KUN SAKI ZIKIRAN MANZON ALLAH SAW.KUNKAMA NA SHEHUNNAI.INJI YAN IZALA!


KUN SAKI ZIKIRAN MANZON ALLAH ,KUN KAMA NA SHEHUNANKU. IN JI (IZALA)


ME YA SA KU KA BAR ZIKIRAN ANNABI (SAW) WANDA YA KOYAR ,KUMA YA RAYU YANA YI SHI DA SAHABBANSA , KUMA YA FAƊI FALALARSU A ƘUR'ANI DA HADISAI INGANTATTU, KUKA KAMA NA SHEHUNANKU ?? IN JI 'YAN UWA ('YAN IZALA)


Alhamdulillah !!!


JIN HAKA KE DA WUYA , SAI AMEERIL WA'IZINA SHEIKH ABDULJABBAR KABARA (H) YA CE,


WANNAN  GASKIYA NE , ZIKIRAN DA ANNABI (SAW) YA KOYAR SUN FI KOWANE ZIKIRI , KUMA BABU ZIKIRIN DA YA KAI SU.


DAGA YAU ZAN ZA'BO ZIKIRAI DAGA ƘUR'ANI DA HADISAI WANDA MANZON ALLAH (SAW) YA RAYU YANA YI ,KUMA YA KOYAR , A MATSAYIN LAMBA (1) TARE DA BIYANTAWA DA ZIKIRAN SHEHUNAN MU ,A MATSAYIN LAMBA TA (2) .DUK DA WAƊANDA, SU KA YI MANA WANNAN TAHADDI ,SU BA SA YIN ZIKIRIN SAM, SAI ƊAN KAƊAN !!!

A KAN HAKA  NE, YA SA WASU 'YAN ƊARIƘAR KE ZAGINSA, TARE DA ƘYAMATAR ZIKIRAN DA ANNABI (SAW) YA KOYAR ƊIN, KAWAI SABODA MALAMIN YA YI RIƘO DA SU TAMKAR NASA MADALLAH DA WANNAN ZAGI DA AKE WA MALAM.


WASU 'YAN ƊARIƘAR KUMA, NA ZAGINSA NE SABO YA CE ((ZIKIRAN ADDININ MUSLINCI DUKA ƊAYA NE)), BATUN CEWA ,BA A HAƊA ZIKIRAN WATA ƊARIƘAR DA NA WATA , ƘARYA NE !!! 


قال النووي في "الاذكار" :- "فصل" كما يستحب الجلوس للذكر ،يستحب الجلوس في حلق أهله..... ويكفي في ذالك حديث ابن عمر (رضي) قال : 

قال رسول الله (ص) :- إذا مررتم براض الجنة فارتعوا ، قالوا 

(وما رياض الجنة ؟ قال :- حلق الذكر ".


 Daga Ibn Umar (R)  ya ce Annabi (saw) ya ce , "  IDAN ZA KU WUCE A DAUSAYIN ALJANNAH , TO KU TSAYA KU YI KIWO, SAHABBAI SUKA CE , MINENE DAUSAYIN ALJANNAH ? MANZON ALLAH YA CE ," HALAƘA TA ZIKIRI".


SABO DA HAKA, DUK WANDA YA CE BA A HAƊA ZIKIRAI TARE , TO SAI DAI IN NASA ,BA NA ALLAH ,DA MANZON ALLAH BA NE, DAGA WANNAN LOKACIN WASU, KE TA ZAGIN SA HAR ZUWA YAU  MADALLAH DA WANNAN


ALLAH YA SAKA WA (IZALA) DA ALKHAIRI BISA WANNAN FAƊAKARWA DA SUKA YI MANA ,KUMA MUN KARBI GYARA ,IN JI MALAMIN, DOMIN SHAIƊAN MA ANA KARBAR GASKIYA DAGA GUN SHI, BARE ƊAN UWANKA MUSULMI. Akan haka ne ya yi littafi

 

((رياض الجنة من أدعية وأذكار الكتاب والسنة ))


wannan (1) ne daga dalilan da ya sa na ke son malamin ,domin kuwa samin irinsa a jagororin addini akwai wahala a yau !!!


©Fatimiyya Alawuyya TV 

Comments