SAHIHIN ABINDA YAFARU AKOTU 29/9/2022

 Shari'ar Sheikh Abduljabbar: Yadda ta wakana a zaman da aka gabatar na karshe kafin hukunci.



Aliyu Samba 


A zaman shari'ar da ya gabata a ranar Alhamis 29 ga watan Satumba 2022 a babbar kotun shari'ar Muslunci dake zaman ta a kofar kudu, lawyoyi 14 ne suka tsaya a gaban kotu a madadin masu gabatar da ƙara ƙarƙashin Jagorancin Barista Mamman Lawan Yusufari SAN, inda Barista Muhammad Lawan Abubakar ya gabatar da kan sa a matsayin mai riƙewa Lawyan Wanda ake ƙara Barista Dalhatu Shehu Usman. 


Mai Shari'a Alƙali Ibrahim Sarki Yola, ya fara da tambayar dukkan ɓangarori biyun akan jawabin su na karshe da suka gabatar wa kotu, ya nemi jin me suke buƙatar kotu tayi da wadannan jawabai na su. 


Daga ɓangaren lawya kai gabatar da ƙara, Barista Mamman Lawan Yusufari ya bsyyana cewa;


"Muna rokon wannan kotun da ta amshi wadannan bayanai na mu na karshe a matsayin hujjojin mu da muke rokon wannan kotu mai adalci tayi amfani da su wajen tabbatar da laifin da ake zargin wanda ake ƙara ya aikata, kuma a yi masa hukunci daidai da yadda Shari'a ta tanada.''


''Saidai bisa tsari, tunda sune suka fara kawo bayanai, to su ne ya kamata su fara neman a amshi bayanan su''. Inji Yusufari


Anan ne kotu ta nemi ji daga bakin lawyan Wanda ake ƙara kan me suke so kotu tayi da bayanan da suka gabatar wa kotu a rubuce. 


''Kun kawo jawaban ku na karshe, da jawabin martani bisa doka na karshe, ko me kuke so wannan kotu tayi dasu?" Inji Alkali Sarki Yola.


Barista Muhammad Lawan Abubakar ya bayar da martani da kamar haka;


"Yadda aka tsara, duk wannan bayansu da amsa, shi wanda ake ƙara ne zai yi da kansa''


Wanda ake ƙara Sheikh Abduljabbar Kabara bayan samun dama daga kotu , ya bayyana cewa yana so kotu ta nuna masa jawaban karshen da aka gabatar mata ko wanda ya rubuta ne yace a gabatar, inda mai Shari'a ya bada wannan damar takan mika masa takardar, ya duba sannan ya tabbatar itace wacca ya amince s gabatarwa kotu. 


Bayan ya duba, sai kotu ta sake tambayar da me yake bukata tayi dasu.


''Bukata ta shine, wannan kotu mai girma ta karbi wadannan jawabai dana gabatar mata dasu a matsayin hujja a wannan Shari'a, tayi amfani da wadannan jawabai nawa, ta kori ƙarar gwamnatin Jihar Kano da tayi a kaina, ta kuka umarce ta ta bani hakuri, wannan shine rokona'' inji Sheikh Abduljabbar Kabara


Barista Yusufari SAN ya sake nanata rokon su na a karbi bayanan su da kuma yi wa wanda ake ƙara hukunci bisa doka, ya kuma bijirar da uzuri tare da rokon kotu ta karbi bayanan su duk da cewa sun samu akasi na ƙetare wa'adin da kotu ta basu domin kawo bayanan masu da kwana 2. 


Bayan wannan roƙo nasu, kotu ta tuntuɓi wanda ake ƙara akan ko me zai ce akai, sai ya bayyana cewa, tunda sun ƙarfafi rokon su da nassi, to ya amince ba shi da suka akai. 


Kotu ta amince da wannan roƙo bayan ta bayyana cewa damar ta ce tayi hakan, kamar yadda nassin Ibn Asim ya kawo, kuma tsarin Shari'a ma ya yarda da baiwa Alƙali wannan damar. 


Abu na gaba da kotu ta tambaya shine yankan hanzarin wanda mai Shari'a ya bayyana cewa zaiyi shi ne bisa dogaro da nassin da ya zo cikin littafin Mawahidud Daleel. 


A nasu bangaren, Lawya mai gabatar da kara ya bijirar da nasu hanzarin kamar haka;


"Hanzarin mu shine, a wajen gabatar da karar nan, mun gabatar da sheda guda 4, 2 daga cikin su zamu iya ce musu su ganau ne da jiyau, sunji, sunga kalaman da shi wanda ake ƙara ya furta, wanda suka jawo wannan zargi a gaban kotun nan mai adalci. Kuma an kaɗa an raya wajen tambayoyi, an shiga an fita amma ba a taɓa shedar su ba, tana nan daram.''


''A cikin shedun nan huɗu akwai ɗan sanda mai bincike wanda yazo ya bada sheda akan binciken da yayi, tun daga lokacin da akai ƙara a wajen su, har zuwa lokacin da aka kawo wannan magana a wannan kotu. Shima shedar sa na da muhimmanci kwarai. Kuma a fahimtar mu tana nan daram ba a rushe ta ba'' inji Yusufari SAN 


Ya kara da cewa ''Shedar mu na karshe kwararre ne a ilimin hadisi, Farfesa ne a jami'ar Bayero, shedar sa taba nuna cewa kalaman da ake zargin wanda ake ƙara ya furta, babu su a cikin hadisin da aka ambata, ko kuma wasu hadisan ma daban wanda ya nuna cewa wanda ake ƙara ne ya kirkiri kalaman shi.''


A karshe ya rufe da cewa wanda ake ƙara a kokarin kare kansa, shedar kansa kawai ya iya gabatarwa kotu, kuma shedar tasa ta gaza saɓa shedun da suka kawo. Ya kuma ce sun dauke nauyin da doka ta ɗora musu na tabbatar da laifin wanda ake ƙara bisa doka, yayin da suke ganin wanda ake ƙara ya gaza dauke wannan nauyi akan sa. 


Kotu ta koma ga wanda ake ƙara inda shima ta tambaye shi ko yana da wani hanzari ko hujja kafin hukunci. 


Sheikh Abduljabbar Kabara ya ce bayanan da na hanzari takaitattu ne kamar haka;


''Game da shedu da ban kawo ba, nayi biyayya ne ga dokar evidence act wanda tace irin wannan sheda ba a tallafar sa da wata hujja ta baka, shedar ce take tabbatar da da kanta. Kuma a ranar 9/6/22 da ranar 23/6/22, na gabatar da wadannan a rubuce, wannan shiyasa ban nemi wata sheda ba, shine shaida ta''


''Sai maganar shedar ɗan sanda da ya gabatar wa kotu maganganun sa, na faɗi sheda ta akan abinda ya faru da mukayi da Kwamishinan yan sanda da shugaban hukumar DSS na jihar Kano. Tabbatar da hakan ba aiki na bane, aikin kotu ne'' inji Sheikh Abduljabbar


''Shi kusa shedar kwarewa, abinda ya bayyana ga kotu abu uku ne; na daya, Ha'incin sa gun sheda, domin littafin da ya zo da shi Sharhin Mukhtasar (Sharhul Kharshi ala Mukhtasar Khalil) don ya tabbatar da laifin da ake tuhuma ta dashi, sai ya zama nashi littafin karfafa ta yake ya kuma wanke Ni kan auren Nana Safiyya cewa, aure ne babu yardar ta, sai ya tsallake wannan wuri ya ha'inci kotu, sai gashi da na kawo wa kotu littafin, sai aka ganta. Ba Ni ne na ƙirƙira ba, bai dace ya tsallake wannan nassi wanda akansa ake Shari'a.''


''na biyu abinda ya bayyana ga kotu rashin ƙwarewar sa domin duk tambayoyin da nayi masa, bai iya amsa mun su ba. Don haka anan rashin ƙwarewar sa ta bayyana. Na uku, shi wannan sheda wanke Ni yayi daga tuhumar da gwamnatin Kano takeyi mun na cewa nayi wa Annabi ɓatanci, na nemi ya rabe mun tsakanin wannan sure da fyade, sai yace khususiyya ce. Wannan yana nuna cewa abinda suka faɗa a cajin su ba daidai bane cewa Ni ba kirkiri wadannan maganganu, da sun nufi gaskiya sai suyi kara ta akan na Kore khususiyya, amma basuyi haka ba.''


Sheikh Abduljabbar bayan kammala wannan jawabin sai ya nemi ya rufe zancen sa da abinda ya kira amana ce da alƙali ya dora masa yake son saukewa. 


''Aramakallahu ina da magana akan lauyan ka da wannan kotu ta bani domin ya cigaba da tsaya mun a gaban ta wato Barista Dalhatu Shehu. Yazo ya same ni a gidan yari da nake zaune yace mun Kai Alƙali ka same shi ka sanar dashi cewa ina da gaskiya ta, abinda yasa baka sallame ni ba shine kana jin nauyin ɗan uwana Ƙaribu Kabara ne da Grand-Khadi, kace masa idan har da zan baka wani abu da zaka sallame ni. Na ja masa akan aikata hakan, amma ya dage daga karshe nace nawa yake gani, yace zai faɗan daga baya ya sami ɗa na yace masa  Naira miliyan 2, kuma na bashi kuma ya tabbatar mun da cewa ya baka Miliyan daya da dubu dari biyun, ya bawa wani babba a garin nan da bai faɗan sunan sa ba dubu 300, shi kuma ya rike dubu 500.''


Mai Shari'a Ibrahim Sarki ya bada martanin sa kamar haka: ''Wallahi tallahi bansan da maganar ba, Akaramakallahu ka kwantar da hankalin ka wallahi wannan shari'ar da nake ba sani ake ba, wallahi zanyi hukunci ne da abunda ya bayyana gareni, ni dai rokon da nake kuyi mun Addu'a Allah ya bani ikon yin Adalci.''


Lawyoyin da ke zaune cikin kotun sun bayyana damuwar su akan hakan inda sukai ikirarin zasu dauki mataki akai bayan gudanar da bincike. Kuma zasu hukunta wanda aka samu da aikata laifin bayan binciken nasu. 


A karshe mai shari'a ya ambaci shedun Ihzari kamar haka; Barista Sani Garba da Barista Sani Yakubu. Ya kuma bayyana cewa kotu zatayi nazari game da duk abubuwan da suka faru a cikin wannan Shari'a, kuma zata yanke hukunci, zata kuma sanar da kowanne bangare ranar da zata yanke hukuncin. 


Aliyu Samba 

2/10/22

Comments