SHIN DAGSKENE NANA FADIMA TANA HAILA KO BATAYI ?
Daga Sayyid Faisal Amin Rijiyar Lemo
Nasiha ga Malam Ibrahim Khalil (mai Iƙirarin zama Shugaban Majalisar malamai ɓangaren Jemagu na ƙasa)
AN GABATAR DA LACCA DOMIN MAI DA MARTANI DA BAYAR DA AMSA GA IBRAHIM KHALIL (Wanda take Iƙirarin zama Shugaban Majalisar Malamai ɓangaren Jemagu) A KAN BATU DA YA YI A KAN HAILAR NANA FAƊIMA A'S DA KUMA TAMBAYA DA YAYI SHIN TA FI MAHAIFIYARTA? SHIN TAFI NANA MARYAM?
GA MAHIMMAN ABUN DA MUKA TAUNA
Da farko an yi bayani kan ma,anar jjnin haila, a lugga da kuma wajan Malaman mazahabobi guda Huɗu da mike da su.
Sannan aka yi bayani kan tabbatar da cewa tabbas akwai matan da ba su yin haila kuma suna haihuwa Wanda waki'i ya tabbatar da haka kuma wasu daga mata sun tabbatar da cewa akwai wadanda ba su yi haila a cikinsu.
Sannan muka kara da ayar da take daukar ma'anar haka shi ne fadin allah aya ta hudu Cikin Suratu Ɗalaƙi
( والائي يئسن من المحيض من نسائكم إن ارتبتم فعدتهن ثلاثة أشهر والائي لم يحضن)
• Daga fassarar da wasu suka yi wa faɗinsa Allah SWT
والائي لم يحضن
shine cewa ana nufin wadanda ba su yin haila yazo Cikin Littafin ma'anil qur,ani na Mallam Zujaji inda yake cewa:
فقياس اللائي لم يحضن قياس اللائي لا يحضن
Ma'ana:
Ƙiyasin wadanda ba su fara haila ba shi ne ƙiyasin wadanda ba su yin haila.
Kaga Ashe akwai wadanda ba su yin haila a cikin mata.
- sannan aka faɗi dalilan da suka tabbatar da cewa Nana FAƊIMA A'S ba ta yin haila dafarko mun ambaci fadin Allah SWT
إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا
Wannan aya ta tabbata cewa ta sauka ne akan mutum hudu ne, Wanda fadima tana ciki babu ko shakka.
To tunda Allah SWT ya ce ya tafiyar da الرجس
Daga wadannan mutum Hudu to hakan ta sa mun tuntubi malaman luga kan ma'anar Kalmar mun duba littafai kamar haka:
: تهذيب اللغة 10 /306
الصحاح للجوهري 3/933
مختار الصحاح للرازي 1/118
لسان العرب لابنمنظور 5/352
المصباح المنير للفيومي 1/219
Inda suka tabbatar da cewa daga ma'anonin Kalmar akwai kazanta datti najasa.
Daganan sai muka tambayi hadisai shin jinin haila najasa ne ko Ba najasa ne ba, inda suka tabbatar mana cewa jinin haila najasa ne, kamar fadin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam ga wata mace game da jinin haila.
فاغسلي عنك الدم وصلي
تحته ثم تقرصه بالماء ثم تنضحه
Ka ga Ashe najasa ne, ita kuma Faɗima A'S an tafiyar mata da haka.
Hadisi na nan zuwa, kan cewa ba ta haila a gaba kaɗan.
A INA AKA CE FAƊIMA A'S BA TA HAILA?
BAYAN MUN KAWO AYAR DA TAKE NUNA CEWA FAƊIMA A'S BA TA HAILA TO A YAU ZA MU KAWO HADISIN DA KE KARA TABBATA HAKA:
Yazo acikin littafin mlMuhibbuddini al-Ɗabary mai suna zaka'irul uƙuba fi manaƙibi zawil qurba 1/44
ذخائر العقبى في مناقب ذوي القربى
Ga abun da yake cewa:
ذكر طهارتها من حيض الآدميات
وعن أسماء قالت قبلت أي ولدت فاطمة بالحسن فلم أر لها دما فقلت يارسول الله إني لم أر لها لها دما عن حيض ولا في نفاس فقال ص أما علمت أن ابنتي طاهرة
مطهرة لا يرى لها دم في طمث ولا ولادة .
Ma'ana:
inji Asma'u Yar Umaisu ta ce Faɗima A'S, ta haifi hassan amma banga jini a gare ta ba, sai na ce ya Manzon Allah ni fa ba taɓa ganin jini a gare ta ba na haila, ko na biƙi sai Annabi Muhammad SAW ya ce, shin baki sani ba cewa 'ya ta mai tsarki ce, a bar tsarkakewa ba. Ba a ganin jini a gare ta na haila ko na biƙi.
Khatamatul Huffaz Allamah Imamus Suyudy ya ambaci wannan magana a cikin littafinsa mai suna:
أنموذج اللبيب في خصائص الحبيب
Juz,I na 1/240 ga abun da ya ce:
وذكر صاحب الفتاوى الظهيرية من الحنفية أن من خصائصه ص أن ابنته فاطمة رض لم تحض ولما ولدت طهرت من نفاسها بعد ساعة حتى لا تفوتها صلاة قال ولذلك سميت الزهراء.
Ma'ana:
Mai Littafin fatawaz zuhairiyya ya ambaci cewa yana daga kususiyar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam cewa 'yar sa Faɗima A'S ba ta haila, kuma yayin da ta haihu ta tsarkaka daga biƙinta bayan awa ɗaya, don kada sallah ta tseremata. Saboda haka aka ambaceta da sunan Zahra'.
Sannan Muhammadu bin Yusuf Assalihi Ashshamiy ya ambaci haka shi ma cikin littafinsa mai suna:
سبل الهدى والرشاد في سيرة خير العباد
Juz,I na 10/486
Haka nan Sheikh Yusuf Al-Nabhany ya ambaci haka shi ma cikin littafinsa
الشرف المؤبد لآل محمد ص 60
Ya ce: NASA,I ya rawaito amma na buncika Nasa'in ban gane shi ba, to amma tunda mun tabbatar da hakan a wasu littafan to Ba matsala.
Wannan shi ne bayani a kan amsa tambayar wannan mutumin (Ibrahim Khalil) da ya ce yayin da aka tambayeshi shin da gaske ne Nana Faɗima A'S ba ta haila, sai yace
INJI UBAN WA? TO GASHI MUN FAƊA MASA WANDA YA FAƊI.
Sannna bayan nan mun amsa wata TAMBAYA wadda za a iyayi shi ne
YAYA FAƊIMA A'S TAKE HAIHUWA BAYAN KUMA BA TA HAILA?
To abun da zai zama amsa anan shine Haƙiƙa kamar yadda muka tuntuɓi wannan masana ilimin Obstetrics and Gynaecology sun ce, asalin haila shi ne, akwai kwayoyin halitta da Allah yake halitta a jikin mace to suna sakkowa zuwa mahaifarta duk wata idan suka sauko ba su hadu da kwayoyin namiji ba, to sai su rube su zama jinin haila, to kaga Ashe duk wacce ba ta haila kenan zai zama ba ta da kwayoyin halitta ba za ta haihu ba!
To a nan abun da muke cewa shi ne waki'i ya tabbatar da cewa, akwai matan da ba sa haila kuma suna haihuwa to ka ga Ashe akwai abun dubawa cikin wannan bincike na malaman Obstetrics and Gynaecology.
Don haka abun da zai iya zama mafuta shi ne, ya zama irin wadannan matan da ba sa haila kuma suke haihuwa kamar Nana Faɗima A'S to zai zama suna haihuwa ta hanyar ya zama Ba a halittar musu wannan kwayoyin na haihuwa har sai lokacin da ake saduwa. da su sai ya zama suna saukowa mahaifa, sai su hadu da kwayoyin namiji sai a samu Rabo
Wannan shi ne abun da zai iya zama mafuta in ko ba haka ba, to ya za mu yi da waki'i da ya tabbatar da cewa akwai masu haihuwa kuma ba su yin haila.?
Ko kuma ya zama ko da hakan ya tabbata to ita Nana Faɗima A'S ta samu hakane ta hanyar karama tun da dama ita karama wata aba ce da ta saɓa da al'ada da Allah yake bayyanata a hannun wani waliyyi salihin bawa.
- sannan mun bawa wannan mutum (Ibrahim Khalil) amsa a kan tambayar da yayi yace shin fadiima tafi mahaifiyarta ne? ko kuma tafi Maryamne ? Inda muka bashi amsa muka tabbatar masa duk tafisu da dogara bisa hadisai tare da kawo malaman da suka fadi haka.
NANA FADIMA TAFI DUKKAN MATA CIKI HARDA MAHAIFIYARTA DA KUMA NANA MARYAM ?
Hakika acikin wannan zama da akayi ranar alhamis
Hakika mun tabbatar da cewa Nana Faɗima A'S ta fi duk matan duniya ciki harda Nana Khadijah mahaifiyarta da kuma Nana Maryam, bisa dogaro da wasu hadisai kamar haka:
1-Hadisin Bukari 3714 da wasunsa da muka ambata inda shugaba ya fada:
فاطمة بضعة مني فمن أغضبها أغضبني
Ma,ana Faɗima A'S tsoka ce Daga gare Ni, Wanda ya fusata ta, to ya fusata Ni.
To ka ga Ashe hukuncinta daya da shugaba saboda Ka,idar usulu
للجزء حكم الكل
Shi ya sa Imamu Malik RTA yake cewa kamar yadda Shehu tijjani ya fada a cikin Irshadatur Rabbaniyah shafi na 121
أما أنا فلا أفضل أحدا على بضعته ص
Ma'ana:
Amma Ni (INJI Imam Malik) ba zan fifita wani ba a kan tsokar jikin Annabi SAW.
Sai Shehu Tijjaniy RTA yace:
يشير إلى ما جتمعت عليه الأمة من تفضيل أبي بكر على فاطمة رض أخبر عن نفسه أنه لا يقول ذلك وسكت......
Ma'ana
Yyana nuni zuwa ga abun da al'umma suka hadu a kai na fifita Abubakar a kan Faɗima A'S cewa shi ba zai faɗi haka ba sannan ya shiru.....
2- Hadisin Imam Al-hakimu 4730 da waninsa cewa shugaba ya ce: a haƙƙin Nana Faɗima
إن الله يغضب لغضبك ويرضى لرضاك
Wannan hadisin ya nuna cewa tana da matsayi babba na yin fushin Allah saboda fushinta haka yadda ka ga duk mata Ba wacce ta samu haka.
3- Hadisin Bukari 3624 da wasunsa cewa annabi saw ya fada a hakkinta
أما ترضين أن تكوني سيدة نساء أهل الجنة أو نساء المؤمنين
A wani lafazi
سيدة نساء العالمين
Kaga ya tabbata ita ce shugaba matan aljannah kuma shugabar matan aljannah.
Kuma Nana Khadijah da Nana Maryam, suna cikin matan aljannah ko matan talikai.
Kuma duk da wasu hadisan sun nuna Maryam ita ce shugabar matan zamaninta to Nana Faɗima tana gaba da ita saboda aalam ɗin Nana Faɗima A'S yana gaba da aalam din Nana Maryam
كنتم خير أمة أخرجت للناس..........
4- Hadisin da Abul Abbas Shehu Ahmad Tijjaniy RTA ya kawo a irshadatu shafina 121 cewa Annabi Muhammad SAW ya ce: ita da ƴaƴanta da mijinta suna tare da shi a matsayinsa a cikin aljannah.
أنك وهذين وذلك النائم معي في درجة واحدة في الجنة
Wannan matsayi kamar yadda Shehu Abul Abbas Ahmad Tijjaniy RTA ya fada: ko Annabawa da Manzanni ba su same shi ba.
5- Hadisin Ɗabrany daga Nana A'ishah ta ce ba ta taɓa ganin Wanda ya fi Faɗima darajaba in ban da mahaifinta.
ما رأيت أحدا أفضل من فاطمة غير أبيها
A wajan Imam Hakim 4756 take cewa, ba ta taɓa ganin mai gaskiyar zanceba kamar Faɗima A'S ba, sai dai Mahaifinta.
ما رأيت أحدا أصدق لهجة منها إلا أن يكون الذي ولدها.
قال الحاكم صحيح على شرط مسلم ووافقه الذهبي
Dama mukamin Siddiƙanci shi ne ke bin mukamin Annabta.
مع الذين أنعم الله عليهم من النبيين والصدقين....
To ka ga wacce take a wannan matsayi ta yaya wata za ta fi ta?
Wannan kadan ne daga hujjojinmu a kan cewa Nana Faɗima A'S ta fi kowace mace.
A gaba za mu kawo malamai magabata da suka tafi a kan cewa Nana Faɗima A'S, ta fi mahaifiyarta'
Sannan mu ƙara kawo wasu magabatan da suka faɗi cewa ta fi Nana Maryam A'S.
MAGABATAN DA SUKA FADI CEWA NANA FADIMA TA FI MAHAIFIYARTA DARAJA
Kafin mu fara ambatonsu za mu kawo wani hadisi, Wanda muka ambato a cikin wannan za ma Wanda hadisi shi kaɗai ya isa ya zama hujja kan cewa nana FAƊIMA ta fi mahaifiyarta shi ne hadisin da Abu Ya'ala ya rawaito 1/18 lamba ta 6 acikin hadisi Mai tsawo na Sayyidi Umar da yake ba da labarin ya nemi Abubakar ya auri Hafsah sai ya yi shiru, sai ya yi wa Usmanu magana sai ya ce ba shi da ra'ayin aure yanzu .......Wanda a karshe Umar ya kai karar Usmanu wajan Shugaba SAW, saboda ya fi bashi haushi fiye da Abubakar da yayi shiru sai Annabi SAW ya ce:
تزوج حفصة خير من عثمان وتزوج عثمان خيرا من حفصة فزوجه النبي ص بنيته
Ma'ana:
sai ya ce hakika Wanda ya fi Usman ya auri Hafsah wato shi Shugaba SAW kenan, shi kuma Usmanu ya auri wadda ta fi Hafsah wato yayan Annabi SAW daya aura mata guda biyu Ruqayyah da Ummu Kulsum.....
To kenan iya wannan ya nuna mana cewa duk 'ya'yan Annabi SAW Ba ma Faɗima A'S ba sun fi matansa dataja to ka ga ashe Faɗima A'S ta fi mahaifiyarta.
Don kada ace magabata Mai suka ce, to ga maganar Ibnu Hajar kamar yadda Manawiy ya kawo a cikin littafin Faidul Qadeer 2/462
يدل لتفضيل بناته على زوجاته خبر أبي يعلى عن عمر مرفوعا تزوج حفصة خير من عثمان وتزوج عثمان خيرا من حفصة.
Sannan ga wasu daga Magabata, da suka tafi akan wannan magana:
1-يقول القسطلاني في إرشاد الساري 6/68 أما) بتخفيف الميم( ترضين أن تكوني سيدة نساء أهل الجنة) دخل فيه أخواتها وأمها وعائشة إلى قوله وقد سئل أبوبكر بت داود من أفضل خديجة أن فاطمة؟ فقال إن رسول الله ص قال إن فاطمة بضعة مني فلا أعدل ببضعة من رسول الله ص أحدا.
Kaga anan Qasdalaniy yana fadar cewa shugabancin nana FAƊIMA A'S ya game yan uwanta da mahaifiyarta sannan ya kawo maganar Ibnu Abi Daud da aka tambaye shi, kan wa tafi tsakanin Faɗima da nana Khadijah.
Ya Kara fada shi kasdalaniy 6/146 bayan ya ambaci hadisin shugabannin matan aljannah
فالحديث صحيح وهو صريح في أن فاطمة وأمها أفضل نساء أهل الجنة والحديث الأول المعلق يدل لتفضيلها على أمها.
Ma,ana hadisin yana nuna fifikon Faɗima da mahaifiyarta a kan sauran matan shuwagabannin aljannah hadisin farko kuma mu'allakiy yana nuna fifita Faɗima kan mahaifiyarta. Sannan ya kawo zancen Subukiy da yake cewa abun da suke Kai shi ne Faɗima ta fi sannan Khadijah sannan aysha........
2- Mai littafin Mirkatul mafatihi 9/3964 yana cewa, bayan ya kawo hadisin أما ترضين ..........
والحديث بظاهره يدل على أنها أفضل النساء مطلقا حتى من خديجة وعائشة ومريم وآسية وقد تقدم الخلاف
Ma,ana hadisin da zahirinsa yana nuna cewa fadima tafi duka mata ba togaciya har khadija da aysha da maryam da asiya amma sabani akan haka ya gabata.
3- يقول المناوي 4/421 في فيض القدير شرح الجامع الصغير قال الشيخ شهاب الدين ولوضوح ما قاله السبكي تبعه عليه المحققون قال فأفضلهن فاطمة فخديجة فعائشة إلى قوله وعبارة السهيلي في روضه عند كلامه على خبر إنها سيدة نساء أهل الجنة ما نصه: قد دخل في هذا الحديث أمها وأخواتها وقد تكلم الناس في المعنى ....
Ma'ana
Da yawa daga muhakkikai sun bi, Allamah Subukiy a kan maganarsa ta fifita Faɗima A'S a kan kowa saboda bayyanar maganartasa. Sannan Allamah Suhailiy ya faɗa a cikin Arraudu s
Yayin da yake magana a kan hadisin cewa ita ce shugabar matan aljannah ya ce: mahaifiyarta ta shiga ciki da yan uwanta, malamai sun yi bayani a kan wannan ma,ana....
Shi ya sa Maulanmu Sheikh Abduljabbar Kabara (H) Amirul wa'izeena ya ke fada cikin wasu baitukansa ababil 1/301
أنت في صف أربع كملت بين
نساء الدنيا لما تم فيك
أنت قدام الصف بل أنت فحوى
ولبان الصف اللواتي يليك أنت بل أنت من سواك إذا ما
قيس ما فيك بالذي حزن منك فعليك الصلاة يا بنت بل يا
يا ويا يا ويا كما صح فيك
MAGABATAN DA SUKA FADI CEWA NANA FADIMA TAFI NANA MARYAM DARAJA
Acikin wannan majalisi da mukayi domin maida martani ga Ibrahim Khalil mun ambaci wasu daga malamai da suka fadi cewa nana fadima tafi nana maryam kamar:
1- Zainuddin Al-Manawiy a cikin littafinsa التيسير بشرح الجامع الصغير 1/22
Bayan ya ambaci hadisin zuwan mala'ikan da yayi bushara ga Shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam, cewa Assayidah Faɗima A'S ita ce shugabar matan aljannah, sai ya ce:
هذا يدل على فضلها على مريم سيما إن قلنا بالأصح أنها غير نبية
Ma'ana wannan ya nuna tafi Nana Maryam musamman idan muka tafi a kan abun da ya fi inganci cewa Nana Maryam ba annabiya ce ba.
2- Khatamatul Huffaz Allama Jamaluddin Abdulrahman Suyudy kamar yadda yazo cikin littafin شرح البخاري للسفيري شمس الدين محمد بن عمر الشافعي 1/163
ya ce shin Nana Maryam ce ta fi falala ko kuma Assayidah Faɗima A'S?
قال شيخنا العلامة جلال الدين السيوطي: لم يتعرض أحد للتفضيل بين مريم وفاطمة والذي نختاره بمقتضى الأدلة تفضيل فاطمة عليها.
Ma'ana shehunmu Khatamatul Huffaz Allama Jamaluddin Abdulrahman Suyudy ya ce: wani daya Bai bujuraba wajan fifita tsakanin maryam da fadimaba sai mu abunda muka zaba bisa abunda dalilai suka hukunta shine cewa fadima tafi maryam.
3- Sheikh Yusuf Al-Nabhany acikin littafinsa
الشرف المؤبد لآل محمد ص 59
Ya ambaci cewa da yawa daga malamai tabbatattu a cikin ilimi wadanda suka tafi a kan cewa Sayyidah Faɗima A'S ta fi dukka mutane ciki har Nana Maryam daga cikinsu akwai
-takiyyuddinis subkiy
-suyudiy
- badaruz zarkashiy
- takiyyul maqareeziy
ga abun da yake cewa:
وصرح بأفضليتها على سائر الناس حتى السيدة مريم كثير من العلماء المحققين منهم التقي السبكي والجلال السيوطي والبدر الزركشي والتقي المقريزي.
Sannan ya ambaci maganar wasu a cikinsu kamar yadda mun ambaci hakan a cikin majalisin.
4- Shehu Ahmad Abul Abbas Tijjaniy RTA, kamar yadda yazo cikin jawahirul ma'aniy shafi Na 121 yake cewa:
ولا مطمع للنساء في استمداد تلك الكمالات منه صلى الله عليه وسلم إلا فاطمة رض فقط فبذلك كانت أفضل النساء على الإطلاق.
Ma'ana Babu tsammani ga mata cikin samun madadin wannan cika daga gare shi SAW, sai dai ga Sayyidah Faɗima A'S kawai, Allah ya Ƙara mata yarda, saboda haka ne ta zama mafi daukakar mata Saki babu ƙaidi, ma'ana ba a cire kowa ba.
5- A karshe za mu cike da mujaddidin wannan karniy Maulana Sheikh Abduljabbar Kabara (H) ameerul wa'izeena shi ma akan haka yake, kamar yadda yake fada a cikin wasu baitukansa da yayi ga Nana Faɗima A'S, duba ababil Na daya shafi Na 301
أنت في صف أربع كملت بين
نساء الدنيا لما تم فيك
أنت قدام الصف بل أنت فحوى
ولبان الصف اللواتي يليك
أنت بل أنت من سواك إذا ما قيس ما فيك بالذي حزن منك
فعليك الصلاة يا بنت بل يا
يا ويا يا ويا كما صح فيك
Edited and compiled by
Fatimiyya Alawuyya TV
Comments
Post a Comment