FASSARAN BAITUKANDA MAULANA AMIRUL WA'IZINA AKAFITAR

 FASSARAN BAITUKANDA MAULANA AMIRUL WA'IZINA AKAFITAR

FASSARAR BAITIKAN 'IBTIHALI' DA AMIRUL WA'IZINA(H) YAYI A GIDAN KURKUKU RANAR ALHAMIS 30/9/2021


FASSARAR SHIMFIDA:

Bayan bismillah da godia ga Allah da Salati ga Shugaba da alayensa masu girma, Malam Yace:


Yana daga mafi girman ni'imar da Allah zaiwa bawa ya cancantar dashi baiwarsa kuma ya sanya shi muhallin yi masa da'a. Ina gode masa bisa baiwar dayai mini ya kimsa min wadannan baitoci na "ibtihaali" gareshi yayin da nake tsaka da karanta littafinsa mai girma (Alqur'ani), inda nazo dai dai aya ta 62 cikin Suratun_naml 


أَمَّن يُجِيبُ ٱلْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ ٱلسُّوٓءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَآءَ ٱلْأَرْضِ ۗ أَءِلَٰهٌ مَّعَ ٱللَّهِ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ


Sai Allah yai min budin wadannan baitoci, saina dinga rokonsa dasu. 

Ina fatan yan uwa masoya suma zasu karanta su da adadi masu yawa don albarkarsu ta game kuma a sami ijaba, domin Allah ta'ala shine me datarwa, madalla da mai amsa rokon bayi. 


FASSARAR BAITIKA:

-Ya rayayyen Sarki, Tsayayyen dabai jingina da komai ba (mara kini mara kishiya) ya Ma'abocin daukaka, 


Ma'abocin kyauta da karamci, ya (Sarki) Mafi Adalchi


- Babu wani mai amsa addu'a sai Kai,  saboda haka kai kadai ni nake roko.


- Kaine Ubangijina, kaine kasan abinda shine kubutata da zarar kayi shi. 


-Shin gajiyayye ya dogara ga dabararsa? 

Bari dai tsayuwarsa kofarka shine yafi. 


-Ina rokonka da ludufinka kayi min kyauta, kayi min ya Sarkin da bashi da Farko. 


-Ka sanya Hijabin Ludufinka a gareni a dukkan abu mai hawa ko mai gangarowa a gareni! 


-Ka sanya min mafita a abinda ya kuntata min, ka yassare hanyar alkhairi a gareni na shigeta. 


وَآخِرُ دَعْوَاهُمْ أَنِ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ


Da Alqalamin: Khadimi a kofar jagororinmu Ahlul Kisaa'i(AS), wato Amirul Wa'iziyna Sheikh Dr. Abduljabbar Kabara(H)!


____

Tambihi: Kar a manta kwana 1 da yin wannan ibtihali asirin wanda ya daddatsewa Malam karatu ya fara tonuwa, don haka yan uwa sai a bada himma. 


Wassalamu warrahmatu alaikum

2/10/2021.

Fatimiyya Alawuyya TV

Comments