TABBAS BA'A TSAGAWA ANNABI SAW KIRJIBA DON FITAR MASA DA KAZANTA

 TABBAS ! BA A TSÃGÃ WA ANNABI (SAWW) KIRJĪ BA, DON A FITAR MASA DA  KAZANTA WACCE SHAIDAN KE ZUBA MASA A ZUCIYA, KUMA ANNABI SAM BA SHI DA SHAIDANI !!!



✍️ Saifullahi Murtala Jibia


" BA FALALA BA CE, TSÃGA ƘIRJIN ANNABI (SAW), DOMIN CIRE MASA HAZZIN SHAIƊAN

TAWAYA CE, KUMA ROSA ADDINI NE  !!!! "


TAMBĪHĪ !!!


Dole sai kã fãra yardã cewa Annabi (saww) ya na da shaidani, Kuma shadanin ya raina sa, inda yake ziyartarsa lokaci-lokaci yana bata masa zuciya. Sannan kuma sai ka yarda cewa  Allah yana turo mala'iku suna tsaga kirjin Annabi (saww) suna cire masa kazantar  da saidan ke zuba masa a zuciyar ; Idan Kuma Sam ba ka yarda cewa ba, Annabi (saww) yana da shaidani  Wanda ke bata masa zuciya ba, kenan dole ka yarda cewa sam ba a tsaga kirjinsa ba don cire masa wannan kazantar ba.


Kuma jama'ar  Annabi Muhammad (saww) mu dubi girman Ubangijin Annabi Muhammad da buwayarsa. Shi ne Wanda idan ya so abu ya zamo sai ya ce da shi, " zamo " Kuma sai abin ya kasantu. Kuna ganin , dã zuciyar Annabi (saw) za ta Sami matsala, idan Allah (swt) ya nufi ta zamo Mai lafiya, bã kawai cē da ita zai Yi ba " ki zamo Mai lafiya " Kuma ta zamo ba ?

To amma wai sai aka ce duk lokacin da zuciyar ta lalace sai mala'iku sun sauko sun Yi wa Ma'aiki (saww) oppression. Hakan ma wallahi tawaye buwayar girman kadarin Ubangiji ne !

____________


👉 Zan kawo maku inda suka rubuta cewa wai Annabi (saw) yana da shaiɗani wanda ke bata masa zuciya, sanadiyyar hakan Allah (swt) yake aiko Mala'iku su yi wa Ma'aiki operation , kuma bayan sun kammala, zuwa wani lokaci kuma sai Shaɗanin ya sake dawowa ya bata wa Ma'aiki (saww) zuciyar. Hakan ya sa, aka yi operation ɗin sau huɗu (4) ko sau (5) kamar yadda wasu cikin malamai, suka kattaba.


Wato Allah (swt) Ya bai wa shaiɗan wata dama, ta tarbar duk wani jariri lokacin da aka haife shi, tare da yi masa tsīkarī, wato ( cakulkulo ) a kuibi wanda hakan ke sa wa, jariri ke faɗowa yana yin kuruwa (kuka) sanadiyyar wannan tsīkarī. Kuma ta hanyar wannan tsīkarīn ne, shaiɗan ke samin damar yin bukka , a zuciyar mutane yana sa su, suna aikata ba daidai ba. Kowane Ɗan'adam, a duniya sai da sheɗan ya yi masa tsīkarī, har da Manzon Allah (saw) , Amma banda Sayyidatuna Maryam (AS) da Ɗanta Annabi Isah (AS). Kamar dai yadda ya zo a litattafi ma fi inganci, wato Sahihul Bukhari, a waɗannan gurare  :


👉 Kitabuttafsir ( Babun wa inni u'īzuha bika wa zurriyyatuha minasshaɗãnirrajīm ) Hadisi na (4548 )


👉 Kitãbu a hãdīsil  Anbiyã'i ( Babun  Ƙaulillahi Ta'ãlã wazkur fī kitãbi Maryam.....) Hadisi na ( 3437 ).


👉 Kitãbul bad'il khalƙ ( Babu sifati Iblīsa wa junudihi ) Hadisi na  ( 3286 )


«3286» حَدَّثَنَا أَبُو الْيَمَانِ أَخْبَرَنَا شُعَيْبٌ عَنْ أَبِي الزِّنَادِ عَنِ الأَعْرَجِ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((كُلُّ بَنِي آدَمَ يَطْعُنُ الشَّيْطَانُ فِي جَنْبَيْهِ بِإِصْبَعِهِ حِينَ يُولَدُ، غَيْرَ عِيسَى بْنِ مَرْيَمَ، ذَهَبَ يَطْعُنُ فَطَعَنَ فِي الْحِجَابِ)). 


Daga Abuhuraira (ra) ya ce  Annabi (saw) ya ce : " Dukkan Ɗan'adam , shaiɗan yana zungurin kuibinsa biyu da yatsunsa, lokacin da za a haife shi, wato ( cãkulkulo ) , banda Annabi Isah ɗan Maryam (AS) . A wata ruwayar , bayan shaiɗan ya yi wa jariri tsīkarī, a kuibi, sai ya faɗo yana mai yin kururuwa , wato ( kuka ) kamar yadda ya zo a Bukarin Hadisi na ( 4548 ).


Ashe idan muka cire Nana Maryam da Ɗanta Annabi Isah (AS), har Annabi (saw) shi ma, an yi masa wannan tsīkarīn a kuibi , kuma ya yi kuka. Kamar dai yadda waɗannan👆ruwayoyi suka yi nuni. Kenan Sayyidatuna Maryam, da Annabi Isah (AS) sun sami wata kariyar Ubangiji daga shaiɗan, wacce Manzon Allah (saw) bai samu ba  !!!


👉 CIKIN ALMAJIRAN MANZON ALLAH (SAW) 

Wato ( sahabbai ) akwai wani mai girman daraja da idan ya bi hanya shaiɗan ba ya iya bin hanyar har abada. Amma kuma , sun rubuta shi kan shi, Annabi (saw) ɗin , wai yana da shaiɗani 😭 !!!


Mu leƙa Sahihu Muslim (Kitãbussifatul ƙiyãmati wal Jannati wan Nãri )


باب تَحْرِيشِ الشَّيْطَانِ وَبَعْثِهِ سَرَايَاهُ لِفِتْنَةِ النَّاسِ وَأَنَّ مَعَ كُلِّ إِنْسَانٍ قَرِينًا: 


«7286» حَدَّثَنَا عُثْمَانُ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ وَإِسْحَاقُ بْنُ إِبْرَاهِيمَ قَالَ إِسْحَاقُ أَخْبَرَنَا وَقَالَ عُثْمَانُ حَدَّثَنَا جَرِيرٌ عَنْ مَنْصُورٍ عَنْ سَالِمِ بْنِ أَبِي الْجَعْدِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((مَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ إِلاَّ وَقَدْ وُكِّلَ بِهِ قَرِينُهُ مِنَ الْجِنِّ)). قَالُوا وَإِيَّاكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ قَالَ: ((وَإِيَّايَ إِلاَّ أَنَّ اللَّهَ أَعَانَنِي عَلَيْهِ فَأَسْلَمَ فَلاَ يَأْمُرُنِي إِلاَّ بِخَيْرٍ)). 


Daga Abdullahi Bn Mas'ud (ra) ya ce , Annabi (saw) ya ce : " Babu ɗaya daga cikin ku, face sai yana da ƙarini shaiɗan ". Sai Sahabbai suka ce : Har kai ya Rasulallah ? Sai Annabi (saw) ya ce " HAR NI INA DA SHAIƊAN, SAI DAI ALLAH YA TAIMAKE NI , YA MUSLINTA, BA YA UMURTATA SAI ALKHAIRI . Kenan , Shaiɗan yana Umartar Manzon Allah (saw) yin wani abu. Idan haka ne, to wannan👇 maganar ta roshe !!!


نَبِيُُّ بِغَيْرِ الْوَحْيِ لاَ يَتَصَرَّ فُواْ


Mu Matsa gaba, cikin Muslim ɗin, cikin wannan babin Hadisi na ( 7288 ) Inda Ma'aiki (saw) ke yi wa Uwarmuminai, nasiha, bisa wani abu da ta yi  inda yake cewa :


« فَقَالَ: ((مَا لَكِ يَا عَائِشَةُ أَغِرْتِ)). فَقُلْتُ وَمَا لِي لاَ يَغَارُ مِثْلِي عَلَى مِثْلِكَ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((أَقَدْ جَاءَكِ شَيْطَانُكِ)). قَالَتْ يَا رَسُولَ اللَّهِ أَوَمَعِيَ شَيْطَانٌ قَالَ: ((نَعَمْ)). قُلْتُ وَمَعَ كُلِّ إِنْسَانٍ قَالَ: ((نَعَمْ)). قُلْتُ وَمَعَكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ قَالَ: ((نَعَمْ وَلَكِنْ رَبِّي أَعَانَنِي عَلَيْهِ حَتَّى أَسْلَمَ)). 


(( Me ya same ki ya A'isha kishi kike ? )) Sai na ce, tayaya irina ba zai yi kishin irinka ba Ya Rasulallah ? Sai Annabi (saw) ya ce (( wato shaiɗaninki ne ya zo maki ko ? )) Sai ta ce, wato ina da shaiɗani ma kenan ko ?  Sai Ma'iki (saw) ya ce (( ƙwaraikuwa )) . Sai nace , Yanzu kenan kowane mutum yana da shaiɗa ni ? sai Annabi (saw) ya ce (( ƙwaraikuwa )) Sai na ce, Har kai kana da shaiɗani Ya Rasulallah ? Sai ya ce :

ƘWARAI KUWA, HAR NI INA DA SHAIƊAN, SAI DAI , ALLAH YA TAIMAKE NI YA MUSLINTA .


TAMBAYA :


Idan (wal'iyãzubillãh) shaiɗanin dake tare da shi Ma'aiki (saw) ya muslinta, me ya sa yake bata masa zuciya,wacce tun yarinta Allah (saw) yake aiko wa Ma'aiki (saw) da Mala'iku, suna kwantar da shi suna tsãga ƙirjin sa (saw) suna cire masa hazzin shaiɗan, amma shaiɗanin bai daina bata zuciyar ba, har zuwa lokacin da za yi ISRÃ'I DA MI'RÃJI sai da mala'iku suka sake kwantar da shi suka cire masa hazzin shaiɗanin a zuciyarsa , kuma suka zo da imani da hikima cikin tasa, bayan sun wanke , suka sake cika zuciyar da imani da hikima, sannan suka mayar da zuciyar suka ɗinke. ANAS BN MALIK ya ce suna ganin sayun ɗinki a ƙirjin Annabi (saw) kamar yadda ruwaya ta zo cikin Bukhari ???


GUDUN TSAWAITA RUBUTU, BARI IN KAWO MAKU 'YAN WASU GURARE DA HADISIN NAN NATSAGA ƘIRJIN MA'AIKI (SAW) YA ZO, TARE DA GAYYATO WASU AYOYI DAGA ALƘUR'ANI , WAƊANDA ZA SU BINDIGE WAƊANNAN RUWAYOYIN HAR LAHIRA !!!


RUWAYA TA KAN ABUDDARDÃ'I DAGA UTBATU BN ABDIN ASSULAMI.


👉 Sunan Dãrimī , Hadisi na 13, da na 14.

👉 Ahmad Bn Hambal Hadisi na 17648.

👉 Ɗabarī A Tãrīkh Juz'i na 1 shafi na 534 

👉 Uƙailī Cikin Kitãbuddu'afã'u , 2/359

👉 Hãkim A Mustadarak , 2/600 . Hãkim ya ce, Hadisun sahihun. Imamuzzahabi, shi ma yã rattaba hannu.


RUWAYA TA KAN ANAS BN MALIK 


👉 Sahihu Muslim Hadisi na 161,162

👉 Imamu Ahmad Bn Hambal , Hadisina 12221

👉 Ibn Sa'ad, Alkufi , Juz'i na 1 shafi na 150.

👉 Abdu Bn Humaid , Hadisi na  1380.

👉 Abu Awãna Juz'i na ɗaya shafi na 125.

👉 Abu Ya'ala Hadisi na 3374.

👉 Ibn Hibãna Hadisi na 6334.

👉 Abu Nu'aim, Cikin Dala'ilunnubuwwa na ɗaya shafi na 146.

👉 Hakanan, Bukhari ta wata hanyar 7517, ya yi ittifaƙi da muslim Hadisi na 162.

👉 Ibn Khuzaima , a kitabuttauhid  1/ 521. Ta kan Sharikh Bn Abdullahi Bn Abi Namr. Ita ma wannan wata ruwaya ce ta daban.

👉 Dãrimī Cikin Arraddu Alal Jahmiyya, shafi na 34. Har yau, Bukhari ya yi musharaka da shi cikin ruwaitar wannan lafazi, Hadisi na 349, 1636, 3342. Hakanan, Muslim ma ya yi ittifaki da shi, kan ruwaitar wannan lafazi Hadisi na 163.

👉 Nisã'i A Kubura Hadisi na 314.

👉 Abu Awãna Juz'i na 1 shafi na 333.

👉 Ibn Hibbãna Hadisi na 7406.

👉 Ãjurī  Cikin Kitabusshari'ah, shafi na  481.

👉 Bagawi  Cikin Kitabussunnah Hadisi na 3753 ta kan Zuhuri, daga Anas Ɗanmalik , ta kan Abuzarrin, ya ce Abuzarrin ya ce . (a'azahullah)


Bayan wannan ma, akwai wata ruwayar ta kan Ubayyu Bn Ka'ab, tana nan cikin Musnad 2222. Akwai watahanyar ma , ta kan Nana Halimatu Sa'adiyya (RA) cikin Ibn Hibbãn 6335. Hallau, akwai wata ruwayar ta kan Nana A'isha (RA) tana nan gurin Ɗayãlisi 1539. Wata hanyar kuma, ta kan Shaddadu Bn Auss, tana nan cikin Tãrīkh Bn Asãkir  Juz'i na 80 shafi na 380.


Na kawo maku waɗannan hanyoyin ne da yawa, saboda akwai haɗari a mas'alar wallahi billahi !


DOMIN BUGA MISALI,BARI MU ISU DA HADISAI GUDA  BIYU : (1) Wanda aka tsãga Ma'aiki (saw) a lokacin yãrintã (2) Da kuma wanda aka tsãga ƙirjinsa domin cire masa hazzin shaiɗan bayan, ya manyanta , lokacin da za a yi Isrã'i da Mi'irãji da shi (saw).


👉MU LEƘA  SAHIHU MUSLIM (( Kitãbul īmãn ))

Babul isrã'i bi Rasulillahi (saw) ilassamãwãti wa fardis salãti. Hadisi na ((431)) Imamu Ahmad Bn Hambal ma, ya ruwaici Hadisin . Bari mu yi amfani da lafazinsa


حَدَّثَنَا يَزِيدُ بْنُ هَارُونَ أَخْبَرَنَا حَمَّادٌ عَنْ ثَابِتٍ عَنْ أَنَسٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَلْعَبُ مَعَ الصِّبْيَانِ فَأَتَاهُ آتٍ فَأَخَذَهُ فَشَقَّ صَدْرَهُ فَاسْتَخْرَجَ مِنْهُ عَلَقَةً فَرَمَى بِهَا وَقَالَ هَذِهِ نَصِيبُ الشَّيْطَانِ مِنْكَ ثُمَّ غَسَلَهُ فِي طَشْتٍ مِنْ ذَهَبٍ مِنْ مَاءِ زَمْزَمَ ثُمَّ لَأَمَهُ فَأَقْبَلَ الصِّبْيَانُ إِلَى ظِئْرِهِ قُتِلَ مُحَمَّدٌ قُتِلَ مُحَمَّدٌ فَاسْتَقْبَلَتْ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَقَدْ انْتَقَعَ لَوْنُهُ قَالَ أَنَسٌ فَلَقَدْ كُنَّا نَرَى أَثَرَ الْمَخِيطِ فِي صَدْرِهِ. (مسند أحمد بن حنبل)


Daga Anass , lallai Annabi (saw) ya kasance ya na wasa da yara, sai mai zuwa, ya zo masa, sai ya kama Annabi (saw) ya tsãga ƙirjinsa,ya fitar da gudan jini, ya jefar ya ce, " wannan rabon shaiɗan ne da yake jikinka" . Sannan ya sa zuciyar ya dulmiya ta, cikin tãsar zinare da ruwan zamzam ya wanke ta, sannan ya shafe ta ya manne ( inda ya tsãga ɗin ) . Sai yara suka tafi da gudu, gurin Mariƙiyarsa (Nana Halimatus Sa'diyya) suna cewa " an kashe Muhammadu " sai ta taho gurin Annabi (saw) kalarsa ta ɗashe ( saboda tsananin wahalar operation ). 

To maruwaicin wannan Hadisin dai Anas ne, kuma a isnãdin akwai(Hammãdu Bn Salamata)


👉 SAI TSÃGA  ƘIRJIN MA'AIKI (SAW) LOKACIN ISRÃ'I DA MI'IRÃJI, BAYAN YA MANYANTA !!!


Muslim yã kawo a kitãbul īmãn, ( Babul isrã'i bi Rasulillahi (saw) ilãssamãwãti, wa fardis salãti) Hadisina 433, da 434, da 435, ruwaya daga Anas Bn Malik. 


Imamul Muhaddisina ma, ya kawo , a littafinsa ma fi inganci wato (Sahihul Bukhari) Hadisi na (349). Shi ma, ruwaya ta kan  Anas Bn Malik, bari mu yi amfani da lafazin Bukhari :


باب كَيْفَ فُرِضَتِ الصَّلاَةُ فِي الإِسْرَاءِ: 


«349» حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ بُكَيْرٍ قَالَ: حَدَّثَنَا اللَّيْثُ عَنْ يُونُسَ عَنِ ابْنِ شِهَابٍ عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ قَالَ: كَانَ أَبُو ذَرٍّ يُحَدِّثُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((فُرِجَ عَنْ سَقْفِ بَيْتِي وَأَنَا بِمَكَّةَ، فَنَزَلَ جِبْرِيلُ فَفَرَجَ صَدْرِي، ثُمَّ غَسَلَهُ بِمَاءِ زَمْزَمَ، ثُمَّ جَاءَ بِطَسْتٍ مِنْ ذَهَبٍ مُمْتَلِئٍ حِكْمَةً وَإِيمَانًا، فَأَفْرَغَهُ فِي صَدْرِي ثُمَّ أَطْبَقَهُ، ثُمَّ أَخَذَ بِيَدِي فَعَرَجَ بِي إِلَى السَّمَاءِ الدُّنْيَا،............


Anas Bn Malik ya ce , Abu Zarrin ya kasance yana bada labari cewa, Annabi (saw) ya ce (( an buɗe, ko yaye, rufin gidã nã, alhãli, ina a Makka, sai  Jibrilu (as) ya sauko, ya tsãga ƙirji na, sai ya fito da zuciyata, sai ya wanke ta da ruwan zam-zam, sannan sai ya zo da wata tãsã ta zinare, wacce aka cika ta da ( hikima da īmãni)

Sai aka kwarara shi cikin zuciyata, sannan aka ɗinke wato ( aka rufe inda aka tsãga ) sai aka riƙe hannu na, aka yi sama da ni, wato ( Mi'irãji )


'YAN UWA MUSULMI, MU KALLI ALƘUR'ÃNI, MU AJE ƘUNGIYANCI, KO BANGARANCI, MU DUBI ALLAH (SAW) ABIN DA YAKE CEWA 👂👂👂!!!


Mu leƙa Suratul Hijri, daga ãya, ta (28) inda Allah (swt) ke bai wa Mala'iku labari cewa, zai Halicci Annabi Adamu (as), har zuwa lokacin da ya hallicce shi, Ya umarce su, da su yi masa sujjada, kuma suka yi, amma iblis (shaiɗan ) ya ƙi yin sujjadar, zuwa inda Allah (swt) Ya la'ance shi, da alfarmar da ya roƙa gurin Ubangiji, ta jinkirta rayuwarsa zuwa tashin ƙiyama, zuwa inda yake  cewa :


قالَ رَبِّ بِما أَغوَيتَني لَأُزَيِّنَنَّ لَهُم فِي الأَرضِ وَلَأُغوِيَنَّهُم أَجمَعينَ


Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa sai nã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa sai nã ɓatar da su gabã ɗaya."


إِلّا عِبادَكَ مِنهُمُ المُخلَصينَ


" Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."


👉 MAHANGAR MU ( 'YAN ASHABULKAHFI ) !!!


Ya za a yi, mu yarda Annabi (saw) yana cikin bayin nan na Allah Mukhlasai, waɗanda suka fi ƙarfin shaiɗan wato ( ba ya iya yin tãsīrī a kan su ) kuma, ya za a yi mu yarda Annabi (saw) yana da shaiɗani, wanda ke yi masa umarni, kuma yake shiga zuciyarsa, bayan an wanke ta, an cika ta da imani, da hikima, kuma ya rinƙa shiga yana bata zuciyar wanda ba a daina tsaga ƙirjinsa ba har zuwa ranar da aka yi isrã'ida mi'irãji da shi ? Bayan kuma Allah (swt) ya ce wa Ibliss ( shaiɗan ) :


إِنَّ عِبادي لَيسَ لَكَ عَلَيهِم سُلطانٌ إِلّا مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الغاوينَ


"Lalle ne bãyĩ Na, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."


Idan Sayyid na Umar (r.a) za mu yarda cewa in ya biyo hanya shaiɗan ba ya bin hanyar , to me ya sa muka yarda Annabi (saw) wai yana da shaiɗani, kuma yana shiga jikinsa ya bata zuciyarsa, har sai Mala'iku sun zo sun yi masa operation ? Kenan ba ya cikin bayin ubangijin can da ya ce wa shaiɗan, "bã ka da īko a kan su" da kuma maganar shi kan shi shaiɗanin cewa, " Zai batar da kowa gababa-ɗaya, fãcē  Bayinka daga gare su waɗanda ka tsarkake " To wai  tasakanin sayyid na Umar (ra) da Annabi (saw) waye wanda shaiɗan ba ya tãsīrī a kan sa ???


Mu ƙara leƙawa cikin Suratul isrã'i , ãya ta 64 zuwa ta 65, Inda Allah (swt) yake ce wa shaiɗan


وَاستَفزِز مَنِ استَطَعتَ مِنهُم بِصَوتِكَ وَأَجلِب عَلَيهِم بِخَيلِكَ وَرَجِلِكَ وَشارِكهُم فِي الأَموالِ وَالأَولادِ وَعِدهُم ۚ وَما يَعِدُهُمُ الشَّيطانُ إِلّا غُرورًا


"Kuma ka rikitar da wanda ka sãmi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma ka yi hari a kansu da dawãkinka da dãkãrunka kuma ka yi tãrẽwa da su a cikin dũkiyõyi da ɗiyã, kumaka yi musu wa'adi. Alhãli kuwa Shaiɗan bã ya yi musu wa'adin kõme fãce da ruɗi."


إِنَّ عِبادي لَيسَ لَكَ عَلَيهِم سُلطانٌ ۚ وَكَفىٰ بِرَبِّكَ وَكيلًا


"Lalle ne bãyiNa, bã ka da wani ƙarfi a kansu. Kuma Ubangijinka Ya isa Ya zama wakĩli."


👂 TO MU MUN YARDA ANNABI (SAW) YANA CIKIN BAYIN ALLAH ( MUKHLASAI ) WAƊANDA SHAIƊAN BA YA IYA YIN TASIRI , AKAN SU. HAKANAN, DAGA YAU MUN FITA DAGA MASU CEWA , ANNABI (SAW) YANA DA SHAIƊANI, KUMA YANA SHIGA JIKINSA YA BATA MASA ZUCIYA, AMMA IDAN SAYYID NA UMAR  YA BIYO HANYA SHAIƊAN BA YA BI, SABODA  GIRMAN DARAJARSA !!! WANDA YA SHIRYA FAHIMTAR DA MU, AKAN WANNAN MAS'ALA, ƘOFA NA BUƊE. WASSALAMU ALAIKUM.


👉 Ina tare da Ameerilwa'izeena Sarkin  Gidan Malam Kabara (H) %%%. Kuma wannan rubutu sharar fage ne, na tauna mas'alar Isrã'i da Mi'irãji, da fatan Allah (swt) Ya ba mu sadakar rai, da cikakken iko, albarkar Manzon Allah 🤲.


#HAPPY_MAULUD_TO_ALL_MUSLIM_UMMAH


🇳🇬AS'HABULKAHFI JIBIA, SOCIAL MEDIA TEAM , 09/10/2022, 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬.

Comments