SIFFOFI DA KAMALA NA MANZON ALLAH (SAW)
Bismillahi rahamani rahim dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ma daukakin sarki salati da taslimi ga shugabamu Annabi muhammadu s a w da Alayan gidan sa da sahaban sa tsarkaka da sahabban sa baki daya
Insha Allah yauma cikin amincewa da lamunce wa a cikin girma da matsayi na annabinmu Annabi muhammad s a w zamu cigaba da wannan rubutu mai taken SIFFOFIN DA KAMALA NA MANZON ALLAH (SAW)
Babu shakka manzon Allah saw yakasance yanada jazibiyya minene ma anar jazibiyya ma anar jazibiyya shine yayin da ka kalli manzon Allah saw zakaji zuciyarka tayi tsun tsu ta tashi ta tafi izuwa gareshe sallallahu ailaihi wasallam.
A dai dai wannan lokacin zakaji babu wanda kakeso ka kallah in bashiba saw ayayin da kacigaba da kallonsa saikaji tsoro yakamaka saboda kwarjini na manzon Allah s a w
Kuma zaka iya binsa misali kamar yadda mukaga zulaika tabi annabi yusuf alaihisalam ayayin da so ya cika zuciyanata kamar yadda yazo a kur ani
Amma manzon Allah s a w in ka ganshi in ka tun kareshi sai kaji kwarjinsa ya kamaka kuma tsoro ya kamaka kamar yadda imamu busiri yacewa idan kaga annabi saw kai zakaci rundunane sukazo saw idan yazo zakazaci yana tafiya da rundunane amma kuma shidaya ne s a w to babu shakka sifofi na manzon Allah s a w riwaya ta ibni abi halata shi ya karbane daga al imamu hussain wanda babu shakka al imamu husain ya dade bai fadaba saboda tsadar maganar dakuma kyanta saw
Al fazazi yana cewa annabinmu mai kwarjini ne. Annabi mai hai bane bawani idon da zaiyi arba da banzon Alla s a w sai tsoro da kuma soyya ya chudanya da wannan zuciyar saw
Abinda yasa akace kyau na manzon Allah saw yana da jazibiyya kuma yanada dafi iyya sabanin kyau na sauran annabawan da suka gaba misali mu dauki kyau na annabi yusuf da akace kyakkyawane kwarai babu wani wanda ya kaishi saboda yana kama da sayyida tuna sara ita sayyida tuna sara itace kakan annabi yusuf matar annabi ibrahim ma haifiyar annabi isma il alaihi salam
Ance kamaninta irin na hurri inune sai akace annabi yusuf yana kama da ita kwarai ya dakko kyanta da kuma kwarjininta to anan sai akace kyau na annabi yusuf yana da jazibiyya in ka ganshi zakaji soyayyarsa ta kamaka
Insha Allah zan dakata anan sai mun hadu a rubutu nagaba domin cigaba da bayani akan siffofi da kamala na manzon Allah s a w
Allah muna rokonka kasa dan Allah muke ka haskaka lamarinmu ka dafamana kabamu ilimi mai albarka ka tai makemu da taimakonka dan isar sayyidina rasulullahi s a w
Rubutawa
Mai nana fadima
Comments
Post a Comment