ANYA AKAN ANNABI S.A.W SUKE RIGIMA DA ABDULJABBAR 🤔
Duk ɗan da yace muku Sheikh Abduljabbar ya zagi Annabi S.A.W ku tambayeshi wane Annabin a ciki?
A-namu Annabin da Allah yake bugawa tambarin (وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٍۢ) ya tattare dukkan dabi'un girma ?
B-Ko nasu Annabin da bukhari yake cewa (يَدْخُلُ عَلَى أُمِّ حَرَامٍ بِنْتِ مِلْحَانَ فَتُطْعِمُهُ) yana shiga gidan ummu haram ta ciyar dashi?
Idan sunce namu da Allah ya bugawa wancen tambari ku tambayesu ina wajen yaushe dan duk wanda yasan Sheikh Abduljabbar tsawan sama da shekara 30 bashi da Aiki sai kariya da yabo da kirari da dasa kaunar ma'aikin Allah da girmama duk wani Abu daya rabeshi (S.A.W.W)
Idan sunce nasu wanda bukhari yace yana zuwa gidan matan mutane pls kuce rigimar ba tashi bace daga su bukhari ne in kisa ko zagi ko wani horo suke so suyi to su zasu yiwa bashi ba, matsalarsa dasu bukhari jinginawa namu Annabin haka shine yake fito da bayani na gaskiyar yadda nasa Annabin yake.
Dalilina akan hakan:-
Da bukhari ya rawaici hadisi me lamba 2788 yace:
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّهُ سَمِعَهُ يَقُولُ : كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْخُلُ عَلَى أُمِّ حَرَامٍ بِنْتِ مِلْحَانَ فَتُطْعِمُهُ، وَكَانَتْ أُمُّ حَرَامٍ تَحْتَ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ
Anas dan malik yace: Annabi ya kasance yana shiga gidan Ummu haram matar Ubada dan Samit ta ciyar dashi....
Idan ka duba lamba ta 2800 kuma za kaga yace ita Ummu haram din tace idan haje yana bacci a kusa da ita:-
عَنْ خَالَتِهِ أُمِّ حَرَامٍ بِنْتِ مِلْحَانَ ، قَالَتْ : نَامَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمًا قَرِيبًا مِنِّي..
Idan kuma ka koma kuma waccen lambar ta sama wato 2788 za kaga wai kama kan Nasu Annabin take tana duba kwarkwata shine yayi baccin:
..فَدَخَلَ عَلَيْهَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَأَطْعَمَتْهُ وَجَعَلَتْ تَفْلِي رَأْسَهُ، فَنَامَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ..
Shi kuma Sheikh Abduljabbar sai yace: A'a wlh malam Bukhari karya yake ko ince ya fada ba dai-dai ba (kar ace nima nayiwa Bukhari rashin kunya) sai dai in naka Annabin ne a haka, ni nawa Annabin koma cikin littafin malamin ka Ahamad ɗan hambali hadisi me lamba 2722 ƙanin nawa Annabin Ibn Abbas yace ko kadan Annabi (S.A.W) a dakin ɗaya daga matansa yayi wannan bacci har yayi wannan mafarkin da duk wanda yaje ya duba karashen hadisin xai gani kuma karya kake babu maganar kamawa nawa Annabin kwarkwata dan shi me tsarki ne abun tsarkakewar Ubangiji mu duba mu gani me ahamad yake cewa:
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ ، قَالَ : بَيْنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي بَيْتِ بَعْضِ نِسَائِهِ، إِذْ وَضَعَ رَأْسَهُ فَنَامَ، فَضَحِكَ فِي مَنَامِهِ، فَلَمَّا اسْتَيْقَظَ قَالَتْ لَهُ امْرَأَةٌ مِنْ نِسَائِهِ : لَقَدْ ضَحِكْتَ فِي مَنَامِكَ، فَمَا أَضْحَكَكَ ؟ قَالَ : " أَعْجَبُ مِنْ نَاسٍ مِنْ أُمَّتِي يَرْكَبُونَ هَذَا الْبَحْرَ هَوْلَ الْعَدُوِّ، يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ ". فَذَكَرَ لَهُمْ خَيْرًا كَثِيرًا.
Wannan shine asalin hadisin namu Annabin (S.A.W) saboda gudun tsawaitawa basai na fassara ba.
Idan kuma sun ce Annabin mu daya dasu to kuce musu me yasa da Bukhari yace: yana shiga gidan matan Aure su bashi abinci yaci ya kwanta a kusa dasu su dinga kama masa kwarkwata yayi bacci basu karyata shi amma da Mal Abduljabbar ya karyata shi ya fadi yadda akai ya kawo ruwayar data fi dacewa da girman Manzan Allah kuma bata dauke da wani nau'i na cin mutumcin Annabi S.A.W shi suke zaginsa da tsine masa hasali yau suka hada kai da gwamnatin su aka turashi kurkuku anya Akan Annabi Suke wannan rigimar kuwa kodai akwai wani Abu a kasa?
Idan akan Annabi ne kamata yayi suyi rigima da Bukhari bada Abduljabbar ba👌
©Fatimiyyaa
Comments
Post a Comment