Yau shekara biyu da gabatar da mukabala a jihar kano tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da wasu Malamai 4 a Jihar Kano.


 Yau shekara biyu da gabatar da mukabala a jihar kano tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da wasu Malamai 4 a Jihar Kano. 


A rana irin ta yau a shekarar 2021 aka yi mukabala da Malam Abduljabbar Kabara da sashen Malamai a Jihar Kano, biyo bayan zarge-zarge da zauren Malaman jihar Kano sukayi akan cewa Malamin na furta wasu kalmomi da nasabta su ga littafan Bukhari da Muslim, wanda suke zargin babu su, shi ya kirkire su.


Zaman ya biyo bayan zargin da Zauren Malaman Kano yayi wa gwamnatin Kano da cewa tana “Jan Kafa” akan daukar mataki kan tuhumar su ga Malam Abduljabbar da cewa kalaman sa suna cin zarafin Manzon Allah SAW da sahabbansa. 


Saidai a nashi bangaren, Sheikh Abduljabbar ya sha musanta wannan zargi, inda ya ke bayyana cewa yana korewa Annabi SAW miyagun dabiu da aka jingina masa a sashen littafan hadisai, wanda a cewar sa sun jawo wasu da dama sun fita daga musulunci. Yayi hakan ne dan wanke manzon Allah daga wannan miyagun abubuwan da aka nasabta masa, amma sai aka dawo da abubuwan kan sa aka zarge shi da furta su. 


A farko gwamnatin ta Kano ta sanya ranar muhawarar kafin daga baya a ɗage ranar, kuma a an samu bambamace-bambamce kan yadda za a gudanar da muhawarar daga tsarin da aka yi da farko.


Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana sunayen malaman da za su fafata da Sheikh Abduljbbar Kabara ba a wannan muhawara.


Kwamishinan Al’amuran Addinai na jihar a wancan lokacin Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ya ce sai a wajen muhawarar ne za a fadi sunayen malaman da za su yi.


Haka kuma a baya, ita ma haɗakar malaman ta Kano ta ce ta shaida wa gwamnati malaman da za su wakilce ta, amma ta ce ba za ta bayyana ba sai a zauren muhawarar.


Sai dai sanannen abu ne cewa malamai daga ɓangarorin Ahlussnnah da Izala da Tijjaniya da Kadiriyya da suke ƙalubalantar Sheikh Abduljabbar sun jima da jikakkiya tsakanin su. 


Wakilin Malaman Ahlussunnah shi ne Sheikh Abdulwahhab Abdullah, sai Shehi-Shehi da ke wakilatar ɓangaren Tijjaniyya, sannan sai Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara da ke wakiltar ɓangaren Ƙadiriyya, wanda yaya ne ga Sheikh Abduljabbar, yayin da Sheikh Abdullahi Pakistan yake wakiltar ɓangaren Izala.


Sheikh Abduljabbar ya ce dukkan kalaman da ake cewa ya yi Malaman da yake Mukabala da su sun gaza musantawa ko karyata Hadisan da ke cewar Buhkari ya rawaito su da suke taba janabin Annabi (SAWW).


Yan jarida ƙalilan ne suka shiga ɗakin muƙabalar ciki, yayin da Jami'an tsaro suka yi wa ofishin Hukumar Shari'a ta Kano tsinke, wurin da aka gudanar da muhawarar.


Kafin tsunduma cikin muhawarar gadangadan, alƙalin muƙabala Farfesa Salisu Shehu - shugaban cibiyar Musulunci da tattaunawa tsakanin addinai ta Jami'ar Bayero - ya bayyana sharuɗa kamar haka


1, Za a gabatar da muƙabalar da Hausa


2, Za a bai wa dukkan ɓangarorin dama ba tare da fifita wani ba. Za a bai wa kowane bangare minti 10


3, Dukkan maudu'i su na da minti 30 tare da bayar da min 5 na ɗauraya


4, Za a bayar da dama na minti 5 na nuna hoto ko bidiyo ko sauti


5, Ba a yarda masu muƙabala su katse ɗaya daga cikinsu ba yayin da yake magana har sai lokacin da aka bayar ya cika


6, Ana buƙatar hujjoji ingantattu kuma karɓaɓbu a Musulunci


7, Dole ne dukkan masu muƙabalar su kiyaye cakuɗa hadisai da ayoyi, a gabatar da su cikin ladabi


8, Dole ne a girmama juna tare da yin amfani da lafazi na mutuntawa


9, Babu zuga babu kirari, ko wani abu da zai nuna ɓangaranci


Malaman da suka fafata a mubaƙalar


Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fuskanci malamai huɗu ne yayin muƙabalar domin kare kansa daga zargin kalaman ɓatanci ga Annabi (SAWW)


1, Malam Mas'ud Mas'ud Hotoro daga ɓangaren ɗariƙar Ƙadiriyya kuma tsohon ɗalibin Sheikh Abduljabbar wanda a baya ake masa lakabi da “Magayakin Kogo”. 


2, Malam Abubakar Mai Madatai daga ɓangaren Tijjaniyya


3, Malam Kabir Bashir Kofar Wambai daga ɓangaren ƙungiyar Izala


4, Dr. Muhammad Rabiu Umar Rijiyar Lemo daga ɓangaren Salafiyya


Alkalin da Gwamnatin Jihar Kano dake Najeriya ta nada domin jagorancin mukabala tsakanin Malam Abduljabbar Nasir Kabara da tawagar malaman Jihar Farfesa Salihu Shehu yace Malam Kabara ya gaza bada amsar tambayoyin da malamai su kai masa a zaman da akayi.


Yayin da yake jawabi bayan kammala mukabalar Farfesa Shehu yace duk wanda ya halarci zaman da kuma duk wanda zai saurari bayanan da maluma suka yi a wajen mukabalar zai fahimci cewar Malam Abduljabbar bai iya bada amsa akan wadannan tambayoyi ba.


Farfesan yace maganganun da Malam Abduljabbar keyi akan hadisai ba daidai bane ganin yadda yake caccakida su wadanda ba a doron ilimin hadisi suke ba.


Farfesan ya mika godiyar sa ga daukacin malaman da suka halarci zaman da akayi saboda gudumawar da suka bayar na ilimi da kuma yadda taron ya gudana cikin kwanciyar hankali.


Sai dai Shiekh Abduljabbar Nasiru Kabara yace ba'a bashi isashen lokaci domin gabatar da hujjojin sa ba, saboda haka yana bukatar a sake shirya wani zama nan gaba. Ya kuma zargi cewa Alkalin Mukabalar na daga wadanda suke da matsala da shi, kasancewar ya fito ne daga bangaren Izala, wanda sune gaba-gaba wajen yi masa ca da ikirarin ya taba mutuncin Annabi SAW. 


Shehin malami Abduljabbar Nasiru Kabara wanda shi ne mai kare kansa daga malamai huɗu da ke zargin da yin kalaman ɓatanci ga Annabi (SAWW) ya ce ba zai tuba ba a wurin wannan muƙabala "saboda rashin ƙwararan hujjoji" da suka tabbatar da cewa ya aikata laifi. 


Ya faɗi hakan ne a daidai lokacin da Mallam Abubakar Madatai ya ce duk wanda ya ci mutuncin Annabi hukuncinsa kisa ne sannan ya nemi Abduljabbar da ya fito fili ya tuba.


Sai malamin ya ce: "Ba zan tuba a wurin wannan mukabala ba har sai an ba ni cikakkiyar hujja. In dai aka ba ni hujjojin da suka fi nawa zan tuba, amma yanzu mutum ba zai tuba ba bayan ya na kan gaskiya. Ba'a biyo turbar da zan tuba ba."


Sheikh Abduljabbar ya jaddada cewa shi ma Annabi yake karewa daga irin ƙagen da ake yi masa a wasu hadisai amma babu isasshen lokaci na tabbatar da hakan "saboda minti 10 sun yi kaɗan".


"Abin da nake yi ina yin su ne don rarrabe hadisan da ake yi wa Annabi ƙarya. Da don Annabi ake yi da an bayar da isasshen lokaci don a yi muƙabalar. Littafan da na zo da su, minti goma sun yi kaɗan a kwance su."


Farfesa Salisu Shehu wanda shi ne alƙalin muƙabalar, ya zargi Sheikh Abduljabbar da ƙin amsa wasu tambayoyi da kuma ƙin buɗe littafi don bayyana in da ya ciro wasu abubuwan ya na mai fakewa da rashin isasshen lokaci.


"A kowace gaɓa, malam Abduljabbar ba ya tsayawa a kan tambayoyin da aka gabatar masa saboda na farko yana cewa babu isasshen lokaci," a cewarsa.


"Na biyu ya na cewa a tsaya a kan maudu'i ɗaya a yi magana, amma shi ne ba ya tsayawa a kan maudu'i guda ɗayan, sai ya yi ta yawo ya na haɗo mas'aloli daban-daban maimakon ya yi bayani game da tambayoyin da aka yi masa.


"Idan ya yi da'awar cewa maganar da ya yi ta kaza a littafi kaza ya gani; in an ce ya buɗe littafi ya karanto wa mutane sai ya bayar da uzurin cewa babu lokacin da zai karanto wa mutane."


Shehin malami Abduljabbar ya zargi alƙalin da ke kula da muhawarar, Farfesa Salisu Shehu, da cewa yana mara wa abokan muhawarar tasa baya.


"Kamata ya yi a ce a haɗa ni da wanda na sani amma sai ga shi na ga alƙalin muƙabalar ya goyi bayan malaman da muke mukabala da su," in ji shi.


Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da Mallam Kabir Bashir ya zarge shi cewa ya ce: ya tura kawaliya don ta duba masa wata budurwa, zargin da Abduljabbar ya musanta nan take.


Jim kaɗan bayan kammala muhawarar ce kuma Sheikh Abduljabbar ya ce bai gamsu da muƙabalar ba amma ya ce duk sanda aka sake nemansa zai zo.


"Fisabilillahi da gyara, wannan ba tsarin yadda ake muƙabala ba ne, ban gamsu ba," in ji shi.


Shehin malamin ya ce ba a bayyana masa tsarin yadda muƙabalar za ta kasance ba har sai da ya shiga ɗakin tattaunawar.


"Matsalar ba su ba ni tsarin yin (muƙabalar) ba, ban san yaya za a gudanar ba balle na ba su shawarwari," a cewarsa.


"Fatanmu dai a samu nasara a zaman, a samu mafita ga wannan addini namu. Ba ƙure ne buƙatarmu ba; ina gaskiya take domin mu samar wa addininmu mafita."

Comments