ ﺑﻜﺮﺓ.)


To anan ina qalubalantar shi Alnafahat cewa, Alhasan din nan da yace ko Bukhari yace ya ji wannan hadisi daga Abu Bakrah, to ina so ya tabbatar mani da sama'in Hasan daga Abu Bakrah, duk da Bukhari ya nuna yaji din kamar yadda yace:


ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪ اﻟﻠﻪ: " ﻗﺎﻝ ﻟﻲ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ اﻟﻠﻪ: ﺇﻧﻤﺎ ﺛﺒﺖ ﻟﻨﺎ ﺳﻤﺎﻉ اﻟﺤﺴﻦ ﻣﻦ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮﺓ، ﺑﻬﺬا اﻟﺤﺪﻳﺚ " 


To ni dai ban gamsu ba, kuma na ce Alhasan bai ji ba daga gurin Abu Bakrah ba. Amma ga dalilaina kamar haka:


____

(a) Mu duba sharhin Sahiyhul Bukhari, mai suna Umdatul Qãri juz'i na 1 shafi na 220, ga abinda Badaruddiyn Al'ayniy ya fada:


ﻭﺃﻧﻜﺮ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ ﻭاﻟﺪاﺭﻗﻄﻨﻲ ﺳﻤﺎﻉ اﻟﺤﺴﻦ ﻣﻦ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮﺓ.


Yahya bn Ma'iyn da Addaraqutniy sun musa sama'in Alhasan daga Abu Bakrah, wato suna nufin Alhasan bai ji hadisi daga Abu Bakrah ba.


(b) Al'ayniy yace: Addaraqutniy yace, tsakanin Alhasan da Abu Bakrah akwai mutum guda wato shine Al'ahnafu.


ﻗﺎﻝ اﻟﺪاﺭﻗﻄﻨﻲ: ﺑﻴﻨﻬﻤﺎ اﻷﺣﻨﻒ


(3) Duk Wanda ya karanta ko da dan wani Abu na tarihin yadda aka yi wannan sulhu tsakanin tawaga biyun nan, to lallai za ya ji kunyar kiran Mu'awiyah mutumin kirki matuqar yana da kunya kamar yadda bayanai zasu zo in sha Allah cikin wannan tattaunawar.


(4) Yanzu kenan Alnafahat Annasibiy a gurinka shi Imam Aliy (as) da ya yaqi su Mu'awiyah shine a halittarsa akwai fitina koko dawa kake yi ? 


Ala ayyi hal, wannan hadisin bai tabbata Annabi (saw) ne ya fada ba saboda wadannan Dalilan da wasu da zasu zo nan gaba. Sai Alnafahat yace:


____

Tun A Farkon Khilafar Ima'm Ali ( A S ) Da Ya Ce Zai Bar Madina Ya Tafi Iraq Sai Da Al-hasan Ya Bashi Shawarar Cewa

Duk Da Cewa Ya Fita Yaqi Jamal Da Siffin Amma Sam Bada Sonsa Ba, Har Sai Da Ta Kai Ya Wajjahar Da Nasihohi Ga Ima'm Ali A Kan Kada Yaqin Ya Faru, Amma Ina! Azal Ta Riga Ta Rigaya Sai Da Abinda Allah Ya Nufa Ya Faru Ya Faru, Duka Allah Ya Yi Gafara A Gare Su.

____


Amsa:


(a) Kawo mani Nasiyhohin da shi Sayyiduna Alhasan (as) din yayi zuwa ga Mahaifin nasa Imam Aliy (as) akan cewa kar ya fita yaqin Jamal da Siffiyn din na gani tare da marja'in da zan duba naga maganar ?


(b) Shin tsakanin Aliy (as) da wadanda ya yaqa a Jamal da kuma wadanda ya yaqa a Siffiyn waye yake akan gaskiya sannan waye yake akan kuskure? 


(c) Yanzu wannan yaqe-yaqe guda biyu da nasiyhar da kace Sayyiduna Alhasan (as) yayi ga Imam Aliy (as) sune suka baka damar kiransa fitinanne?


____

Muhsin Dass

Almajirin Maulaya Saiful Jabbar

Almajirin Dr. Abduljabbar Kabara (rta) 

Fatimiyya Alawuyya TV

Comments