MACIJI ZAI FITO YA SARE KA, IDAN HAR KA SAKE KA ƘARYATA HADISIN SAHABI ABUHURAIRA (RTA)
Saifullahi Murtala Jibia
Masu ƙaryata Hadisin Anas suna cin bulus to , idan kuka sake kuka ƙaryata Hadisin Abuhurairai, akwai bi-baya, saboda haka, a yi hattara !!!
Kamar yadda ya zo a ( سير أعلام النبلاء )
Na Al-Hãfizuzzahabi (R) yã tabbatar cewa, wata macijiya mai girma ta biyo wani saurayi, akan yã ƙaryata hadisin sayyidna Abuhuraira. To yãya aka ƙarke ??
قال الحافظ أبو سعد السمعاني : سمعت أباالمعمر المبارك بن أحمد.سمعت أبا القاسم يوسف بن علي الزنجاني الفقيه سمعت
الفقيه أبا إسحاق الفيروزابادي ، سمعت القاضي أباالطيب يقول : كنا في مجلس النظر بجامع المنصور ، فجاء شاب خراساني ، فسأل عن مسألة المنصورة، فطال بالدليل، حتي استدل بحديث أبي هريرة الوارد فيها ،
Na ji Al-Ƙãdy, Abaɗɗayyibi, yana cewa : Mun kasance a majlisi na munãzarã tsakanin malamai, A Jãmi'ul Mansúr. Sai wani matãshī mutumin Irãn yã zo,. Sai ya yi tambaya a kan Aimamma (dabbar da aka ba wa wani nau'i na abinci ,don tabayyanar da ƙibar da ba ta al'ada ba ).Aka ce masa , ai idan mutum ya sayi dabba aimamma ,yana da ikon ya je ya tayar da cinakin to mene ne hujja ? Sai aka kafa masa hujja da Hadisin Abīhuraira.
فقال- وكان حنفيا : (( أبوهريرة غير مقبول الحديث )). فمااستتم الكلامه حتي سقط عليه حية عظيمة من سقف الجامع. فوثب الناس من أجلها،
Saurayin ya kasance Bahanafe ne, sai ya ce : (( Ai bã á kar6ar Hadisin Abuhuraira )) bai rufe bakinsa ba , sai ga wata shirgegiyar macijiya,tã fãɗó daga kan rufin Masallãci, sai mutane suka watse (ridididididi ) !!
وهرب الشاب منها وهي تتبعه، فقيل له : تب تب. فقال : تبت، فغابت الحية ، فلم يرلها أثر. إسنادها أئمة.
Shi ma saurayi, sai ya girka dagudu. Ai kuwa sai macijiyar ta biyo shi. Ana cikin haka, sai Jama'a suka ce wa saurayin : KA CE MATA , KÃ TŪBA , KÃ TŪBA. SAI YA CE (( NÃ TÚBA )). Sai macijiyar ta bace. Ba a kuma ganinta ba daga wannan ranar !!!!
Isnãdin wannan magana duka A'IMMATU ne suka ruwaito.IN JI ALHÃFIZ (R) (( 2/618-619 )).
Anan ne Dr.Abduljabbar (H) ya ce : Bai dãce ba, mu mayar da Addinin mu ire-iren waɗannan tatsunniyoyi ba,To idanmacijiya zata bayyana har da biyo wani saurayi, saboda kawai ya ce, ba a karbar Hadisan Abuhuraira,TO SAYYID NA UMAR FA, DA YA CE ZAI ROTSA KAN ABUHURAIRA, IDAN YA KUMA ZANTAR DA HADISAN ANNABI (SAW)
A wannan littafin dai (Siyaru A'lãmun Nubala) na Zahabin (( 2/600-601 )) ?????
سعيد بن عبد العزيز : عن إسماعيل بن عبيد الله عن السائب بن يزيد ، سمع عمر يقول لأبي هريرة :لتتركن الحديث عن رسول الله (ص) أو لألحقنك بأرض دوس.
Daga Sa'ibu Bn Yazid,Ya ce, ya ji sayyid na Umar Yana ce wa Abuhuraira :" KO DAI KA DAINA ZANTAR DA HADISAN NAN DA KAKE CEWA DAGA ANNABI (SWA), KO IN MAIDA KA GARINKU " !!
يحيي بن أيوب : عن ابن عجلان : أن أبا هريرة كان يقول : إني لأحدث أحاديث، لو كلمت بها في زمن عمر ،لشج رأسي.
Yahya Ibn Ayyub, daga Ɗan Ijlãn ya ce : Lallai Abuhuraira ya kasance yana cewa, NI BÃ NA ZANTAR DA HADISAI, DÃ NÃ SAKI NÃ ZANTAR ZÃMANIN UMAR , DA YA ROTSA MANI KAI NA". (( 2/601 )).
TO IDAN DAI WANCAN MACIJIN NA GASKIYA NE , ME YA SA BAI FITO BA, YA BIYO UMAR (RTA) WAN DA SHI BAYAN RASHIN YARDA DA HADISAN MA, HAR DA SHARADIN DUKA ????
Yau , ko dã babu Kafurai mã su ƙoƙarin rosa mana Addini, to ya dãce mu cire irin waɗannan ƙarairayi daga litattafan mu na addini.
AS'HABULKAHFI JIBIA SOCIAL MEDIA TEAM JIBIA , 07/09/2021, .
Fatimiyya Alawuyya TV
Comments
Post a Comment