FATAWAR SHEIKH JA'AFAR ADAM (R) DA SHEIKH ABDULJABBAR NASIRU KABARA A KAN HALACCIN YIN TARON (MAULIDI)
FATAWAR SHEIKH JA'AFAR ADAM (R) DA SHEIKH ABDULJABBAR NASIRU KABARA A KAN HALACCIN YIN TARON (MAULIDI)
✍️ Saifullahi Murtala Jibia.
SHEIKH JA'AFAR MAHAMUD ADAM ((R)) CIKIN WANI KARATU NA SA YAKE CEWA
" Shi ya sa lokacin da muke ta musu wato ( jayayya ) da wasu 'yan uwa a kan batun Maulidi, sai muka ce da su ai abu ne mai sauƙi . Gã :
LITTAFIN ( AHALARI ) DA
LITTAFIN ( ISHMÃWĪ ) DA
LITTAFIN ( IZIYYÃ ) DA
LITTAFIN ( RISÃLA ) DA
LITTAFIN ( ASKARĪ ) DA
LITTAFIN ( MUKHTASAR )
Waɗannan 👆 duk litattafai ne na koyon addini, mu ( izala ) da ku ( Ɗariƙa ) mun yi imãni da su, kuma muna koyon addini a cikinsu. Amma duk a cikin su babu wanda ya kawo FASALI KO BÃBI NA ( MAULIDI )
TAMBAYA
👉 To me ya sa ba su kawo ba ne ???
👉 Ko dukkanin su sun yi Mantuwa ne ??
👉 ko dukkanin su sun boye ilimi ne ??
👉 Ko dukkanin su sun jahilta, wato ba su san falalar Maulidin ba ne ??
👉 ko kuma me ? Ko Maulidi ba addini ba ne, don haka ba su kawo shi ba. A cikin waɗannan 👆 dole a yi ɗaya 🙆♂️🙆♂️🙆♂️ !!! "
DR. SHEIKH ABDULJABBAR KABARA (H) CIKIN WANI KARATU NA SA YAKE CEWA
" Ma su cewa sun duba litattafai ba su ga bãbin (Maulidi) ba, ai ba ku dubã gurin da Maulidin yake ba ne.
LITTAFIN ( AHALARI ) DA
LITTAFIN ( ISHMÃWĪ ) DA
LITTAFIN ( IZIYYÃ ) DA
LITTAFIN ( RISÃLÃ ) DA
LITTAFIN ( ASKARĪ ) DA
LITTAFIN (MUKTASAR )
Ai waɗannan 👆 duk litattafan FIƘIHU ne. Ai bã ã sãmin bayanan sīrã wato ( tãrīhi ) cikin litattafan FIƘIHU. Bã maulidi kaɗai zã ka rosa ba, saboda kawai ba ka gan shi ba a cikin su, wato duk ababuwan nan da ake ba mu labari na sīrã wato ( tãrīhī ) , to sū mã sai kã rosa su. MISALI :
YÃƘIN BADAR
YAƘIN UHUDU
YAƘIN KHAIBAR
AUREN NANA KHADIJATU (RTA)
AUREN NANA A'ISHATU (RTA) E.T.C
TAMBAYA
Shin wai, akwai labarin waɗannan 👆 cikin waɗancan litattafai ? Wato :
LITTAFIN ( AHALARI ) KO
LITTAFIN ( ISHMÃWĪ ) KO
LITTAFIN ( IZIYYA ) KO
LITTAFIN ( RISÃLÃ ) KO
LITTAFIN ( ASKARĪ ) KO
LITTAFIN ( MUKTASAR) ????
Tunda babu bayanin yãƙin Uhudu,da Badar da Khaibar da Auren Nana Khadija (rta) da Auren Nana A'isha (rta) a cikin waɗannan littattafai 👆 wato Kenan ƙarya ne sam ba a yi su ba 😀😀😀😀 ????? "
DR.SHEIKH ABDULJABBAR (H) SAI YA CI GABA DA CEWA :
" Ai duk littafin sīrar da ka sani wato tãrīhi indai yã isa a nuna shi da yatsa, to idan ka kawo shi zan nuna maka ( bãbin Maulidi ) a cikin sa !!!
👉 Shamsuddeenizzahabī wato ( almãjirin Ibn Taimiyya ) a cikin littafin sa mai suna : SIYARU A'LÃMUNNUBALÃ , ka duba zã ka ga ( bãbin Maulidi ) !!!
👉 Ka dubi TÃRĪKHUL ISLÃM, Na Zahabin shī mã a cikinsa yã kawo ( bãbin Maulidī )
👉 Ibn Kasir , a cikin littafin sa (ALBIDÃYÃ WANNIHÃYÃ ) Ka duba zã ka ga ya kawo ( bãbin Maulidi ) !!!
👉 Ibnul Īmãd Alhambalī a cikin littafin sa mai suna ( Shazarãtuzzahab ) ka duba ciki za ka ga yã kawo ( bãbin Maulidi ) E.T.C !
ALLAH (SWT) KA JIƘAN SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM, KA GAFARTA MASA, KA YAFE MA SA KUSAKURAN SA 🤲🤲🤲.
Allah (swt) Ka cigaba da tona ma su asiri Malaman da suka ƙulla wa Dr. Abduljabar makirci, saboda hassada, da fifikon falalar Ubangiji a gare shi a kan su 🤲🤲🤲🤲.
Ɗimbin Musulmai, Masoya Manzon Allah (saw) da suka shirya tsaf, don gudanar da tarukan Maulidi a faɗin duniya, Allah (swt) Ka fuwace masu abin yin hidimar, kuma Ka kare su daga dukkan sharri, Ka sa a yi lafiya a ƙare lafiya, Albarkar Annabi (saw)
👉 WANNAN RUBUTU👆 NÃ A MATSAYIN #MARABA_DA_MAULIDI_NE , DAGA
🇳🇬AS'HABULKAHFI JIBIA SOCIAL MEDIA TEAM, 06/10/2022,🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
To shi audu in banda abinsa ai a littafin sira ba addini ake koyarwa ba.abinda ya faru a lokacin baya suke bada labari kuma a cikin sirar da akwai gurinda sahabbai da matan annabi ko yarsa ko annabi ( s a w ) ya Tara mutane yace za'ayi murnar ranar haihuwata ne
ReplyDelete