KOTU TA TASA KEYAN MAKASAN HANIFA GIDAN GYARAN HALI.KURKUKU


 Kotu ta tisa Æ™eyar makasan Hanifah zuwa gidan gyaran hali. 


Aliyu Samba


An gurfanar da Abdulmalik Muhammad Tanko, Hashim Isyaku da Fatima Jibrin Musa a gaban kotun Majistrate dake zaman ta gidan Murtala a jihar Kano. 


An gurfanar da wadanda ake zargin ne da aikata laifukan hada kai don aikata laifi, garkuwa, biye wanda akai garkuwa da shi da laifin kisan kai.


M.A LAWAN Kwamishinan Shari'a na jihar Kano shine ya gabatar da Æ™ara a gaban mai Shari'a Mohammed Jibrin da misalin karfe 2:40 na yamma, inda ya bayyanawa kotu cewa nan da kwana 7 zasu gurfanar da wadanda ake Æ™ara a gaban kotun da take da hurumi da irin laifin su. 



Bayan gabatar da wadanda ake ƙara a gaban kotu, an karanta musu tuhumar da ake yi musu cikin harshen turanci, inda aka fassara cikin harshen Hausa:


'' Ana tuhumar ku da laifin hada kai don aikata laifi, garkuwa, boye wanda akai garkuwa da shi da laifin kisan kai''



''kai Abdulmalik Mohammed Tanko Mai shekaru 34, malamin makaranta mai makarantar Noble kids dake Kwanar dakata a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, ka haÉ—a kai da Hashimu Isyaku mai shekaru 37 da Fatima Jibrin mai shekaru 26 dukkan ku yan unguwar Tudun Murtala dake Kano, kuka aikata laifin garkuwa da Hanifah Abubakar yar shekara 5,

 tare da É“oye ta a inda kuka yi garkuwa da ita, ku ka kuma kashe ta, wacca É—aliba ce a makarantar ka, kuka ci zarafin ta, kuka cutar da ita, kuka boye ta.''


''Sannan kai Abdulmalik ka kashe Hanifa Abubakar da shinkafar bera, ka gutsutsura sassan jikin ta, ka sa a ta buhu.''


''kai kuma Hashimu ka binne ta a wani kabari dan kankani a makaranta Noble Kids, kafin ku karbi ₦100,000 a hannun iyayen ta cikin ₦6,000,000 da kuka ce a baku kuÉ—in fansa'' Inji wani sashe na tuhumar.


Mai gabatar da Æ™arar ya shedawa kotu cewa Ƴan sanda sun kammala bincike, kuma wadanda ake tuhuma sun fahimci tuhumar a ake musu, sakamakon haka, sun rokon kotu data bada umarnin tsare wadanda ake tuhuma su 3 duba da irin girman laifin da ake tuhumar su dashi. 


Sunyi alkawarin zasu gurfanar dasu a gaban kotun da zatayi Shari'ar su cikin kwana 7 kacal.


Mai Shari'a Mohammed Jibrin ya bada umarnin kaishi gidan gyaran hali, ya kuma daga zaman zuwa 2/2/2022 domin a cigaba da sauraron karan




©Fatimiyyaa

Comments