Yanda Aka bayyana Rashin Babban.Darakta Aminu s Bono



 Rashin Malam Aminu S Bono babban rashi ne a tafiyar Ashabul Kahfi Warraqem, kai tamkar rasa babban muƙaddami ne a tafiyar. Shi yasa har yanzu kahfawa suke juyayi da alhini na rashinsa. 


Duk da Mal Aminu ɗan kahfi ne tun da jimawa, amma da yawa ba su san haka ba sai da Ashabul Kahfi ta shiga rintsin da bata taɓa shiga ba, a lokacin da hatta wasu ɗaliban boye kansu suke, suna tsoron a kirasu yan kogo amma shi Malam Aminu a lokacin ya nunawa Duniya shi ɗan Kogo ne. 


Ga shi ba Mutum ne gama garin Mutane ba balle ace ai ba wani abu bane nunawa duniya kai ɗan kogo ne, a'a Mutum ne shararre a cikin al'umma, Al'ummar da take da ra'ayoyi daban daban tare da Mutane kala kala.


Abun da ya sa nace rasa shi kamar rasa muƙaddami ne a Kahfi, shi muƙaddami ba kowa bane face wanda yake jagorantar wani yanki yake shiryar da su izuwa tafarkin da yake kai, to a wannan ma'anar za mu ga Lalle Malam Aminu yana cikin manya manyan muƙaddamai. 


Za ka sha mamakin masu bibiyarsa, da dubban mutanen da suka gane sharrin da akaiwa Amerul Waizina idan ka bibiyi shafukansa, Musamman a Tiktok. Ga shi wani abun jin daɗi yadda yake ba da amsa ga duk wautar mai wauta yasan ta inda zai tare shi. 


Lalle mun yi rashi 

Allah yajikansa yai masa Rahama.

Comments