INA MASU CEWA YAN ASHABULKAHFI SUNA FASSARA HADISAI DASON RAI?

 INA MASU ZAGIN YAN ASHABULKAHFI

 MASU ZAGIN ( 'YAN AS'HABULKAHFI )  CEWA SUNA FASSARAR HADISAI A BISA KUSKURE, DA KUMA SON RAN SU, KU ZO MUNA KIRAN KU, DON GIRMAN ALLAH !


 Saifullahi Murtala Jibia


Ban taba ganin inda zagi ya zama sanadin shiriyar wani ba, ko cin mutunci, kuma wai da sunan addini. Yaushe za a kawo maka hadisi, a faɗa maka sunan littafin da yake ciki,kuma tare da juzi'in littafin da shafinsa da lambar Hadisin, bayan wannan kuma a fassara maka Ɗan'uwa, amma da zarar ka buɗa baki sai ka yi zagi,ka ce an yi fassara ta jahilci ko ta son rai, idan aka ce kuma zo ka fassara , sai a nema ka a rasa  ?


ƊAN'UWA: Dubi bisa hanyar da Allah (swt) Ya ɗora Annabi (saw) idan zai yi (da'awa) wato kira i zuwa addinin Islama 

  


ادْعُ إِلِى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ وَجَادِلْهُم بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ . ( سورة النحل ١٢٥)


Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azī mai kyau, kuma ka yi jayayya da su da magana wadda take ma fi kyau, lalle ne Ubangijin ka Shi Ne Ma fi sani ga wanda ya bace daga hanyar Sa, kuma Shi ne ma fi sani ga mãsu shiryuwa.


 KENAN : Yin zagi irin na maguzawa da sunan shiryar da wani ɗan'uwan ka wanda kake yi masa kallon batacce , saba wa irin hanyar da Allah (swt) ya ɗora Ma'aikin sa ce a kai. Kuma zaginka ba zai canja komai ba, na daga fahimtar wanda kake yi masa kallon bataccen .


WALLAHI : ba wai muna kawo  maku irin waɗannan Hadisai ba don Nisahaɗi, ko don nuna ilimi ba, sai don kare kan mu daga masu yaɗa sharri na ƙarya a garemu da kuma naiman ladar Ubangiji wacce Ya ke bai wa wanda ya fahimtar da bawan Sa wani abu daga addini.


 


YAU ZA MU KAWO WANI HADISI, WANDA A FAHIMTAR MU, MUMMUNA NE, KUMA HADISIN ƘARYA NE AKA ƘIRƘIRA SHI GA ANNABI (SAW), AMMA KAI MUKE SO KA FASSARA MANA DA KANKA !


Saboda idan muka fassara maka ne kake cewa , mun yi fassar ƙarya da kuma son rai, don cimma wata manufa ta mu, ko ka ce , mu jahilai ne ba mu fahimci fiƙihun Hadisin ba. To a yau kai zaka fassara da kan ka, kuma ka fito mana da irin fiƙihun da ke cikin hadisin. mu kam cin mutuncin Annabi (saw) kawai muke kallo a ciki.


MU TAFI CIKIN ( MU'JAMULKABEER ) NA ƊABARÃNI HADISI NA (( 2658 )).


المعجم الكبير للطبراني - 3178/26615


2658 - حَدَّثَنَا الْحَسَنُ بْنُ عَلِيٍّ الْفَسَوِيُّ، ثنا خَالِدُ بْنُ يَزِيدَ الْعُرَنِيُّ، ثنا جَرِيرٌ، عَنْ قَابُوسَ بْنِ أَبِي ظَبْيَانَ، عَنْ أَبِيهِ، عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا قَالَ: «رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَرَّجَ مَا بَيْنَ فَخِذَيِ الْحُسَيْنِ وَقَبَّلَ زَبِيبَتَهُ»


WALLAHI ! DÃ ZAN CIRE SUNAN ANNABI (SAW) IN SAKA SUNAN BABANKA ACIKIN WANNAN HADISIN DA SUNAN SHI NE KE AIKATA WAI IRIN ABIN DA ANNABI (SAW)  AKA CE YANA AIKATAWA, IDAN DA WANI MAKA MI A HANNUN KA, BABU ABIN DA ZAI HANA KA ,SANYA MANI SHI, SABODA CIN MUTUNCI NE NA ƘARSHE , A NAMU TUNANI. 


'YAN AS'HABULKAHFI : Ku yi mentioning na sunan dik wanda kuka san yana zagin ku ,tare da cewa ba ku iya fassarar Hadisi ba, cewa ya zo ya fassara mana wannan Hadisin kuma ya faɗa mana darasin da Hadisin yake koyarwa , idan yã isa 


AS'HABULKAHFI JIBIA SOCIAL MEDIA TEAM, 06/09/2021,

Comments