ANYI SHARHI AKAN MAGANAR BARR HASHIM HUSAINI FAGGE


 POST:NO:1213


GAJERAN SHARHI KAN MAGANAR BARRISTER HASHIM FAGGE 


Barrister Yace "Yanzu Duk Wanda Kaji Yana Cewa Malam Abduljabbar Ya Zagi Annabi S.a.w To Dama Shekara Goma Baya Akan Wannan Yake" 


Tabbas Wannan Magana Ta Barr Hashim Fagge Haka Take, Ko Baka Gaskata Shi A Rubuce Ko A FaÉ—ake Ba, A Zuciyarka Zaka Ce Shugaban ÆŠarikar Baristiya Yayi Gaskiya. Bari Mu Ga Kashe Kashen Masu Wannan Da'awa ( Ta Malam Abduljabbar Ya Zagi Annabi) Wa'iyazubillahi


1- Ƴan Tijjaniya, 

A Yanzu Duka Ƴan Tijjaniya Na Allah Wanda Kishin Annabi S.a.w Ne Yasa Suka Shiga Kifaffu Da Kwando Suke Cewa Malam Abduljabbar Ya Zagi Annabi S.a.w Yanzu Sun Gane Gaskiya, Ya Ku Ƙara Yarda Yanda Kukaga Sun Jaa Bakinsu Sunyi Shiru, Sun Kyale Wanda Dama Can Shekara Goma Suna Kan Wannan Da'awar ( Maganar Barrister) 


2- Ƴan Izala,

 Æ³an Izala Masu Sauran Hankali WaÉ—anda Basu Bada Aron Hankulansu Anai Musu Tunani Ba, Sun Jaa Bakinsu Sunyi Shiru, Sun Bar Arnan Togo, Masu Tsotsan G*nd*n Yara Suna Cigaba Da Kulle Kullen Su Da Sukai Shekara Goma Sunayi.


3- Ƴan Kadiriya

Ƴan Kadiriya Na Sidi Abdulkadir Wanda Suka KwankwaÉ—i "Ya Rasulillahi Kuz Biyadi" Sukai Tatil Da "Anuwaru" Sunja Bakinsu Sunyi Shiru, Sun Kyale Masu Cutar Hassada, Da Ƙaton MaÆ™ogaro, Suna Nuna Hassadarsu Ta Shekaru Fiye Da Goma Baya. 


4- Yan Boko

Ƴan Bokon Da Aka Kifawa Kwando A Ka, Wanda Kishin Annabi S.a.w Ya Kaisu Ga Zagin Malam Abduljabbar Sunyi Bincike Sun Gano Karyar Banza Ce Ace Masoyin Annabi Kamarsa Ya Zage Shi, Sunyi Shiru Sun Kyale, Wanda Dama Can Gadon Ƙiyayyar Malam Abduljabbar Sukai Gurin Iyayen Su. 


5- Ƴan Baruwanmu

Ƴan Ba Ruwanmu Da Aka RuÉ—a Gwala Gwalan Karatuttukan Barrister Hashim Hussein Fagge Ya Tsamo Su Sun Gane Kifa Musu Kwando Akai Da Suna Malam Abduljabbar Ya Zagi Annabi Wa'iyazubillahi Sun Kyale Ya'yan Kishiya Da Tallan Tirmi. 


Waɗannan Sune Waɗanda Suka Yayatawa Duniya Sharri Da Ƙage Da Ƙaharu Da Akaiwa Malam Abduljabbar, Yanzu Duka Sun Fahimci Gaskiya.


©️ Jawad Salisu Umar

Attaqiy Alganawiy

Comments