ANNABINMU DABAN YAKE

 ANNABINMU DABAN YAKE

            ANNABINMU DABAN YAKE

بسم الله الرحمن الرحيم والصلاة والسلام على سيدنا محمد أصدق وادالعميد سيدنا ونبينا وحبيبنا وشفيعنا ومولانا محمد صلى الله عليه وسلم


Yan uwa barkanmu da warka fatan kowa yana cikin koshin lfy Allah yasa haka insha Allah yauma zamu dora daga yadda muka tsaya akan bayanin siffofi da mu A mala dakuma yadda manzon Allah s a w yake abubuwa na rayuwarsa duba da cewa komai na manzon Allah s a w abin koyine garemu


A yau insha Allah zamuyi bayani ko ince zamuyi rubutu a kan kaya na manzon Allah ko ince sanya kaya na manzon Allah s a w  shine باب ما جاء في لباس رسول الله صلى الله عليه وسلم 


Wannan babi zaiyi bayanine akan nau i na kayan da manzon Allah s a w yake sawa wanne kala yake sawa kokuma wanne yafi sawa   dakuma anfanin sanin hakane do min muyi kokari muma muna kwatan tawa in har munji akwai irin wanda zamu samu a wannan lokaci   bayan haka babu shakka manzon Allah s a w akwai irin kayan da yakesakawa 


Babu shakka munsani wannan sutura da Allah yamana ni imace babba daga cikin ni imar sanya tufafi akwai rufe al aura sanna kuma kaya ado ne ga dan adam  kalmar لباس yana zuwa da ma anoni da dama A cikin qur ani misali وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا)  kagani anan Allah sai yace sai muka sanya dare yazama sutura gare ku


A wani lokacin kuma sai Allah yakira iyalanka da cewa sutura ne gareka aya a cikin qur ani  {هُنَّ لِبَاسٌ لَكُمْ وَأَنْتُمْ لِبَاسٌ لَهُنَّ}  kaga suna rufamaka asiri kaima kana rufamusu asiri  sannan tana zuwa da ma anar lullubewa    ﴿ وَضَرَبَ اللَّهُ مَثَلًا قَرْيَةً كَانَتْ آمِنَةً مُطْمَئِنَّةً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدًا مِنْ كُلِّ مَكَانٍ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ اللَّهِ فَأَذَاقَهَا اللَّهُ لِبَاسَ الْجُوعِ وَالْخَوْفِ  sannan in muka kara dubawa acikin qur ani zamu ji Allah nacewa.

يَا بَنِي آدَمَ قَدْ أَنزَلْنَا عَلَيْكُمْ لِبَاسًا يُوَارِي سَوْآتِكُمْ وَرِيشًا ۖ وَلِبَاسُ التَّقْوَىٰ Allah yake cewa lalle munsaukarmuku da tufafi duba ga wannan ayar in muka duba babanmu adamu lokacin da sukaci wannan ita ciyar miya faru  sai Allah ya ciremu su sutura gaba  bayan sunzo duniya sai Allah yace yaku yan adam mu saukar muku da tufafi sai Allah ya sutur tasu  sannanan kuma akwai لباس  تقواna tsoron Allah ke  sannan dai in muka kara dubawa cin qur anin zamuga yadda Allah yake cewa

وَجَعَلَ لَكُمْ سَرَابِيلَ تَقِيكُمُ الْحَرَّ وَسَرَابِيلَ تَقِيكُم بَأْسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُتِمُّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تُسْلِمُونَ Allah yake cewa kamar haka muka sanya muku kaya  sutura ke nan da zai kareku daga rana dakuma gurin yaki kamar sulke kenan babu shakka kalmar لباس tana da yawaa a cikin qur ani sai dai in ta  kaita kawai


Babu shakka malamai sun hadu a kan cewa  dikkan sutura halal ne sai wanda shari a ta hana da kuma abin ci da abin sha  dik halal ne har sai in shari a ta haka dalili kuwa ne  

 :كلوا واشربوا ولا تسرفوا izuwa karshe  yace kuci kusha kuyi sutura sannan kar kuyi al mubaxxaranci  kuyi komai dai dai


Insha Allah zan ta kaita anan duba da cewa na danyi dogon bayani kar kashin kalma ta باب ما جاء في لباس رسول الله صلى الله insha Allah rubutu nagaba kai tsaye zan tashi a kan hadisan da suke magana akan haka allamdulillah


Signing

Mai nana fadima


Comments